Yadda wasu suka yi imani da sihiri da addu'o'i don neman nasara a Gasar Kofin Duniya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Dalia Walker na ganin akwai wani abu na al'ajabi game da nasarar da kasarta ta samu a gasar cin kofin duniya ta FIFA da aka yi a Qatar a 2022.

"Ina ganin sihiri ne ya taimaka wa Argentina ta yi nasara," in ji matar mai shekara 41 daga Buenos Aires.

Dalia na cikin tarin mutanen da suke kiran kansu mayu, suna yin tsafi da gudanar da al'adu don taimaka wa Lionel Messi da sauran ƴan wasan Argentina.

Matan sun ba kansu suna "La Brujineta", an haɗa da kalmar "bruja" wadda ke nufin mayu, da kuma "La Scaloneta", lakabin da ake kiran tawagar ƙasarsu ta Argentina a ƙarƙashin koci, Lionel Scaloni wanda ke jan ragama.

La Brujineta suna amfani da sihirin zamani da ya haɗa da ƙyandir da yin addu'o'i da amfani da layu wajen gudanar da sihiri, a cewar Dalia.

Suna tuntuɓar juna ta hanyar kafafen sada zumunta kamar WhatsApp da sauran su, suna tantance waɗanne wasa ne mai haɗari da tawagarsu ke buƙatar kulawa mafi yawa.

Wasu daga cikin shahararrun sihirin da suke yi, suna tsarawa ne, domin "dakushe" ƙarfin wasu fitattun ƴan wasan abokan hamayya, wani abu da Dalia ta ce ba ta yarda da shi ba.

A maimakon haka, ta fi son abin da ta ɗauka a matsayin na al'ada mai ƙyau, kamar kunna kyandir da zai kara ''musu kwazo'' a lokacin da suke taka leda..

Lokacin da Argentina ta yi nasarar lashe kofin duniya a Qatar a 2022, tawagar masu sihiri ta La Brujineta na ganin cewar kokarinsu ne ya sa kasar ta yi bajinta.

"A gani na, shi ne Kofin Duniya da mayu suka yi aiki tukuru a kai," in ji Dalia.

Saboda haka ta sake yin shirin gudanar da irin waɗannan sihirce-sihirce ta hanyar kunna ƙyandir masu launin shuɗi da fari wato kalolin tawagar ƙasarta, Argentina a wurin ibadarta.

"A Argentina, idan har aka yi sihiri ya kuma ci, (a bisa imanin camfi, idan za ka kara a karo na biyu) dole ne ka maimaita shi daidai da yadda aka yi a baya."

Magoya bayan masu sihiri na La Scaloneta ba su kaɗai ba ne daga wata ƙasa da ke neman taimakon ko suka shiga yin sihiri. Wasu masu tsafi daga Peru sun gudanar da wani aiki na al'ada a babban birninsu Lima, domin taimaka wa tawagarsu ta samu tikitin shiga gasar ta 2022. Amma sai suka sha kashi da ci 5-4 a bugun fenariti a hannun Australia. A duk faɗin nahiyar Afirka kuwa, al'amuran rauhanai suna da nasaba sosai da rayuwar yau da kullum, har ma idan aka zo ga harkar ƙwallon ƙafa.

Al'adu da layu

Ga wasu, hakan na nufin imani da tasirin abubun gargajiya da kuma masu maganin gargajiya. A shekara ta 2002 hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (Caf) ta haramta abin da ake kira "masu ba da shawara ga tawaga" – wata kalma ce da ake kiran masu aiki da rauhanai a gargajiyance – inda aka hana su taka rawa a duk wata tawagar da ke fafatawa a Gasar Kofin Nahiyar Afirka.

Har yanzu akwai magoya baya masu tsananin goyon baya da ke amfani da abubuwan gargajiya, yayin da suke rawa da tafi da murna a filin wasa, sanye da layu da ƙuƙumi, har ma a wasu lokuta suna fitar da wuta da hayaki daga bakinsu, in ji ɗan jaridar ƙwallon ƙafa Maher Mezahi.

Kuma a watan Nuwamban bara lokacin da aka fitar da Najeriya daga wasan neman cike gurbin shiga gasar cin Kofin Duniya, kocinsu, Éric Chelle ya zargi tawagar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (DRC) da amfani da tsafi domin samun nasara. Tsohon kocin DRC, Florent Ibenge ya yi watsi da zargin yana mai cewa "shirme ne kawai."

Yin amfani da tsafi karara na iya zama dalilin da ya sa wasu mutane da dama ke ƙin zuwa kallon wasa a fili cewa suna faɗawa irin waɗannan al'adun gargajiya.

"Ƙwallon ƙafa ya fi karkata zuwa Turai," in ji Mezahi. A can ne "Manyan ƙungiyoyi suke, kuma manyan ƴan wasa suna buga wasa a can, don haka duk abin da ba na Turai ba ina ganin ana iya kallon sa ko a ɗauke shi da shakku."

Amma yana ganin cewar wannan ba "wani abu ba ne da ya kamata ƴan Afirka su ce abin kunya ne. Wani abu ne da muke aikatawa a rayuwarmu ta yau da kullum."

Ya kara da cewar yarda da kuma amfani da irin waɗannan sihirce-sihirce, koma baya ne ga kasashe masu tasowa.

Amma akwai waɗanda za su yi tantama kan banbanci tsakanin yin sihiri kan yadda abokiyar hamayya za ta yi nasara a wasa ko yin tasiri a karawar da kuma masu addu'ar neman samun nasara daga Allah.

'Allah ne mai komai'

Magoya bayan ƙwallon ƙafa ta tawagogi a Afirka sun buɗe ido wajen rungumar addinai masu nasaba da Annabi Ibrahim, kamar Kiristanci da Musulunci, in ji Mezahi.

A ɓangaren magoya bayan Algeria sun yi kaurin suna a rera wata waka da suke roƙon Allah ya kare ya kuma taimaki tawagarsu. Kuma "idan ka saurari ƙasashen Afirka ta Yamma musamman, Ghana ko Najeriya, suna kunna waƙe-waken addini a abin amsa kuwwa a kowane wasa," in ji Mezahi.

Ministan Wasanni na Ghana Kofi Iddie Adams ya roƙi masu ibada a wani taron coci da aka yi kwanan nan da su yi addu'a, domin nasarar tawagar ƙasar, wadda aka fi sani da suna The Black Stars.

Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana (GFA) ma ta nemi addu'a daga manyan ƙungiyoyin addini guda biyu mafi girma a ƙasar, Kiristoci da Musulmi. An gudanar da wani taron ibadar Kirista na ƙasa a Accra, inda aka yi addu'a domin tawagar Black Stars ta samu nasara – gabanin abin da hukumar GFA ta kira "babban dandali na ƙwallon ƙafa."

Haka kuma Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana (GFA), tare da babban Limamin ƙasar, sun gudanar da addu'o'in Musulunci gabanin gasar, inda malamin ya "roƙi samun nasara ga tawagar", kamar yadda GFA ta bayyana a cikin wata sanarwa.

"Mun yi imani cewa Allah ne mai yin komai a duk abin da muke yi," in ji Nathan Laryea, ɗan jarida da ke zaune a Accra. Ya bayyana yadda imani yake da muhimmanci a al'adun Ghana.

Akwai wata ƙasa, wadda imani da kuma ƙwallon ƙafa suke da alaƙa sosai kamar yadda yake a nahiyar Afirka, in ji Maher Mezahi.

"Daya daga cikin abubuwan da na gani da ya shafi addini tun ina ƙaramin yaro shi ne lokacin da Brazil ta lashe Kofin Duniya a 2002."

"Wani ɗan wasa mai suna Kaka ya cire rigarsa, kuma yana sanye da wata riga a ciki da aka rubuta, 'Ni jinin Yesu ne'. Sai na ce, 'Oh, wannan abin sha'awa ne.' Ban taɓa tunanin [wani] zai sanya irin wannan riga a lokacin wasa ba a baya."

Wannan, a cewar Mezahi, "wani saƙo ne ga duniya."

Haka ma aka yi wa tawagar Brazil bankwana zuwa gasar ta wannan shekara. Kafin jirginsu ya tashi, an "yi masa feshin ruwa" ta hanyar amfani da motocin kashe gobara ɗaya daga hagu da wata a dama, sannan ya rastsa ta tsakani.

A al'adar harkar jiragen sama, irin wannan alama yawanci ana yin ta ne ranar da jirgi zai fara aiki, ko kuma idan matukinsa zai yi ritaya, ko kuma za a ajiye jirgin sakamakon daɗewa da ya yi yana tafiye-tafiye a sararin samaniya.

A wannan karo, magoya bayan Brazil suna fatan cewa hakan zai taimaka musu wajen samun damar lashe kofin duniya na 2026 su haɗa da biyar da suke da shi ya zama shida mafi yawa da kasa ta lashe a tarihin gasar da aka fara shekarar 1930.