Jirgin Turkey ya fara tashi daga Kano

An wallafa
Kamfanin jirgin saman Turkiyya (Turkish Airlines) ya fara jigilar fasinja daga Kano, Nigeria zuwa birnin Santambul na Turkiyya.
Jirgin, samfurin Boeing 787-800 DELTA mai daukar fasinja 151 ya fara tashi ne a daren Juma'a kuma zai ci gaba da daukar fasinja sau hudu a kowanne mako.
A baya dai gwamnatin jihar Kano ta sha zargin ma'aikatar sufurin jiragen saman Nigeria da yunkurin hana jirage sauka a birnin domin dakile tattalin arzikin yankin.
Sai dai ministar ta musanta hakan.







