Hotuna sun nuna yadda Isra'ila ke ruguza gine-gine a kudancin Lebanon

    • Marubuci, Emma Pengelly
    • Marubuci, Merlyn Thomas
    • Marubuci, Barbara Metzler
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Verify
  • Lokacin karatu: Minti 5

Isra'ila na ci gaba da ruguza garuruwa da ƙauyuka a kudancin Lebanon, kamar yadda hotunan tauraron ɗan'adam da BBC ta tantance suka nuna.

Sashen tantance bayanai na BBC ya gano sama da gine-gine 1,400 da aka ruguza tun ranar 2 ga watan Maris, bayan hujjoji da aka samu.

Wannan kaɗan ne cikin irin gine-ginen da hare-haren Isra'ila ta sama suka lalata, saboda su kaɗai aka iya samu sakamakon rashin kai wa fagen daga. Sai dai ɓarnar za ta iya fin haka.

Aikin rusa waɗannan gidaje ya zo ne bayan da ministan tsaron Isra'ila Israel Katz ya ba da umarni ranar 22 ga watan Maris cewa "a gaggauta ruguza gidajen ƴan Lebanon" kusa da iyaka da Isra'ila, a matsayin wani ɓangare na yaƙi da Hezbollah.

Ruguza waɗannan garuruwa da ƙauyuka zai iya zama a matsayin laifin yaƙi, kamar yadda wani ƙwararre kan dokokin ƙasa da ƙasa ya shaida wa sashen tantance bayanai na BBC.

Dakarun tsaron Isra'ila sun ce suna aiki yadda dokoki suna tsara kuma ba sa rusa wani gini haka kawai sai idan ya zama dole.

Sun ƙara da cewa Hezbollah ta saje cikin gine-ginen jama'a a yankin shi ya sa suke far musu, sai dai babu wasu hujjoji da suka bayar kan haka.

A ranar 2 ga watan Maris ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran ta harba rokoki da jirage mara matuki zuwa cikin Isra'ila a matsayin martani na kashe jagoran addinin Iran a farkon fara yaƙin Amurka-Isra'ila da kuma Iran.

IDF ta mayar da martani ita ma ta hanyuar kai jerin hare-hare a faɗin Lebanon, inda ta ce ta kai su ne kan gine-ginen Hezbollah, inda ta kuma kaddamar da mamaya ta ƙasa a kudancin Lebanon.

Tun da farko, wani mai magana da yawun dakarun Isra'ila ya bai wa fararen hular da ke zaune kusa da kan iyaka umarnin cewa su fice ranar 2 ga Maris. Kwanaki kalilan bayan nan, aka faɗaɗa umarnin zusa waɗanda ke zaune a kudancin kogin Litani mai nisan kilomita 30 da kan iyaka. Haka kuma aka sake bai wa mazauna gefen kogin Zahrani mai nisan kilomita 40 da su ma su bar wurin nan take.

A ranar 16 ga watan Maris, dakarun na Isra'ila suka fara mamaya ta ƙasa kan Hezbollah.

An kiyasta cewa rikicin ya ɗaiɗaita sama da mutum miliyan 1.2 a fadin Lebanon, ciki har da 820,000 da suka fito daga kudancin ƙasar, a cewar alkaluman Ofishin Kula da Jin Kai na Majalisar Ɗinkin Duniya. Ofishin ya ce yaƙin a Lebanon ya tilastawa mutane da dama tserewa zuwa arewacin ƙasar ko kuma tsallakawa zuwa Syria.

Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce sama da mutum 2,000 ne aka kashe tun fara yaƙin. Hukumomin Isra'ila sun ce Hezbollah ta kashe musu sojoji 13 da fararen hula biyu a tsawon makonni shida da suka wuce.

A yanzu da wuya mutum ya iya gane wasu garuruwa da kuma ƙauyukan da ke kan iyakokin Lebanon. A baya an san garuruwan da tituna cike da mutane ga kuma manyan gine-gine, sai dai yanzu hotunan bidiyo sun nuna yadda wuraren suka zama ɓaraguzai da kuma ƙura.

Garin Taybeh mai nisan kilomita huɗu daga kan iyaka, ya fuskanci gagarumin rusau. Hotunan bidiyo 11 da aka tantance sun nuna yadda hare-hare suka tayar da garin baki ɗaya.

Wasu hotunan tauraron ɗan'adam da aka ɗauka ranar 28 ga Fabrairu da 11 ga Afrilu, sun nuna sama da gine-gine 400, ciki har da Masallaci waɗanda aka ruguza a can.

A ɗaya gefen, a garin Khiam da ƙauyukan Qouzah, Deir Seryan, Markaba da kuma Aita al-Shaab, hotunan bidiyo sun nuna yadda aka rusa gin-ginen wurin ta hanyar amfani da abubuwan fashewa.

Mun gano cewa an ruguza gine-gine sama da 460 a ƙauyen Aita al-Shaab kaɗai.

A garin Naqoura da ke gaɓar teku, wasu abubuwan fashewa daga hare-haren Isra'ila sun lalata hedkwatar tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a kudancin Lebanon.

Wata mai magana da yawun tawagar a Lebanon, ta ce ta ga lokacin da ake rusa wasu gine-gine a farkon watan Afrilu.

Hotuna da muka tantance sun nuna aƙalla gine-gine 100 da aka ruguza a garin Naqoura a makonnin baya-bayan nan.

Ardiel ta ce an rusa yawancin gine-ginen da ke gefen hedkwatar wanzar da zaman lafiya na MDD, inda ta ce abin da ke faruwa a garin "yana tayar da hankali". "Waɗannan ba gine-gine ne kawai ba, suna wakiltar al'ummomi ne," in ji ta.

Rusa gine-gine da gangan ba wani sabon abu bane a wajen sojojin Isra'ila. Ta aikata irin haka a faɗin yankun Gaza lokacin yaƙi wanda ya faru sakamakon kai hari da cikin Isra'ila ranar 7 ga Oktoban 2023 da ƙungiyar Hamas ta yi.

"Abu ne a fili cewa tun ranar 7 ga Oktoba kuma tun bayan shiga yaƙi tsakanin Isra'ila da Hezbollah akwai tsari a wajen Isra'ila na sake duba batun iko a yankin," in ji Renad Mansour, mataimakin darekta a Chatham House da ke Birtaniya.

Masana shari'a da dama sun faɗa wa BBC cewa lalata gine-gine ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa, in har ba wai ya zama dole ba.

Farfesa Ben Saul, Wakilin Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman kan kare hakkin ɗan'adam, ya ce "ruguza gine-ginen mutane, musamman a Kudancin Labanon, har ma da wasu sassan birnin Beirut" da alama ya saɓa wa dokar jin kai ta ƙasa da ƙasa.

Al'ummar Musulmi 'yan Shi'a su ne mafi rinjaye a kudancin Lebanon, amma akwai sauran mutane har da Kirista da ke zaune a can.

"A wasu wurare hare-haren na son lalata ƙauyukan da ƴan Shia suka fi yawa da ke kudanci, abin da yake shafar fararen hular da Hezbollah ta shiga cikinsu," in ji Saul.

Dakarun tsaron Isra'ila sun mayar da martani tare da watsi da batun cewa suna son ƙawar da fararen hula ko kuma ɗaiɗaita su musamman kan irin addini da suke yi ko kuma ƙungiya da suke ciki a Lebanon.