NBC za ta kafa kwamiti don sauraron laifukan kafofin yaɗa labarai
Hukumar Kula da Ayyukan Watsa Labarai ta Najeriya NBC ta bayyana cewa za ta kafa wani kwamitin sauraron ƙararraki mai zaman kansa domin duba laifukan da ake zargin gidajen watsa labarai sun aikata.
Darakta Janar na hukumar, Dakta Charles Ebuebu, ne ya bayyana hakan ga manema labarai inda ya ce kwamitin zai ƙunshi alkalai masu ritaya da sauran jami'ai masu zaman kansu domin tabbatar da adalci da gaskiya wajen yanke hukunci.
Ebuebu ya ce hukuncin kotu bai hana NBC ɗaukar matakan ladabtarwa kan gidajen watsa labarai da suka karya ƙa'idoji ba, sai dai ya nuna cewa ba za ta iya sanya tarar kuɗi ita kaɗai ba tare da wani tsari na shari'a mai zaman kansa ba.
Ya ce hukumar ba ta amince da wannan ba, tana mai jaddada cewa akwai bambanci tsakanin tarar gudanarwa da tarar laifukan da kotu ke yankewa, saboda haka ta ɗaukaka ƙarar hukuncin zuwa kotun daukaka ƙara.
Shugaban NBC ya ƙara da cewa sabon tsarin zai yi kama da kotunan tafi-da-gidanka da Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Kasa (FRSC) ke amfani da su, inda ake gabatar da masu karya doka gaban wata hukuma mai zaman kanta kafin a yanke hukunci.




























