Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Isra'ila da Hezbollah ke son kame ganuwa mai shekara 900?
- Marubuci, Kaine Pieri
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Wani hoton bidiyo da sojojin Isra'ila suka saki ya nuna wasu dakarun sojin ƙasar na ratsawa ta cikin wata tsohuwar ganuwa da ke kan tsauni wadda aka gina tun zamanin da, kafin daga bisani dakarun su kafa tutar Isra'ila. Isra'ila ta yi iƙrarin kame gidan sarautar Beaufort Castle da ke kudancin Lebanon, a karo na biyu.
"A ranar Lahadi, bayan kame ganuwar, firaiministan Isra'ila ya kira hakan da 'wani mataki mai muhimmanci da kuma babban sauyi a manufofinmu.'"
"Mun cire tsoro," in ji Benjamin Netanyahu. "Muna ɗaukar matakin jagoranci. Muna aiki a dukkan ɓangarori — a Siriya, a Gaza, a Lebanon."
"Hakan na zuwa ne yayin da dakarun Isra'ila ke ƙara kutsawa cikin yankin Lebanon, har sun ƙetare iyakarsu ta farko da aka kafa a kogin Litani."
"Birtaniya da Faransa da Jamus sun soki sabbin hare-haren Isra'ila a kan Lebanon, yayin da rundunar sojin Isra'ilar (IDF) ta gargadi karin mazauna su fice daga wani babban yanki na kudancin Lebanon. Firaiministan ƙasar Leabon ya zargi Isra'ila da aikata 'hukunci na kan mai uwa da wabi'."
Wannan ba shi ne karo na farko da Isra'ila ta yi iko da ganuwar Beaufort ba. Rundunar sojin Isra'ila ta ƙwace ganuwar shekaru 44 da suka gabata, a lokacin abin da Isra'ilawa ke kira Yaƙin Lebanon na Farko. Don fahimtar dalilin da ya sa ake gwabza yaƙi mai tsanani kan wannan wuri, ya dace a duba tarihin ganuwar da kuma muhimmancinta da na tsaunin da take kansa, ta fuskar dabarun soja.
Wasu masana tarihi na ganin cewa an fara yi wa tudun garkuwa ta hanyar gina takanga tun a zamanin Romawa — amma ganuwar yadda take a yau ta samo asali ne daga ƙarni na 12.
A zamanin Yaƙin da mabiya addinin Kirista suka ƙaddamar — tsakanin ƙarshen ƙarni na 11 zuwa na 13 — an ga rundunonin Turai suna gina jerin ganuwa a saman tuddai a yankin Levant, domin kare hanyoyin da ke tsakanin bakin teku da garuruwa na cikin ƙasa. Ganuwar Beaufort ta zama ɗaya daga cikin mafi muhimmanci. A shekara ta 1190, Salahuddeen, jagoran Musulmi da ya yaƙi mayaƙan Kirista kuma ya sake fasalin yankin, shi ne ya ƙwace ganuwar.
Majiyoyin turai sun ce ganuwar ta samo sunanta ne na "Beaufort" ne daga harshen Faransanci da ke nuni da yadda aka aka gina ganuwar a kan tudu. Sunanta na Larabci shi ne Qal'at al-Shaqif ko kuma Shaqif Arnoun da ke nufin ganuwa a kan tsauni.
Tarihinta na da alaƙa da irin yadda aka gina ta wanda ya zama na daban, kasancewar ta haɗa tsarin gini da mayaƙan Kirista da ake kira Crusader da kuma tsarin gini na Musulman gabashi. Kuma tun a shekarar 2024, ganuwar ta Beaufort ta shiga jerin wuraren tarihi da ke ƙarƙashin kariyar yarjejeniyar Hague wadda ta hana a taɓa su ko da a lokacin rikici.
Daraja da sunan ganuwar ta Beaufort ta sake bayyana ne a lokacin yaƙin duniya na biyu a ƙarni na 20, a daidai lokacin da ake ci gaba da fafatawa tsakanin Larabawa da Isra'lawa inda kudancin ƙasar Lebanon ya zama filin daga.
"Bisa la'akari da muhimmancin ganuwar a yankin, daga shekarun 1970 har zuwa watan Yunin 1982, ta kasance sansanin 'yan gwagwarmayar Falasɗinawa da ke yaƙi da Isra'ila," in ji Farfesa Asher Kaufman na Jami'ar Notre Dame.
A lokacin mamayar Isra'ila ta shekarar 1982, an gwabza ɗaya daga cikin mafi tsananin faɗace-faɗace a wannan ganuwa. Ɗaya daga cikin fafatawar da aka fi rubuta tarihinta a wannan rikici, ita ce yaƙin Shaqif wanda har yanzu yana da matsayi mai muhimmanci a cikin tarihin sojin Isra'ila da na Lebanon, in ji Kaufman.
Bayan da a ƙarshe ta ƙwace ganuwar Beaufort a ranar 6 ga Yunin shekarar 1982, Isra'ila ta yi amfani da ita a matsayin wurin sa ido a cikin 'yankin tsaro' da take iko da shi a kudancin Lebanon, har zuwa janyewarta a shekara ta 2000.
Ganuwar wadda take kan wani tudu mai duwatsu kusa da garin Arnoun, a lardin Nabatieh, na ba da damar ganin nesa zuwa arewacin Isra'ila da filayen kudancin Lebanon, har ma da kwarin Litani.
A tarihi, duk wanda ya mallake ta zai iya sa ido kan muhimman hanyoyi da suka nufi kudanci, wanda ya sa ta zama wuri da ake kai wa hari akai-akai daga ɓangarori masu hamayya tun daga zamani da har zuwa yau.
Amma ƙananan hanyoyinta masu duwatsu, ɗakuna masu sulke, tankunan ruwa da rijiyoyi sun ba mayaƙa damar jurewa na dogon lokaci a lokacin da aka yi musu ƙawanya.
A cewar Dr Lina Khatib, ta cibiyar bincike kan manufofi da ƙudure-ƙuduren gwamnatocin ƙasashe a duniya reshen Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, sake ƙwace ganuwar da Isra'ila ta yi an yi shi ne musamman domin raunana ƙwarin gwiwar Hezbollah da magoya bayanta.
"Kame ganuwar Beaufort na nuna cewa ƙungiyar Hezbollah ba za ta iya hana Isra'ila ci gaba da mamayar yankunan Lebanon ba," in ji ta.
Wuri ne na tarihi da ke samun kariya, wanda aka gyara kuma aka sake buɗe shi ga baƙi a 'yan shekarun nan, ana kallon ganuwar Beaufort a matsayin wani ɓangare na tarihin da al'adun al'ummar ƙasar Lebanon.
A ranar Litinin ne kuma, kakakin ƙungiyar Tarayyar Turai, Anouar El Anouni, ya ce: 'Muna kira ga Isra'ila da ta dakatar da hare-harenta a Lebanon, sannan ta mutunta kasancewar Lebanon ƙasa mai cin gashin kanta.