Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda magoya bayan Obi da Kwankwaso suka kafa ƙungiya don samun tikitin ADC
Magoya bayan tsoffin yan takarar shugaban kasa a Najeriya Peter Obi, da kuma Rabiu Musa Kwankwaso sun kafa wata kungiya mai suna Obi–Kwankwaso (OK Movement) da ta soma tattaunawa domin ganin jam'iyyar ADC ta tsayar da su takarar shugaban kasa da mataimaki a zaben 2027 da ke tafe.
Ƙungiyar, wadda aka kafa a Abuja a ranar Litinin, ta ce tuni ta soma samar da rassanta a jihohi 36 na ƙasar da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da naɗa shugabanninta na jihohi da yankuna domin jagorantar yaɗa ayyukanta.
Sakataren watsa labaran ƙungiyar na ƙasa, Justin Ijeh, ya bayyana ta a matsayin gamin gambiza, don haɗa karfi da karfe tsakanin kungiyar magoya bayan Peter Obi ta Obidient Movement, da kuma ta magoya bayan Kwankwaso, wato Kwankwasiyya.
Wannan dai na nuna wani irin sabon salo na sake daure damara yayin da ake ta kulla mu'amalar siyasa, sakamakon rashin tabbacin wanda zai lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na ADC kafin babban zaɓen 2027.
Da yake jawabi ga manema labarai, kakakin kungiyar ya bayyana cewa sabuwar kungiyar ta kunshi mambobi daga Kwankwasiyya, da Obidients, da jam'iyyar NNPP, da Labour da kuma wasu daga ADC.
Bayyanar ƙungiyar OK Movement dai, na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ja-in-ja tsakanin magoya bayan Peter Obi, da na tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar, wanda yayin wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan ya bayyana aniyarsa ta sake yin takara a zaben mai zuwa.
Wasu magoya bayan Obi a shafukan sada zumunta na ganin cewa kamata ya yi Atiku ya hakura ya ci girma, ya ba wa masu karancin shekaru dama su gwada ta su sa'ar, duba da yadda ya dade yana yin takarar shugaban kasa ba tare da ya yi nasara ba.
Sai dai da yawan magoya bayan Atiku Abubakar na ganin cewa sabbin yankan rake ba za su iya kayar da shugaba Bola Ahmed Tinubu ba, don haka akwai bukatar gogaggen dan siyasa da ya ga jiya ya ga yau irinsa, da ya san siyasar kasar ciki da bai ya shige gaba wajen yin takara idan har ana son a samu nasara.
Wato irin abun nan da Hausawa kan ce idan ruwa ya baci, dole sai kwarawan asali, wato, bigi sai bigi, babban goro sai magogin karfe.
To sai dai a cewar Ibrahim Husaini Abdulkarim, wani na hannun daman Peter Obi, daya daga cikin dalilansu na bijiro da wannan tafiya shi ne bukatar ganin kudancin kasar ya kammala wa'adin shekara takwas dinsa, kafin mulki ya sake komawa Arewa.
Ya ce ''Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cikin wadanda suka yadda da haka, shi ya sa aka zauna da shi kuma ya nuna yana goyon bayan a yi wannan tafiya tare da shi''
Shima bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna cewa wannan shi ne kadai mafita a halin da ake ciki.
A cewar Habibu Saleh Mailemo, wani na hannun daman Sanata Kwankwaso ''Ita kanta jam'iyyar ADC din ta samu karbuwa ne sakamakon shigar wadannan mutane biyu cikinta.
''Dama an jima ana wannan tattaunawa, kuma idan ka kalli shekarunsu, da kwarewarsu, da kuma irin yadda suke da mutane za ka ga cewa abun da ake bukata kenan, Obi sama da mutum miliyan shida suka zabe shi, Kwankwaso sama da mutum miliyan daya, don haka idan aka hade ba shakka za a samu nasara.
Baya ga wadannan yan takara dai, akwai kuma tsohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi, wanda shima yake ci gaba da neman goyon bayan 'yan jama'iyyar ta ADC don samun tikitin.