Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa muke tsoron wasu abubuwa da wataƙila ba za su cutar da mu ba?
- Marubuci, Daisy Stephens
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Yaya kake ji idan gizo-gizo ya shiga cikin ɗakin zamanka ba zato ba tsammani?
Yawancin gizo-gizo suna da dafi, amma kaɗan ne daga cikin su ke da haɗari ga ɗan'adam.
Cibiyar Nazarin Muhalli da Ilimi, wato (Institute for Environmental Research and Education) ta ce ana kyautata zaton ƙasa da mutane 10 ne ke mutuwa a duniya a duk shekara sakamakon cizon gizo-gizo, duk da cewa samun sahihan bayanai kan hakan na da wuyar gaske.
Duk da haka, mutane da dama, za su ce suna jin tsoron gizo-gizo.
Ni kaina ba na iya yin barci idan na san akwai gizo-gizo a ɗakina, kuma tunanin gidajen yanar gizo kaɗai na iya sa ni fargaba da tsoro.
A lokuta da dama, irin wannan tsoro mai tsanani yana kasancewa ne kan wani abu da a zahiri ba zai iya yi mana mummunar illa ba. To amma me ya sa irin waɗannan tsorace-tsorace suka zama ruwan dare, kuma daga ina suke samo asali?
Lokacin da tsoro ke rikidewa zuwa matsanancin tsoro
A cewar Vanessa LoBue, farfesar ilimin halayyar ɗan Adam a Jami'ar Rutgers da ke jihar New Jersey a Amurka, tsoro wani bangare ne a rayuwar ɗan Adam.
Farfesar ta ce, "Tsoro yana da muhimmanci domin yana kare mu daga abubuwan da ka iya zama masu haɗari gare mu."
A cewar András Zsidó, daraktan cibiyar binciken fahimta da motsin rai (Visual Cognition and Emotion Lab) a Jami'ar Pécs da ke ƙasar Hungary, idan tsoro ya kai wani mataki mai tsanani kuma ya fara hana mutum gudanar da harkokinsa na yau da kullum, ana iya ɗaukarsa a matsayin matsanancin tsoro wato (phobia).
Ya ce: "Za mu iya kallon hakan a matsayin wani mataki ne da ke farawa da tsoro na yau da kullum, domin kusan kowa na tsoron wani abu. Amma idan wannan tsoron ya fara wuce gona da iri ga rayuwar mutum ta yau da kullum, a nan ne za mu iya cewa ya rikide zuwa phobia."
Ita ma Vanessa LoBue, ta ce matsanancin tsoro kan kasance ya fi haɗari da abin da ake tsoro ke haifarwa a zahiri.
Tace, " Misali, a wasu sassan duniya kamar Birtaniya, inda na ke rayuwa, yawancin wasu nau'in macizai ba su da haɗari ga ɗan Adam. Saboda haka, tsananin tsoronsu na iya zama ba shi da wata hujja mai ƙarfi, kuma ba za a ɗauke shi a matsayin phobia ba. Sai dai a wasu sassan duniya, inda macizai masu dafi suka fi yawa, irin wannan tsoro na iya kasancewa mai dalili.
Shin ana haihuwar mutum da tsoro ko kuma yana koyon sa ne a rayuwa?
Duk da cewa wasu nau'ikan matsanancin tsoro na zama ruwan dare a tsakanin mutane, yawancin masana ba su yar da cewa ana haihuwar mutum da su ba. A ra'ayin LoBue, tsoro wani yanayi ne da jarirai ƙanana ba sa iya ji tun daga haihuwa.
Ta ce: "Ba a ganin tsoro sai daga baya, domin tsoro yana buƙatar mutum ya fahimci cewa wani abu na iya zama barazana a gare shi."
Saboda haka, idan ba a haifi mutum da tsoron gizo-gizo ko macizai ba, me ya sa mutane da yawa ke fama da matsanancin tsoro ga irin waɗannan halittu?
Stefanie Hoehl, farfesar ilimin halayyar ɗan Adam a Jami'ar Vienna da ke ƙasar Austria, ta gudanar da wani bincike da ya gano cewa idan jarirai suka ga macizai ko gizo-gizo, ƙwayar idanunsu na faɗaɗa fiye da lokacin da suka ga furanni ko kifi.
Faɗaɗar ƙwayar ido na iya zama alamar cewa suna hango wani abu da ka iya zama haɗari.
Hakan na da alaƙa da kunnawar wani tsarin jiki da ake kira noradrenergic system, wanda ke taka rawa a bangaren jiki wajen "yaƙi ko gudu" idan ya fuskanci barazana.
Wannan martani kan haifar da ƙaruwa a bugun zuciya da hawan jini da makamantansu, yayin da jiki ke shirya ko dai ya tsere daga abin da yake gani a matsayin haɗari ko kuma ya tunkare shi.
Sai dai Hoehl ba ta yar da cewa ana haihuwar mutum da irin waɗannan tsorace-tsorace ba. Amma ta ce akwai wasu abubuwa a muhallinmu da muke iya ganewa da sauri fiye da sauran abubuwa, wataƙila saboda yadda suke motsi.
Amma kasancewar ɗan Adam yana da wata halitta ta dabi'a da ke sa shi saurin koyon tsoron wasu abubuwa, abin da masana ke kira "preparedness theory", ba shi kaɗai ba ne ke haifar da tsananin tsoro ko phobia.
Masaniyar ta ce fuskantar wata mummunar ƙwarewa kai tsaye da wata dabba ko wani abu wata hanya ce mai sauri da kan sa mutum ya fara jin tsoronsa, musamman idan tun farko yana da wata dabi'ar tsoron irin wannan abin.
Sai dai kuma mutum na iya koyon tsoron wani abu ta hanyar ganin yadda wasu ke mummunan martani a kansa.
LoBue ta ce: "Kana iya fuskantar wani yanayi a jiki, kamar wani abu ya cije ka ko kuma ya firgita ka."
Ta ƙara da cewa: "Sannan idan mahaifiyarka ta nuna tsoro ko ta ce, 'Eh, wannan abu yana da haɗari sosai,' hakan kan ƙara yiwuwar ka koyi jin tsoron abin."
Saboda haka, kamar yadda Hoehl ya bayyana, ana iya samun irin wadannan tsorace-tsorace masu tsanani ayi gadonsu.
Kallon finafinai
Saboda kasancewar abubuwan da mutum ke fuskanta a rayuwa na taka rawa wajen gina tsoro a zukata, LoBue na ganin cewa al'adun zamani da ake yaɗawa ta kafafen watsa labarai ma suna da tasiri wajen sanya tsoron macizai da gizo-gizo ya zama ruwan dare.
Ta ce: "Ku dubi fina-finai, ko dubi littattafai. Yaushe ne aka nuna macizai ko gizo-gizo a matsayin masu ceto? Ba a taɓa yi ba."
A cewarta, sau da yawa waɗannan halittu ana nuna su ne a matsayin abin tsoro ko haɗari a cikin fina-finai da littattafai, lamarin da ka iya ƙarfafa tsoron da mutane ke ji game da su.
Wataƙila akwai wani ƙarin dalili da ke da alaƙa da matsanancin tsoron abubuwan da ke cikin muhalli, wanda masana ke kira biophobia, wato tsananin tsoron wasu halittu ko abubuwan da ake samu a muhalli.
András Zsidó, ya gudanar da wani bincike don gano ko akwai alaƙa tsakanin yadda wurin zama yake da yawan gine-gine da ci gaban birane, da kuma yiwuwar mutum ya kamu da tsoron dabbobi. Binciken nasa ya nuna cewa, yayin da birane ke ƙara faɗaɗa, matsanancin tsoron halittun da ke cikin muhalli na ƙaruwa.
Idan aka yi la'akari da cewa sama da kashi 80 cikin 100 na mutanen duniya a yau suna zaune ne a birane, hakan na iya taimakawa wajen bayyana dalilin da ya sa matsanancin tsoron dabbobi ya zama ruwan dare a tsakanin mutane.
Yadda ake daina tsoron abubuwan da ke tsoratar da mu
Masana da dama sun amince kan abu biyu game da matsanancin tsoro wato phobia, ana iya shawo kansa, kuma hanya mafi inganci ita ce mutum ya riƙa tunkararr abin da yake tsoro a hankali.
Hoehl ya ce: "Idan kana jin tsoron wani abu, to yana da kyau ka fara tunkararsa a hankali."
LoBue kuma ta ba da shawarar a fara da ƙananan matakai. Misali, mutum zai iya fara kallon hotunan abin da yake tsoro tare da koyan kyawawan bayanai a kansa, kafin daga baya a ƙara kusantar abin a hankali.
Sai dai idan tsoron ya yi tsanani kuma yana matuƙar shafar rayuwar mutum, masana sun ce yana da kyau a nemi taimakon ƙwararru domin samun kulawar da ta dace.
Binciken da Zsidó ya gudanar ya kuma goyi bayan ra'ayin cewa fuskantar abin da mutum yake tsoro ba wai kawai yana taimakawa wajen rage tsoro ba, har ma yana iya hana shi tasowa tun da farko.
Ya ce: "Abin da mutum ya fuskanta da kansa shi ne abu mafi muhimmanci wajen haifar da tsoro. Idan kuwa ƙwarewar ta kasance mai kyau, musamman a lokacin ƙuruciya hakan na iya zama kariya daga ci gaban irin wannan tsoro."
LoBue ta jaddada cewa tsoro wani abu ne da ke taimakawa wajen kare ɗan Adam, kuma mutane suna da ikon shawo kan tsorace-tsoracen da suke fama da su.
Marubucin labarin ya ce shi kansa bai san ko tsoron gizo-gizo da yake fama da shi ya samo asali ne daga iyayensa ba, ko kuma ya koye shi ne daga kallon wani fim, ko kuma saboda bai saba ganin gizo-gizo sosai ba tun yana ƙarami. Ya ce wataƙila duk waɗannan abubuwan ne suka haɗu suka haifar da tsoron.
Sai dai ya ƙara da cewa rubuta wannan labari na iya zama matakin farko a gare shi wajen fara shawo kan wannan tsoro.