Ko sabon tsarin Amurka zai kawar da ta'addanci a Afrika?

'

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, '
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Amurka ta nuna damuwa kan yaɗuwar ƙungiyoyin mayaƙa masu tsattsauran ra'ayi a yammacin Afrika musamman a yankin Sahel da Tafkin Chadi.

Gwamnatin Trump ta yi gargaɗi kan yadda ta ce mayaƙan ke ƙara ƙarfi a yammacin Afrika bayan ta yi iƙirarin murƙushe su a ƙasashen Iraqi da Syria.

Amurka dai ta bayyana haka ne a cikin wani rahoto da ta fitar kan sabon tsarin yaƙi da ta'adanci a 2026.

A cikin rahoton gwamnatin Trump ta bayyana yammacin Afrika da yankin Sahel da Tafkin Chadi da ya haɗa yankin arewacin Najeriya a matsayin wata matattarar mayaƙa masu tsattsauran ra'ayi inda bayan iƙirarin na Amurka na murkushesu a yankin gabas ta tsakiya, a yanzu sun tare a Afrika.

Yankin na Afrika dai na fama da matsalar masu tayar da ƙayar baya saboda abinda ta kira raunin gwamnatoccin ƙasashen na Afrika.

Masana tsaro irinsu Dokta Kabiru Adamu ya ce rahoton ya saɓawa tsaren tsaren da aka rubuta a baya:

''Wannan akwai maganganu na siyasa da yawa a ciki,misali a ciki shugaban ƙasa mai ci a yanzu ya nuna cewa lokacin da ya yi mulki na farko ya tarwatsar da ƙungiyar IS da ƙungiyar Alqaeda daga Iraƙi da Syria''

Bayan haka sai suka taso suka dawo nahiyar Afrika kuma kamar yadda ya ambata a cikin tsarin gwamnatin da ya karɓa mulki daga gareta (gwamnatin Biden) ita ta bari har hakan ya faru'',

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''Shugaba Trump ya ayyana wasu wurare 6 inda ya ce a nan ne a Afrika waɗannan ƙungiyoyi suka dawo ciki har da da Afrika ta yamma da yankin Sahel da Tafkin Chadi da ƙasar Mozambique da Sudan da kuma Somaliya'', in ji shi.

Ɗaya daga cikin manufar sabbin dubarun yaƙi da ta'adacin da Amurka ta bayyana shi ne hana yaɗuwar ƙungiyoyin ta'adanci waɗanda manufarsu ita ce kai wa Amurka hari da kuma jadadda manufar kare mabiya adinin kirista da ta ce suna fuskantar 'barazana' musaman a Najeriya

Sai dai Dokta Kabiru Adamu ya ce wannan ba zai sa Amurka ta kafa sansani ba

''To a ƙarkashin wannan ne ita Amurka ba za ta kafa sansani ba amma za ta riƙa tura ƙananan tawaga da niyyar cewa su taimakawa gwamnatoccin Afrika kare kawunansu''

''Abin nufi a nan shi ne ita Amurka ba za ta ɗauki nauyin ba, sai dai ƙasashen Afrika su ɗauki nauyin da taimakonta''

''Abu na biyu shi ne ƙarfafa alaƙa tsakanin tsaro da kasuwanci, ma'ana duk inda za ta zo ta taimaka toh sa an biya mata buƙatunta na kasuwanci''

''A fahimtarmu abinda ya kamata kowace ƙasa ta tsaya tantance shin me nene muradunta kuma shi za ta yi ƙoƙarin ta cimma a dangantaka game tsaro da yaƙi da ta'addanci tsakaninta da ƙasashen waɗannan yanki''. in ji shi

Gwamnatin Amurka ta ce za ta ci gaba da aiki da gwamanatoccin ƙasashen Afrika da ke fuskantar barazanar ƙungiyoyi masu alaƙa da IS da Alqaeda da kuma ke yi wa Amurka barazana amma a cewarta har sai ƙasashen sun tabbatar da tsaron kan iyakokinsu da toshe duk wata kofa ga ƴan ta'ada.