Wa ya fi tsufa da ƙuruciya da za su buga gasar cin kofin duniya 2026

Portugal's Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Cristiano Ronaldo zai zama ɗan wasan mafi yawan shekarun haihuwa da zai taka leda a gasar Kofin Duniya 2026
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Da yake an tabbatar da dukkan sunayen ƴan wasan da za su buga wa tawagoginsu 48 gasar Kofin Duniya 2026, tuni aka duba yadda kowace ƙasa ta kammala sanar da ƴan ƙwallonta, an kuma kwatanta kowanne kafin fara gasar.

Waɗanne kasashe ne suka fi yawan ƴan wasa? Guda nawa ne daga kowace tawaga ke taka leda a manyan lig-lig a duniya? Kuma wane ne mafi yawan shekarun haihuwa da mafi ƙuruciyar daga ƴan ƙwallon da za su buga wasannin bana?

Duk da cewa Manchester City ba ta lashe Premier League ba a kakar da aka kammala, amma ƴan wasanta 19 ne za su kara a gasar cin kofin duniya ta bana da za su wakilci kasa 12.

Bayan City, sauran ƙungiyoyin da ke biye da ita masu ƴan wasa da yawa da za su buga kofin duniya sun haɗa da wadda ta lashe kofin Bundesliga da na Premier League da na Ligue 1 da kuma na La Liga a kakar da aka kare.

Arsenal tana da ƴan wasa 16 da za su wakilci tawaga 10, ita kuwa Inter Milan ta Italiya tana da ƴan ƙwallo bakwai, kuma ta samu tawaya, saboda kasar ba ta samu tikitin shiga babbar gasar tamaula ta duniya ba karo na uku a jere.

Idan muka yi duba daga ƙungiya 20 da suka buga gasar Premier League ta 2025/26, guda uku daga saman teburi ne suke da ƴan wasa da yawa da za su buga gasar kofin duniya, fiye da Crystal Palace, wadda ta lashe Conference League na bana mai mutum 12.

Sunderland ma tana da ƴan wasa da yawa idan ka haɗa har da masu buga wasannin aro tana da 11 da za su wakilci kasashensu, yawan iri ɗaya daga Chelsea da kuma Liverpool, hakan ya nuna yadda Sunderland ta yi cefane tun kan fara kakar bana da kuma rawar da ta taka a gasar ta Premier League.

Ƙungiyar Brentford da Everton da kuma Leeds United sune suke da karancin ƴan ƙwallon za su buga gasar kofin duniya da kowacce keda huɗu,

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ana kallon manyan lig-lig biyar na Turai—Ligue 1 ta Faransa, Serie A ta Italiya, Premier League ta Ingila, La Liga ta Sifaniya da Bundesliga ta Jamus—a matsayin mafi ƙyau a duniya, amma tawagar Sifaniya ce aka tattara ƴan wasanta gaba ɗaya daga cikin waɗannan manyan lig-lig.

Ivan Toney na Al-Ahli da Leroy Sané na Galatasaray sun shiga cikin jerin ƴan ƙwallon Ingila da na Jamus, yayin da Faransa ta haɗa, Theo Hernández na Al-Hilal da N'Golo Kanté na Fenerbahçe a cikin tawagarta.

Ƙasashe irin su Switzerland da Netherlands da Belgium kuma suna da adadi mai yawa na ƴan wasa da ke taka leda a manyan matakai duk da ƙanƙantar ƙasashensu. Idan muka fita daga Turai kuwa, Argentina da Senegal su ne ƙasashen da suka fi yawan ƴan ƙwallon da ke buga gasar lig-lig mafi daraja a duniya.

Sai dai babu wata daga cikin tawagogin Curacao da Iran da Iraq ko Qatar da ke da ƴan wasa da suka taka leda a manyan lig-lig biyar na Turai a wannan kakar. Duk da haka, ɗan wasan Iraq, Ali Jasim, yana cikin ƙungiyar Como ta Serie A, amma ya shafe kakar bana a buga wasannin a aro a ƙungiyar Al-Najma ta Saudi Arabia.

Panama, wadda take rukuni ɗaya da Ingila za ta buga gasar da ƴan wasa da dama masu shekarun haihuwa da yawa tare da Iran da Colombia da kowacce take da matsakaitan shekarun haihuwa 30.

Carlo Anceloti zai dogara da tsoffin ƴan ƙwallo da suka haɗa da Danilo da Casemiro da Neymar da kowanne yake da shekara 34, domin lashr kofin bana, wadda rabonta da shi tun 2002, haka itama Scotland ta je da ɗaya daga cikin ɗan wasa mafi tsufa a tawagar a gasar kofin duniya da za ta buga a karon farko tun bayan 1998.

Babban dalilin hakan shi ne mai tsaron ragar Scotland, Craig Gordon, wanda zai kai shekara 43 da kwanaki 162 a lokacin da za a fara gasar a mako mai zuwa. Wannan ya sa shi ya zama mafi tsufa, amma ba a tabbas ko zai tsare ragar kasar.

Ana sa ran wannan ce gasar kofin duniya ta karshe da Cristiano Ronalo zai halarta karo na shida mai shekara 41, ƙyaftin ɗin tawagar Portugal, kuma dama ta karshe idan zai samu ɗaga kofin da yake kishirwa a tarihin sana'arsa ta taka leda.

Haka kuma Luka Modrić da Edin Džeko su ne sauran manyan ƴan wasa da suka shiga rukunin sama da shekara 40, inda duk da tsufansu, har yanzu suke taka muhimmiyar rawa a tawagoginsu.

Tawagar Ivory Coast ce mai yawan matasa, yayin da ake sa ido kan rawar da Yan Diomande mai shekara 19 da kuma Bazoumana Toure mai shekara 20 za su taka.

Itama wadda aka bai wa kofin nahiyar Afirka, Morocco da tawagar Sifaniya mai rike da kofin nahiyar Turai, suna da matasan ƴan ƙwallo da ya haɗa da Lamine Yamal mai shekara 18 da kuma Pau Cubarsi mai shekara 19.

Ɗan ƙwallon tawagar Mexico, Gilberto Mora shi ne matashin da zai buga gasar cin kofin duniya 2026, wanda zai cika shekara 17 da kwana 240 a lokacin da za a fara wasannin.

Shi kuwa ɗan kasar Jamhuriyar Czech, Hugo Sochurek zai cika shekara 18 da haihuwa ranar Lahadi, yayin da ake sa ran matashi ɗan ƙwallon Bayern Munich zai haskaka a bana da zarar ya samu damar buga gasar kofin duniya da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico a bana.