Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴanwasa 5 da suka samu manyan kyautuka a Gasar Kofin Duniya
Hukumar ƙwallon ƙafa da Duniya FIFA, ta karrama wasu gwarazan ƴanwasa biyar da suka yi fice a Gasar Kofin Duniya ta 2026 da aka kammala a ranar Lahadi.
A kowace Gasar Kofin Duniya da FIFA ke shiryawa takan lura da wasu ƴanwasan da suka fi fice a fannoni daban-daban domin karrama su kan rawan da suka taka a gasar.
Sifaniya ce ta lashe kofin bayan doke Argentina - wadda ta ɗauka a 2022 - da ci 1-0 a wani wasa da ya ɗauki hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.
Karo na biyu kenan da Spain ke ɗaukar kofin bayan wanda ta ɗauka a gasar 2010 da aka gudanar a ƙasar Afirka ta Kudu.
Ƴan wasa biyar da FIFA ta karrama bayan kammala gasar Kofin Duniyar su ne:
Rodri (Sifaniya)
Ɗan wasan tsakiya na Sifaniya ya lashe kyautar Golden Ball, wadda ake bai wa gwarzon ɗan wasa a gasar baki ɗaya.
Kyaftin ɗin tawagar Sifaniyan ya kasance jigon tsakiyar fili, inda ya taimaka wa ƙasarsa wajen sarrafa wasanni da kuma kaiwa ga lashe kofin duniya ba tare da rashin nasara ba.
Ɗan wasan tsakiyar na Manchester City ya ƙware wajen sarrafawa da rarraba ƙwallo a tsakiyar fili.
Rawar da ya taka ta sa aka ɗauke shi a matsayin mafi tasiri a gasar.
Kylian Mbappé (Faransa)
Kylian Mbappé na Faransa ne ya lashe kyautar ɗanwasan da ya fi zura ƙwallo a raga, wadda ake kira 'Golden Boot' da FIFA ke bayarwa.
Ɗan wasan gaban na Real Madrid ya zura ƙwallo 10 a gasar, inda ya ƙare a gaban Messi na Agentina mai takwas.
Baya ga bajintar zura ƙwallaye a gasar 2026, Mbappé ya kafa tarihin ɗanwasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya, inda ya ci 22.
Duk da cewa Faransa ba ta kai wasan ƙarshe ba, Mbappé ya nuna bajinta wajen cin ƙwallaye a kusan kowane mataki na gasar.
Unai Simón (Sifaniya)
Unai Simón mai tsaron ragar Sifaniya ne ya lashe kyautar Safar Zinare ta gola mafi ƙwazo a gasar Kofin Duniya ta 2026.
Simón ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Spain, inda ya yi wasanni bakwai ba tare da ƙwallo ta shiga ragarsa ba.
Kuma a duka tsawon gasar sau ɗaya ne kawai ƙwallo ta shiga ragarsa.
Pau Cubarsí (Sifaniya)
Pau Cubarsí na Sifaniya ne ya lashe kyautar matashin ɗanwasan mafi ƙwazo a gasar.
Mai tsaron bayan ya nuna jajircewa wajen tsaron bayan Sifaniya a ɗaukacin gasar, inda ya buga duka wasannin ƙasar takwas a gasar.
Mai shekara 19, da ke taka leda a Barcelona ya haska sosai duk da ƙarancin shekarunsa a gasar.
Netherlands
Kyauta ta ƙarshe ita ce wadda aka bai wa Netherlands a matsayin wadda ta fi nuna kyawawan ɗabi'u a gasar.
FIFA ta ce Netherlands ta nuna kyakkyawan ɗabi'a da ladabi da mutunta dokokin wasa a tsawon gasar.
Bayanai sun ce katin gargaɗi uku kawai aka bai wa tawagar, yayin da ba ta yi wani laifin da ya cancanci katin kora ba.
Duka katin gargaɗin uku na Netherlands ta same ne a wasan farko da ta buga da Japan.
Bayan haka ba ta ƙara samun katin gargaɗi ba a duka sauran wasannin nata, har zuwa lokacin da Moroko ta fitar da ita a matakin ƴan 32.