Alvarez na shirin zuwa Arsenal, Man Utd na son Balde

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan gaba na Argentina Julian Alvarez, mai shekara 26, a shirye yake ya koma Arsenal, duk da a baya ya fi son zuwa Barcelona yayin da alaƙar sa da Atletico Madrid ta fara lalacewa. (Standard)
Kocin Arsenal Mikel Arteta da daraktan wasanni Andrea Berta sun daɗe suna tuntuɓar Alvarez, duk da har yanzu ɗanwasan na Argentina ya son zuwa Barcelona, yanzu kuma yana ganin Arsenal za ta iya zame masa mafita. (AS - in Spanish)
Tottenham na da tabbacin za ta kammala cinikin ɗanwasan gaba na Masar Omar Marmoush daga Manchester City. (Fabrizio Romano)
Ɗanwasan gaba na Ingila Ollie Watkins ya shaida wa Aston Villa cewa yana son barin ƙungiyar bayan ƙungiyar Saudiyya Al-Hilal ta nuna sha'awar sa. (GiveMeSport)
Ɗanwasan baya na Spain Alejandro Balde, mai shekara 22, ya yanke shawarar barin Barcelona, inda Manchester United ta nuna tana so. (Metro via Jijantes)
Kodayake Balde yana da zaɓin tsayawa domin gwagwarmayar wurinsa a Barca. (Mundo Deportivo - in Spanish, external)
Real Madrid ba za ta bar Liverpool ta saye ɗanwasan Brazil Endrick ba mai shekara 20, bayan ta sayar wa Fulham da ɗanwasan gaba na Spain Gonzalo Garcia, mai shekara 22. (Football Insider, external)
Chelsea ta yi watsi da tayin Roma na karɓar aron ɗanwasan Ingila mai shekara 22 Jamie Bynoe-Gittens. (Talksport, external)
Tottenham na son sayar da ɗanwasan tsakiya na Senegal Pape Matar Sarr, mai shekara 23, kuma ɗanwasan na iya komawa Galatasaray. (Sacha Tavolieri via Teamtalk, external)
Liverpool ta samu ƙwarin guiwa kan farautar ƴanwasan Paris St-Germain Bradley Barcola, mai shekara 23, da kuma Ibrahim Mbaye na Senegal mai shekara 18, bayan ajiye su daga tawagar ƙungiyar a wasan Ligue 1 da Rennes ranar Lahadi. (Standard via RMC)











