Bayern Munich ta lashe Champions League

Wannan shafi na kawo muku yadda ake fafatawa kai-tsaye tsakanin Bayern Munich da PSG a wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Champions League na 2019-2020.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Muna taya 'yan Bayern murna, PSG 0-1 Bayern Munich

    Lewandowski

    Asalin hoton, Getty Images

    Muna taya 'yan Bayern Munoich murnar lashe wannan kofi tare da fatan za mu haɗu a sabuwar kaka mai zuwa ba tare da korona ba.

    Masu bibiyarmu nan muka kawo ƙarshen sharhi a shafin namu.

    Umar Mikail ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Bayern Munich: Zakarun Turai

    Bayern Munich

    Asalin hoton, Getty Images

    • Real Madrid (13) da AC Milan (7) ne kaɗai suka fi Bayern yawan lashe Champions League
    • Ita ce ƙungiya ta farko da ta lashe dukkanin wasanninta na Champions League
    • Bayern ta kammala kakar wasa ta 2019-20 ba atre da an doke ta ba a cikin wasa 30 na ƙarshe a jere - ta ci 29 ta yi canjaras 1
    • Kingsley Coman, shi ne ɗan ƙasar Faransa na biyar da ya ci ƙwallo a wasan ƙarshe na Champions League bayan Benzema da Zidane da Dsally da Boli
    • Ita ce ƙungiya ta uku da ta ci ƙwallo 500 a Champions League bayan Real Madrid (567) da Barcelona (517).
  3. Da ƙyar Neymar ya karɓi kyautarsa

    Neymar

    Asalin hoton, Getty Images

    Neymar ba ya son karɓar kyautar sarƙarsa ta waɗanda suka zo ma biyu amma an lallaɓa shi ya karɓa.

    Ko zai sake zuwa irin wannan matakin?

  4. Robert Lewandowski

    Karon farko kenan da ya lashe Chamapions League! Abin da mamaki kuma da daɗi!

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  5. Kaftin Manuel Neuer

    Kaftin Manuel Neuer

    Asalin hoton, @FCBayernEN

    Manuel Neuer ya zama gola na farko da ya ɗaga kofin Champions League bayan Iker Casilas da ya ɗaga a 2014.

  6. Bayern Munich sun zama zakarun Turai

    Karo na shida kenan Bayern na ɗaga kofin Champions League:

    2020

    2013

    2001

    1976

    1975

    1974

    Bayern

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Shikenan! Wasa ya ƙare! Bayern ta ɗauki kofi

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Kingsley Coman

    Kingsley Coman, shi ne ɗan ƙasar Faransa na biyar da ya ci ƙwallo a wasan ƙarshe na Champions League bayan Benzema da Zidane da Dsally da Boli

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  9. Neymaaaaaar

    Saura ƙiris Neymar ya farke amma Alaba ya wulla ta waje da kyar

  10. , PSG 0-1 Bayern Munich

    'Yan wasan Bayern duka sun miƙe tsaye suna jiran usur ɗin ƙarshe.

    Minti huɗu ne suka ragfe, yanayin ba zai faɗu da baki ba duk da cewa mutanen da ke cikin filin wasan ba su fi 50 ba.

  11. Bayern ta yi canji

    Thiago Alcantara ya fita daga fili Toliso ya shigo.

  12. Coman ya ci iyayen gidansa

    A taƙaice dai Coman gida ya ci - an haife shi a birnin Paris sannan kuma da PSG ya fara wasansa na ƙwallo a 2004.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  13. Thiago Silva ya samu katin gargaɗi

    Ya samu katin ne bayan ya yi wa Lewandowski ƙeta.

    Coutinho ya buga bugun tazara daga ksuan yadi na 26 amma ta yi waje.

  14. Bayern ta ci ƙwallo ta 500 a Champions League

    Bayern

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙwallon da Kingsley Coman ya ci ta zama ta 500 da Bayern ta zira a gaar Champions League.

    Hakan ya sa ta zama ƙungiya ta uku da ta ci 500 bayan Real Madrid (567) da Barcelona (517).

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. Neymar ya ɗaɗa ƙwallo

    Bayan an shiga an fita, an sake shiga an fita, Neymar ya ɗaɗa ta amma ta yi faɗi.

    Wasan ya ƙara zafi matuƙa musamman daga ɓangaren PSG da ke neman kafa tarihin lashe gasar a karon farko.

  16. Marquinhosss

    Ƙwallo ce mai haɗari Marquinhos ya buga wa Neuer bayan Di Maria ya bugo masa daga gefen hagu.

    Sai dai golan bai yi ƙasa a gwiwa ba, ya tura ta waje.

  17. Bayern ta yi canji biyu

    Coutinho ya karɓi Gnabry, Perisic ya karɓi Coman wanda ya ci ƙwallon.

  18. Saura ƙiris

    Di Maria ya bugo wa Mbappe ƙwallo amma Neuer ya gan ta kuma ya kama saboda Mbappe bai iya taɓa ta ba.

  19. PSG ta yi canji

    Marco Vratti ya karɓi Daniel Paredes

  20. Goallllllll, PSG 0-1 Bayern Munich

    Coman

    Asalin hoton, UEFA

    Kingsly Coman ya ci wa Bayern Munich - hakan na nufin saura ƙasa da minti 40 Bayern ta ɗaga Champion League na shida.

    Kimmich ne ya bai wa Coman ƙwallon.