Ƴan wasan da suka haura shekara 40 suna taka leda

....

Asalin hoton, Multiple/Social Media

    • Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

A yayin da yawancin ƴan wasa ke yin ritaya yayin da suka ɗan haura shekara talatin, akwai wasu ƴan wasa ƙwallon ƙafa ƙalilan da ke ci gaba da nuna bajinta duk da cewa shekaru sun ɗan kama su.

Ta hanyar nuna ƙwazo da horo na musamman, da jajircewa a fagen wasa, da kuma kiyaye lafiyar jiki, waɗannan ƴan wasa har yanzu suna fafatawa a matakin ƙwararru—har ma wasu daga cikinsu suna taka rawar gani a ƙololuwar wasan.

Tun daga fitattun gwarazan ƴan wasa irin su Cristiano Ronaldo da Luka Modrić har zuwa taurari masu ɗorewa a fagen kamar Manuel Neuer, waɗannan ƴan wasa suna tabbatar da cewa shekaru ba su zama babban cikas a garesu ba.

Cristiano Ronaldo

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Cristiano Ronaldo ya fara buga wasan tun yana da shekaru bakwai, amma ya shiga matakin ƙwararru ne a hukumance yana da shekaru 16.

A watan Yunin 2025, Ronaldo ya rattaba hannu kan tsawaita kwantiraginsa da ƙungiyar Al Nassr na tsawon shekara biyu, lamarin da zai sa ya ci gaba da zama a ƙungiyar har zuwa shekarar 2027.

A baya, ya buga wa ƙungiyoyin Sporting CP da Manchester United da Real Madrid da Juventus wasa, inda ya samu gagarumar nasara tare da kafa tarihin zura ƙwallaye a kowace ƙungiya.

Ronaldo na ɗaya daga cikin ƴan wasan da ya fi lashe kyautuka a tarihin ƙwallon ƙafa, inda ya lashe kofuna 35 a tarihin rayuwarsa, da suka haɗa da gasar cin kofin zakarun Turai guda biyar, da gasar UEFA Nations League biyu da kuma gasar cin kofin nahiyar Turai ta UEFA. Ya riƙe tarihin mafi yawan ƙwallaye a gasar zakarun Turai.

Kazuyashi Miura

Kazuyoshi Miura, shi ne ƙwararen ɗan wasan ƙwallon ƙafa da ya fi tsufa a duniya.

Ana yi masa laƙabi da 'King Kazu' a Japan, kuma yana ɗaya daga cikin ƴan wasan da aka fi so a ƙasar, sannan shi ne fuskar gasar J League lokacin da aka ƙaddamar da ita a shekarar 1993.

Ya fara ƙwallon ƙafa ne tare da ƙungiyar Santos ta ƙasar Brazil a shekarar 1986, kuma ya taɓa buga wa ƙungiyoyi wasa a ƙasashen Italiya da Croatia da Australia.

Wannan ɗan wasan gaba zai shiga kakar wasa ta 42 a cikin dogon tarihinsa na wasanni, bayan ya tsawaita yarjejeniyar zaman aro a ƙungiyar Fukushima—daga ƙungiyar Yokohama FC ta gasar J2 League—har zuwa watan Yunin 2027.

Rabiu Ali 'Pele'

...

Asalin hoton, Kano pillars

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rabiu Ali , wanda aka fi sani da laƙabin "Pele", ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Najeriya da ke buga wasa a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar Kano Pillars.

Shi ne kyaftin ɗin Kano Pillars kuma ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasa masu tasiri a tarihin ƙungiyar, tare da kasancewa ɗaya daga cikin ƙwararrun ƴan wasan tsakiya da suka yi fice a gasar firimiyar Najeriya (Nigeria Premier Football League).

Ali ya fara wasa a matakin ƙwararru ne a ƙungiyar Nasarawa United kafin ya koma Kano Pillars a shekarar 2009. Tun bayan komawarsa ƙungiyar, ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe gasar lig a lokuta da dama, sannan ya tabbatar da kansa a matsayin ɗaya daga cikin ƴan wasan tsakiya da suka fi zura ƙwallaye a gasar cikin gida ta Najeriya.

A matakin ƙasa da ƙasa, Ali ya wakilci tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, inda ya halarci gasar cin kofin ƙasashen Afirka na ƴan wasan cikin gida (CHAN) a shekarun 2014 da 2018.

Manuel Neuer

Neuer

Asalin hoton, Getty Images

Manuel Peter Neuer ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Jamus wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida kuma kyaftin ɗin ƙungiyar Bundesliga ta Bayern Munich.

Ana yi masa kallon ɗaya daga cikin masu tsaron gida mafi ƙwarewa a tarihi.

Neuer ya fara taka leda a Schalke 04 inda ya lashe kofunan DFB-Pokal da DFL-Ligapokal, kuma an naɗa shi kyaftin ɗin ƙungiyar a shekara ta 2010. A 2011, ya koma a Bayern Munich kuma ya lashe kofuna 32.

A matakin ƙasa da ƙasa, shi ne ke riƙe da tarihin mai tsaron gida da ya fi yawan buga wasanni a gasar cin kofin duniya ta FIFA.

Luka Modric

Modric

Asalin hoton, Getty Images

Ana kallon Luka Modric a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan tsakiya a tarihi, tare da kasancewa babban ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Croatia a tarihi.

Kasancewar ya lashe manyan kofuna guda 34, shi ne ɗan wasan Croatia da ya fi kowa samun nasarori, kuma yana matsayi na uku wajen yawan buga wasanni a matakin ƙasa da ƙasa a tarihin ƙwallon ƙafa.

Bugu da ƙari, yana ɗaya daga cikin ƴan wasa ƙalilan da suka buga wasanni sama da 1,100 a tsawon rayuwarsu ta ƙwallon ƙafa.

Modrić ya fara taka leda ne da ƙungiyar Dinamo Zagreb ta ƙasar Croatia daga shekarar 2003 zuwa 2008 – inda a tsakanin lokacin ya taɓa buga wasa a matsayin ɗan wasan aro a ƙungiyoyin Zrinjski Mostar da Inter Zaprešić – tare da lashe kofuna shida na cikin gida.

Ya koma ƙungiyar Tottenham Hotspur a shekarar 2008, inda ya taimaka musu wajen samun gurbin shiga gasar UEFA Champions League a shekarar 2010; wannan shi ne karo na farko da ƙungiyar ta samu damar shiga gasar cikin kusan shekara 50.

Yanzu haka yana taka leda ne a ƙungiyar AC Milan ta ƙasar Italiya.