Howe na shirin tattaunawa da United, ƙungiyoyin Firimiya uku na zawarcin Karl

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon mai horar da yan wasan Newcastle Eddie Howe, da yanzu ba shi da aiki, zai iya kasancewa a shirye wajen tattaunawa da Manchester United idan old Trafford ɗin suka raba gari da Michael Carrick. (Sky Sports)

Manchester United na harin ɗan wasan Everton Jarrad Branthwaite, a yunkurinsu na siyen mayan masu tsaron bayan ƙugiyar. (Football Insider)

Tsohon mai horar da ƴan wasan Watford, da Burnley, da Everton da Nottingham Forest Sean Dyche na kan gaba a cikin waɗan da Crystal Palace ke son karɓar ƙungiyar idan har suka sallami mai horar da Crystal Palace. (Telegraph - subscription required)

Tsohon mai horar da ƴan wasan Brentford Thomas Frank da tsohon mai horar da ƴan wasan Wolves Vitor Pereira na daga cikin waɗan da ke gogayya da tsohon mai horar da ƴan wasan Ferencvaros Robbie Keane da su ma ke son komawa ƙungiyar. (Talksport)

Ɗan wasan Tottenham Lucas Bergvall, na cikin ƴan wasan da Napoli da Barcelona, ke hari. (Tuttomercato via Teamtalk)

Manchester United ba za ta soke rajistar makarantar ɗan wasanta JJ Gabeiel ba, wanda hakan ke nufin ɗan wasan ba zai iya barin ƙungiyar ba har sai nan da watan Janairu, yayin da Barcelona da Paris-St-Germain ke son ganin sun cimma yarjejeniyar ɗaukar sa da old Trafford. (Football Insider)

Arsenal, da Liverpool da Manchester United na sa ido kan ɗan wasan Bayern Munich Lennart Karl. (Teamtalk)

Ɗan wasan Brazil Dodo na shirin barin Fiorentina idan kwantaraginsa ta ƙare a ƙarshen kaka, yayin da AC Milan, da Juventus and Barcelona. (Football Italia)

Brighton da RB Leipzig na daga cikin ƙungiyoyin da ke son ɗaukar ɗan wasan Juventus Adin Licina, da ke matsayin dan wasan aro a Cremonese. (Gianluca di Marzo)