Fitattun ƴanƙwallo da za su iya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2026

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya FIFA ta bayyana sunayen ƴanwasan da za su fafata a neman lambar yabo ta Ballon d'Or ta shekarar 2026, wadda ake yi wa kallon kyauta mafi girma da muhimmanci da ƙwallo zai iya samu a duniyar tamaula.

Daga cikin ƴan wasan da suka fi ɗaukar hankalin magoya baya a jerin akwai wanda ya fi lashe kyautar a tarihi, Lionel Messi na Inter Miami da Kylian Mbappé na Real Madrid da Vinícius Júnior da Jude Bellingham duka na Real Madrid.

Akwai kuma Erling Haaland na Manchester City da kuma matashin ɗan wasan Barcelona da ke jan zarensa a yanzu Lamine Yamal.

Za a yi bikin karrama ƴanwasan na bana ne a ranar Litinin, 26 ga watan Oktoba a ɗakin taro na London Palladium Theatre da ke birnin Landan da ke Ingila, wanda shi ne karon farko da za a gudanar da babban taron na tamaula a ƙasar.

Wannan ne karo na 70 da za a bayar da kyaututtukan tun bayan da aka fara a shekarar 1956.

BBC ta kankaɗe tare da rairayo wau fitattun ƴanwasan da take tunanin suna kan gaba wajen lashe kyautar ta bana.

Lionel Messi

Shigar da Lionel Messi cikin jerin na bana na daga cikin abubuwan da suka fi ɗaukar hankali.

Messi, wanda ya lashe Ballon d'Or sau takwas, zai sake fuskanci ƙalubale daga wasu daga cikin fitattun matasan ƴanwasan duniya masu tashe, ciki har da Mbappé da Haaland da Vinícius Júnior.

Duk da cewa ɗan wasan na Argentina ya bar manyan ƙungiyoyin Turai, kasancewarsa cikin jerin ya sake nuna irin tasirin da ya ci gaba da yi a duniyar ƙwallon ƙafa.

Ko da aka fara maganar kyautar ta bana, muhawara ta kaure kan yankin da ya kamata wanda zai lashe kyautar ya kasance yana taka leda, inda a ƙarshe hukumar ƙwallon ta duniya ta ce babu ruwanta da yanki.

Messi ya lahe kyautar a shekarun: 2009 da 2010 da 2011da 2012 da 2015 da 2019 da 2021 da 2023.

Mbappe

Real Madrid na da 'yan wasa da dama cikin jerin, amma Kylian Mbappé da Vinícius Júnior na daga cikin waɗanda aka fi sa ran za su iya kasance gaba gaba cikin waɗanda za su iya lashe kyautar.

Kyaftin ɗin na Faransa ya zura ƙwallo 10 a gasar cin kofin duniya ta ƙarshe, inda ya lashe kyautar wanda ya fi zura ƙwallaye, sannan ya zama wanda ya fi zura ƙwallaye a tarihinta da ƙwallo 22 zuwa yanzu.

Tun bayan da ya koma Real Madrid ne matahin ɗanwasan mai shekara 27 yake zura ƙwallaye a raga, amma bai taɓa lashe kyautar mai matuƙar daraja ba.

Ana ganin zai iya kai wa bantensa a bana kasancewar ya nuna bajinta a gasar kofin duniya da gasar zakarun turai da sauransu.

Vinícius

Vinícius Junior na cikin zaratan ƴanwasan da a yanzu ake kallo sosai a ƙungiyar Real Madrid, musamman a cikin ƴanwasan gaba.

Shekarar a ya kusa lashe kyautar ita ce ta 2024, inda ya ƙare a na biyu bayan kusan an ɗauka shi ne, musamman bayan ganin irin rawar da ya taka a shekarar kafin kyautar.

Wannan ne karo na biyar da ɗanwasan gaban na Madrid ya shiga cikin jerin waɗanda za su iya lashe kyautar, amma bai taɓa samun nasara ba.

A shekarar da ta gabata, ɗanwasan ya buga wasa 66, inda ya zura ƙwallo 28, sannan ya taimaka aka zura ƙwallo 16.

Yamal

Ɗaya daga cikin sunayen da suka fi ɗaukar hankali a cikin jerin shi ne Lamine Yamal na Barcelona.

Yamal ya shiga jerin ne a matsayin ɗaya daga cikin matasan ƴan wasan da suka samu damar fafatawa da manyan taurarin duniya.

Shekarunsa da irin yadda yake taka leda sun sanya shi zama ɗaya daga cikin ƴan wasan da magoya baya ke kallo suna nishaɗi sosai a harkar.

Ɗan ƙasar Spain ne, kuma yana cikin zaratan ƴanƙwallon da suka taimaka wa Spain ta lashe gasar kofin duniya ta 2026.

Haaland

Haaland ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƴan wasan da suka fi yin tasiri a gaban raga a Turai.

Ya taka muhimmiyar rawa wajen wakiltar ƙasarsa ta Norway a gasar cin kofin duniya, sannan ya daɗe yana nuna bajinta a ƙungiyar Manchester City ta Ingila, inda yake zura ƙwallo babu ƙaƙƙautawa.

Bellingham

Jude Bellingham, matashin ɗanƙwallo ne da aka haifa a ranar 29 ga Yunin 2003, inda yake taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya a ƙungiyar Real Madrid ta La Liga, da kuma tawagar ƙasar Ingila.

Ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin ƙwararrun ƴan wasan ƙwallon ƙafa a duniya, musamman inda yake nuna bajinta wajen ƙwazo da ƙarfin jiki.

Shi ma ya nuna bajinta sosai a gasar cin kofin duniya.

Dembélé

Ousmane Dembélé na Paris Saint-Germain na cikin jerin ƴanwasan da suka shiga cikin jerin.

Dembélé ne ya lashe kyautar Ballon d'Or na shekarar 2025, bayan nuna bajinta a ƙungiyar PSG da Faransa.

Dembele ne ya jagoranci ƙungiyar PSG wajen lashe zakarun turai, inda ƙungiyar ta lashe gasar sau biyu a jere ta kakar 2024–25 da kakar 2025–26 kuma duk yana taka rawar gani a gasannin.

Yaushe za a bayar da kyautar?

Za a gudanar da bikin bayar da kyautar Ballon d'Or na 2026 a ranar Litinin 26 ga Oktoba, a London Palladium Theatre da ke birnin London na Ingila.

Bikin na bana na da muhimmanci na musamman saboda Ballon d'Or zai cika shekara 70 tun lokacin da aka ƙirƙiro kyautar a shekarar 1956.

An kafa kyautar ne a ƙarƙashin mujallar France Football, kuma tun daga shekarar 2024 ake gudanar da ita tare da hadin gwiwar UEFA.

Zaɓar London a matsayin wurin gudanar da bikin na kuma da alaƙa da tarihin kyautar, saboda ɗan wasan Ingila Stanley Matthews shi ne wanda ya fara lashe Ballon d'Or a shekarar 1956.

Messi na da tarihin lashe kyautar, amma a yanzu yna fuskantar ƙalubale daga Mbappé da Vinícius da Haaland da Bellingham da Yamal a matsayin matasa masu jini a jika.