Mene ne ke ruruta wutar rikici a jam'iyyar APC a Kano?

Asalin hoton, Social Media/Multiple
Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya, na neman faɗawa cikin cikin gida a Jihar Kano da ke Arewacin ƙasar, ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar ke fatan samun ƙuri'u maso yawa a zaɓen da ke tafe.
Takun saƙa da gugar zana da kuma shaguɓe na neman dabaibaye siyasar jihar, ko da yake rikici ne da ake yi a cikin duhu.
Rikici ne da yake neman girmama tsakamin mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin da Ɗan Majalisar Tarayya na yankin Bichi, Abubakar Kabir Abba Bichi.
Rahotanni sun ambato cewa, duk da cewa akwai wata jiƙaƙƙiya a ƙasa tsakanin jiga-jigan siyasar biyu, amma lamarin ya ƙara tsami ne bayan da mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo ya yi wasu kalamai masu kama da jirwaye da kamar wanka a wani taro da ya gudana a Bichi.
Garo ya bayyana a wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda yake cewa duk wanda ya taɓa Abba Bichi sai ya ji su "ba a Bichi ba ko a Kabo ne".
Wannan zance ya haifar da maida martani daga ɓangaren magoya bayan Sanata Barau Jibrin.
A wani bidiyo na daban kuma an ga shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi na mayar da martani cikin kan masu ingiza rikicin da yake tsakaninsa da Sanatan.
"An yi taron taimaka wa mutane a Bichi, kuma masu zuga Abba cewa ya so wani ko ya ƙi wani, to ku sani ya fi ku hankali, ba zai bari a cewa ko kasila ya faɗi ba a Kano".
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce Abba yanzu shugaba ne a ƙasa ba a iya Kano ba, har wasu jihohin yana zuwa a matsayin wakilin APC.
Ta yaya zai so a ce APC ta samu mishkila a Kano ba.
"Da wane ido zai kalli Asiwaju ko Nentawel ko Shugaban Majalisar Dattijai ko kuma wakilai, duk wanda suka zuga shi su sani mun sansu, ta Allah ba ta su ba", in ji Injiniya Bichi.
Wannan ya fito da guna-gunin da ake yi a bayan fage tsakanin magoya bayan 'yan siyasar biyu.
BBC ta samu tattaunawa da ɗaya daga cikin masu goyon bayan Sanata Barau, Honarabil Fa'izu Alfindiki wanda ya ce wasu ba su son matsayin da Allah ya bai wa Barau shi yasa suke neman daƙushe shi.
"Abin da ya fi ƙamari shi ne yadda suka so a hana shi ya ci takarar a zo a yi wa Sanata Barau anti-fati saboda na sama da suke ganin idan ya ƙara ci zai hana su rawar gaban hantsi", in ji Faizu Alfindiƙi.
An tambaye shi cewa kamar babu wata rigima tsakanin shugabannin tun da ba a taɓa jin ɗayansu na suƙar ɗaya ba.
Dan siyasar sai ya ce "Ga hujja zan kawo maka, an yi taro a Bichi, kamar yadda ka sani idan aka zo ana cewa, Najeriya sai Asiwaju, Kano Sai Abba, Dan Majalisar Tarayya sai wane, Sanata sai wane.
"Amma sai aka riƙa tsallake sunan Sanata ana faɗin wani abu na daban. Mataimakin gwamna kuma ya zo shi ma ya yi maganganu na daban," in ji Faizu Alfindiki.
A gaban kowa ya faɗi hakan ciki har da shugaban Jam'iyyar APC a jihar, amma babu wanda ya ce komai a cewar Hoarabil Alfindiƙi, wanda kuma hakan "anti-fati ne".

Asalin hoton, Abba Abdullahi Bari
Ibrahim Adamu Tiga ɗaya ne daga cikin magoya bayan Honarabil Abba Bichi, wanda ya ce waɗannan zantukan kawai zarge-zarge ne da ba su da tushe ballantana makama.
"Ba su da hujjar da za su ce ana yi wa Sanata Barau maƙarƙashiya kan takarar da yake yi, wannan abu da yake faruwa Mataimakin Gwamna Murtala Sule Garo ne ya yi ta, ya ce Gwara da kuka faɗa timawa su ji da kunnensu," in ji Tiga.
Ya ce su dai APC suke yi amma yana kira da "dole a sakar wa Abba Bichi Mara.
Shugabancin APC na jihar da shi ma wasu ke zargin "yana tare da su Abba Bichi", bai ce komai ba kan wannan dambarwa.
Sai dai BBC ta ruwaito Kwamishinan ilimi na Jihar na cewa ba su san komai ba bayan fatan cin nasarar jam'iyyarsu ta APC a Kano.
Sai dai masu sharhi na cewa matuƙar ba a ɗauki matakin kan rikicin ba, ka iya zama wani abu da zai haifar da abin da ake gudu a siyasance.





























