Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Auren ƴan tagwayen da ke ɗaukar hankali a Najeriya
- Marubuci, Makuochi Okafor
- Aiko rahoto daga, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Lokacin da baƙi suka taru a wani coci a birnin Ibadan da ke kudu maso yammacin Najeriya a ƙarshen mako, sun san sun zo ganin wani abu ne da ba kasafai ake ganin sa ba.
Wasu tagwaye - Taiwo da Kehinde Oguntoye - suna auren ƴan'uwa mata tagwaye Taiwo da Kehinde Adediran a wani ƙasaitaccen bikin da ake yi wa ma'auranta biyu a lokaci ɗaya.
Ƙabilar Yarabawa da ke yankin kudu maso yammacin Najeriya, sun shahara wurin haihuwar tagwaye amma ba ko da yaushe ne ake samun tagwaye maza kuma a lokaci ɗaya su auri tagwaye mata ba.
Taiwo Oguntoye ya shaida wa sashen Yarabanci na BBC a ranar ɗaurin aurensa, "Mun san tagwaye da yawa, amma jin kamar wannan auren haɗi ne daga Allah. Daman muna burin auren tagwaye.''
"Da yardar Allah, muna addu'ar samun tagwaye a cikin ƴaƴanmu na farko da na biyu. Wannan shi ne burin zuciyarmu."
Ana ɗaukar tagwaye a matsayin albarka a al'adar Yarbawa kuma akasari suna zuwa ne da sunayen da aka riga aka tsara a al'adance. Babban yaron ana kiransa Taiwo, ma'ana "wanda yake gwada duniya", yayin da ƙaramin kuma ake kira Kehinde, ma'ana "wanda ya zo bayansa".
Labarin soyayyar tagwayen dai ya fara ne shekara 10 da suka gabata, a lokacin da su huɗun ke karatu a jami'ar Ibadan.
Wata malama ta gaya wa mazan cewa ta san wasu tagwayen ƴan'uwa mata da ya kamata su haɗu da su.
Taiwo Oguntoye ya ce, "Ba wai ba mu taɓa haɗuwa da wasu tagwaye mata ba ne, mun yi soyayya da wasu tagwayen, amma wani lokacin al'amura ba su kasancewa yadda ake so."
Da farko tagwaye matan sun ƙi amincewa su haɗu da mazan kuma ba su amsa kiran wayar da malamar ta yi ba. Amma daga ƙarshe sun amince su haɗu da su.
Taiwo Oguntoye, mai shekaru 40 a yanzu, ya ce: "A ƙarshe mun ziyarce su, mun tattauna amma ba su da sha'awar ƙulla wata dangantaka da mu a lokacin."
Sakamakon haka sai, ma'auratan sun zama abokai. Sai kuma halin rayuwa ta sanya kowa ya kama gabansa.
Matan da suka yi karatun digiri na biyu a Ibadan, sun tafi ƙasar waje don ci gaba da karatu, yayin da aikin ya kai mazan ƙasashe da dama, ciki har da Amurka da Afirka ta Kudu.
Shekaru da dama sun shuɗe kafin suka sake haɗuwa.
Bayan wani lokaci, ma'auratan sun zo sun shaƙu da juna.
Iyalan ma'auratan sun ji daɗin dangantakar da tagwayen suka ƙulla- Taiwo Oguntoye ya tuna yadda dangantakarsa da surukansa ta yi kyau nan take.
"Kowa ya yi farin ciki da ganinmu, sai ya ji kamar mun san juna duk tsawon rayuwarmu," in ji shi. "An ɗauke mu kamar ƴaƴa a gidan ubanmu."
Ƴan'uwa masu alfahari da tagwayen ne suka fito ƙwan su da ƙwarƙwatansu a wurin ɗaurin auren.
Wasu tagwaye da dama sun hallara - wataƙila ba abin mamaki ba ne saboda an san angwayen da fafutukar inganta al'adun tagwaye. Ƴan'uwa suna nuna ƙwazo wurin bunƙasa al'adu da ayyukan yawon buɗe ido.
Akwai ƴan bambance-bambance a kamannin angwayen duk da cewa tagwaye ne, amma matan suna kama sosai.
Kehinde Oguntoye ya ce "Matanmu sun yi kama da juna ta yadda har ƴan'uwansu a wasu lokutan sukan kasa gane su, amma mu muna gane matanmu, mun san matanmu sosai."
'Yan'uwan sun ce suna da ɗabi'a iri ɗaya da matansu, suna bayyana kansu a matsayin waɗanda yanayin zamantakewarsu da mutane ke sauyawa daga lokaci zuwa lokaci – wani lokaci su ji yin shiru, wani lokaci kuma su ji cewa suna son hayaniya, ya danganta da yanayin.
Duk da cewa suna da kusanci sosai, ma'auratan ba za su zauna tare ba, in ji Taiwo Oguntoye.
''Muna da wani tsari na musamman kan wannan, na gaba mutane za su san ko me nene.''
A yanzu haka dai ma'auratan na ci gaba da jin daɗin wannan sabon babin na labarin soyayyarsu, wanda ya fara, ya kuma dakata bayan wani lokaci kafin daga baya ya bunƙasa ya rikiɗe zuwa labarin soyayyar da kowa a yankin ke magana a kai.