BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Kilogiram na zinare nawa aka hada Kofin Duniya da shi?
Tarihin kofin da ake amfani da shi a yanzu ya fara ne daga shekarar 1974 bayan Brazil ta mallaki kofin Jules Rimet na dindindin.
KAI TSAYE, Za mu yi wa Amurka ɓarnar da ta fi ta baya- Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 19 ga wagan Yulin 2026
Wasannin Hausawa na gargajiya da suka shuɗe da muhimmancinsu
BBC ta waiwayi baya domin tuna irin waɗannan wasannin tare da kuma ko suna da muhimmanci a yanzu.
Tottenham na son Savinho, Milan na harin Phil Foden
Tottenham fatan ɗaukar Savinho daga Manchester City, Real Madrid ta fara ja baya da aniyar ta na daukar Rodri, ya yin da AC Milan ke harin Phil Foden, da ƙarin wasu labaran.
Yadda ƙudirin dokar haramta wa'azi da talla a motocin haya ke tayar da ƙura a Najeriya
Dokar Haramta wa'azi da tallace tallace a cikin motocin haya na tayar da ƙura
Ƴan wasan da suka buga Gasar Kofin Duniya da za su iya sauya kungiya a wannan bazarar
Da yake ana daf da kare Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, hankali ya fara komawa kan gasar Turai ta bana da za a fara cikin watan Agusta da ƴan wasan da za su sauya ƙungiyoyinsu a bazarar nan.
Su wane ne waɗanda aka kama da zargin kitsa sace ɗaliban Oyo?
A makon jiya ne rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto dukkan ɗalibai da malamai su 44 da aka sace kimanin wata biyu da suka gabata daga makarantu a jihar Oyo.
Hanyoyi 4 da mace za ta iya ɗaukar ciki waɗanda suka saɓa wa al'ada
Akwai wasu hanyoyin da mace kan iya samun ciki da ba a saba gani ba, abin da wasu ke ganin ba zai yiwu ba.
Me ya bambanta ƴansandan jihohi da 'askarawan' da gwamnoni suka samar?
Tun kafin amincewa da ƙudurin kafa ƴansandan jihohi, gwamnoni da dama sun kafa rundunonin tsaro na cikin gida, kamar ƴan sa-kai, jami'an tsaron yanki da kuma askarawa, domin taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 20 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 19 Yuli 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 19 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 18 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Sakamakon wasannin Gasar Kofin Duniya 2026
Dukkanin bayanan da suka kamata ku sani kan Gasar Kofin Duniya ta 2026
Wasanni
KAI TSAYE, Gasar Kofin Duniya: Ingila ta lashe tagulla bayan doke Faransa
Gasar Kofin Duniya: Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai game da Gasar Kofin Duniya ta 2026 da sauran labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 13 zuwa 19 ga watan Yuli, 2026.
Ko Sifaniya za ta sake taka irin rawar da ta taka a gasar kofin duniya ta 2010?
Sifaniya ta kai wasan karshe a gasar kofin duniya 2026, ƙwazon da kasar ke yi a bana ana danganta kamaiceceniya da wadda ta lashe kofin duniya a 2010. Ga rahoton da Mohammed Abdu ya haɗa.
Dalilai uku da ke bai wa Argentina damar farke ƙwallaye har ta ƙara
Argentina mai rike da kofin duniya ta zo da wani salo a gasar cin kofin duniya 2026, inda ake zura mata ƙwallo a raga, amma sai ta farke ta kuma kai zagayen gaba. Shin menene dalilin hakan? Mohammed Abdu ya tsara mana rahoto kan wannan.
Ko Mbappe zai lashe takalmin zinare a wasan Faransa da Ingila?
Faranda da Ingila za su kara a wasan mataki na uku a Gasar Cin Kofin Duniya ranar Asabar a birnin Miamin Amurka.
Milan na zawarcin Spence da Romero, Liverpool na son Sano
Inter Milan na tattaunawa kan sayen Djed Spence da Cristian Romero, yayin da Liverpool ke kan gaba wajen neman Kaishu Sano, ita kuwa Arsenal na son Ezri Konsa ne.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Yadda mutumin da bai yi suna ba a siyasa zai zama Firaiministan Birtaniya
Saboda jam'iyyar Labour mai mulki ta yanke shawarar ba za ta gudanar da zaɓen shugabanci ba, sai dai za ta naɗa shi kai tsaye, ba a samu tattaunawa sosai kan manufofinsa ko salon mulkinsa ba.
Mary Habila: Abin da muka sani kan mutuwar budurwa a gidan minista Umahi
Minista David Umahi ya ce kafin Mary Habila ta rasu, ta sanar da saurayinta cewa hancinta na zubar da jini.
Yadda matasan Najeriya ke rububin zama ƴansanda - Mutum nawa ake ɗauka?
A ɗaukar da hukumar ta yi na baya-bayan nan wato na 2025/26, masu neman shiga aikin sun kai 616,873 daga faɗin Najeriya.
Wace ce Aisha Achimugu da kotu ta ƙwacewa kadarori na biliyoyin kuɗi?
Hukumar EFCC ta ce bincikenta ya gano cewa biliyoyin nairori da kuma miliyoyin daloli sun riƙa shiga da fita cikin asusun bankuna da kamfanonin da ke da alaƙa da 'yar kasuwar.
Me ya sa rashin nasarar Ingila a hannun Argentina ta zama mafi raɗaɗi?
Shekarun baƙin cikin Ingila yanzu za su wuce 60, na rashin lashe kofin duniya, amma rashin nasara a hannun Argentina a wasan daf da karshe, zai kasance mafi muni da raɗaɗi a Gasar Kofin Duniya da ta buga.
Aƙalla Falasɗinawa 9 sun mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai Gaza
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 18ga watan Yulin 2026
Amfani shida da Sallah ke da su ga lafiyar mai yin ta
Baya ga lada da kusanci ga Ubangiji, masana lafiya sun alaƙanta ta da inganta lafiya da tsaftar jiki.
Badaƙalar kuɗi 5 da suka shafi kamfanin man fetur na Najeriya
Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya sha fuskantar zarge-zargen badaƙalar kuɗi a tsawon shekaru, daga zargin ɓacewar kuɗin sayar da man fetur zuwa zargin badaƙalar tallafin man fetur.
Manyan kadarorin Emefiele da kotu ta ƙwace
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 17/07/2026
Jami'an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da ceto ɗaliban da shugaban makarantar da wani jami'in NECO a sanarwa da ya fitar.
Ko ratse wa Mashigar Hormuz za ta magance tsadar fetur a duniya?
Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigila ta ruwa a duniya, wadda ta ƙara jan hankalin duniya musamman bayan ɓarkewar yaƙi a tsakanin Iran da Amurka.
Iran ta zargi Amurka da aikata laifukan yaƙi
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Alhamis 16/07/2026
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.































































