KAI TSAYE, Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 28 ga watan Mayun 2026

  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. NLC ta caccaki gwamnati kan taɓarɓarewar tsaro da tattalin arziki

    ..

    Asalin hoton, Nigeria Labour Congress HQ/FB

    Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya ta soki yadda ake samun taɓarɓarewar matsalar tsaro da tattalin arziki a ƙasar.

    A saƙon barka da sallah da Shugaban NLC, Joe Ajaero, ƙungiyar ta ce ma'aikatan Najeriya da talakawa na cikin ƙunci ƙarƙashin manufofin

    A cewar shi, miliyoyin mutane na jurewa yanayin tsadar rayuwa da ke ƙara jefa mutane cikin talauci inda kuma ya yi kira ga ƴansiyasa da su yi nazari kan tasirin matakansu na tattalin arziki.

    Mambobin NLC sun yi kira da a ɗauki matakai domin magance matsalar tsaro da ke ta'azzara a ƙasar.

    Ajaero ya kuma ce ya kamata gwamnatoci su mayar da hankali wajen kare rayukan al'umma da kuma samar musu da abubuwan buƙata kamar abinci da kiwon lafiya da ilimi da kuma ayyukan yi.

  2. EU ta ci tarar Temu dala miliyan 232

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Ƙungiyar Tarayyar Turai sun ci tarar kamfanin kasuwancin intanet na Temu dala miliyan 232.

    Jami'ai sun ce kamfanin ya gaza yin abin da ya kamata wajen hana sayar da haramtattun kayayyaki da kaya masu illa ga kwastamominsa da ke EU ciki har da cajar waya da kuma kayan wasan yara.

    Matakin na zuwa ne bayan wani bincike na shekara biyu da aka yi kan ƙorafe-ƙorafen da hukumomin kare haƙƙin masu sayen kaya daga ƙasashen Turai 17 suka yi game da ayyukan kamfanin na Temu.

    Kamfanin na Temu yana da nan da watan Agusta ya yi gamsasshen bayani ko kuma ya fuskanci hukunci.

  3. Me sabon rahoton Amurka ya ce kan Fulani a Najeriya?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoton Amurka ya yi iƙirarin cewa Fulani masu gwagwarmaya da makamai na ci gaba da gagarumar mamaya a gonakin Kiristoci da kai miyagun hare-hare a kan wuraren addinan Kiristanci da na Musulmai.

    Ya ce a 'yan shekarun nan, masu gwagwarmaya da makamai daga tsatson Fulani sun tafka miyagun hare-hare a kan al'ummomi da ba lallai kawai Kiristoci ba a Najeriya.

    Ya ce da yawan ƙungiyoyin Fulani 'yan ta-da-ƙayar-baya na ƙaddamar da hare-hare, amma akwai wasu waɗanda lokaci-lokaci suna haɗa gwiwa da gungun 'yan fashin daji, da kuma sanannun ƙungiyoyin 'yan ta'adda don yaɗa wata fassarar addinin Musulunci ta tarzoma.

    Najeriya, musamman yankin arewacinta na fama da rikice-rikice masu nasaba da ƙabilanci ko addini.

    A baya-bayan nan shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin cewa ana "gallaza wa Kiristoci" a Najeriya, zargin da hukumomin ƙasar suka musa.

    Ga ƙarin bayani a nan.

  4. Ƙananan yara da mata sun mutu a harin Isra'ila kan Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar agaji ta Palestine Red Crescent da kuma wasu majiyoyi daga wani asibiti sun ce wani hari da Isra'ila ta kai kan wani gida da ke Gaza ya yi sanadin rasa rayukan mutum bakwai ciki har da ƙananan yara mata biyu tare da jikkata wasu 15.

    Rahotannisun ce wani jirgin yaƙin Isra'ila ne ya harba makamai masu linzami a kan gidan da ke tsakiyar birnin.

    Rundunar sojin Isra'ila dai ta ce ta kai wa wasu manya biyu a ƙungiyar Hamas hari a arewacin Gaza, to amma bata bayyana sunayensu ba.

    A jiya Laraba Isra'ilan ta hallaka sabon kwamandan Hamas a Gaza wato Mohammed Odeh.

    Wannna rikicin dai na zuwa ne duk da yarjejeniya tsagaita wuta da aka amince da ita a watan Oktoban da ya gabata.

  5. ADC za ta ceto dimokraɗiyya daga barazana - Atiku

    ..

    Asalin hoton, Atiku Abubakar/FB

    Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce tsarin da aka bi wajen ba shi takarar yin zaɓe a jam'iyyarsa ta ADC ya nuna cewa dimokraɗiyya ba ta mutu ba.

    Da yake magana bayan samun tikitin tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin ADC a Abuja, Atiku ya ce yayin da jam'iyya mai "mulkin zalunci da adawa da dimokraɗiyya" ke yi wa dimokraɗiyyar riƙon sakainar kashi, dimokraɗiyya na nan da ranta a ADC.

    "Ina son miƙa godiyata bisa wanan dama da kuka ba ni, ta yi wa jam'iyyarmu ta ADC takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa. Na ji daɗi ƙwarai da gaske da wannan karramawa." in ji Atiku.

    Atiku ya ƙara da cewa ADC a shirye take ta kuɓutar da dimokraɗiyyar Najeriya da ke fuskantar barazana mafi muni tun komawa tsarin mulkin dimokraɗiyya a 1999.

    Ya ce mambobin jam'iyyar na da damar bayyana ra'ayinsu su kuma nemi takara a tsari na gaskiya da adalci.

    Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fitar da gwanin na shugaban ƙasa a ADC da ƙuri'a 1,846,370 inda ya doke abokan takararsa da suka fafata a zaɓen - Rotimi Amaechi da kuma Muhammed Hayatu-Deen.

  6. Sanata Omo-Agege ya fice daga APC

    ...

    Asalin hoton, Senator Ovie Omo-Agege/FB

    Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ovie Omo-Agege ya fice daga Jam'iyyar APC mai mulki.

    Cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara ka harkar labarai, Sunday Areh ya fitar, Sanata Omo-Agege ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓa da ya yi da makusantansa a siyasa da kuma magoya bayansa, bugu da ƙari kuma abubuwan baya-baya da suka faru a jam'iyyar reshen jihar Delta.

    Tsohon ɗanmajalisar ya ce ya fi dacewa ya nemi cika burinsa na siyasa da muradan da yake da shi ga al'ummar mazaɓarsa a wata jam'iyyar inda ya ƙara da cewa ba zai ci gaba da kasancewa a jam'iyyar da ba zai iya samar da ci gaba ga mutanensa ba.

    Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Omo-Agege yana gode wa APC bisa damar da ta ba shi na riƙe muƙamin mataimakin shugaban majalisar dattawa a majalisa ta tara inda kuma ya ce yana yi wa jam'iyyar fatan alheri.

  7. Isra'ila na ƙara zafafa hare-hare a Lebanon

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Ƙarin wasu hare haren da Isra'ila ta kai sun faɗa ciki da kuma kewayen birnin Tyre da ke kudancin Lebanon inda suka faɗa kan wani gini da ya kama da wuta daga bisani.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana harin gine-ginen 'yan Hezbollah ne bayan ta umarci mazauna wurin da su tashi daga wajen.

    Wakilin BBC ya ce hare-haren sun zo ƙasa da sa'oi biyu da Isra'ila ta bai wa mazauna wajen umarnin su tattara nasu ya nasu su bar wuraren inda aka bar su da yanke hukunci mai sarƙaƙiyar gaske.

    Rundunar ta ce wani hari da jirgi marar matuƙi da Hezbollah ta kai ya kashe wani soja a arewacin Isra'ila.

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross, ta ce kashe 'yan Lebanon da kuma lalata wurare da ake na nufin rayuwa ta yi tsanani ga fararen hula.

  8. Gobara ta yi ajalin ɗalibai 16 a Kenya

    ..

    Asalin hoton, Robert Maina

    Ɗalibai 16 sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a makarantar kwana da ke Gilgil a Kenya, kamar yadda wani ɗansanda ya shaida wa manema labarai.

    Wasu ɗalibai 74 kuma suna samun kulawa a asibiti bayan raunin da suka ji.

    Gobarar da ta faru a makarantar ƴanmata ta Utumishi ta soma ne da sanyin safiyar yau Alhamis lokacin da ɗaliban suke barci, in ji ƙungiyar agaji ta Red Cross a Kenya da kuma ƴansanda.

    Ƴansanda sun ce ana aikin ceto sai dai zuwa yanzu hukumomi ba su gano musabbabin gobarar ba.

    Ƙungiyar Red Cross a Kenya ta ce masu bayar da agajin gaggawa na wajen domin ba da tasu gudunmawar.

    A yayin da yake magana da iyayen ɗalibai da sauran mutanen da suka taru a wajen makarantar, babban jami'in ƴansanda Masoud Mwinyi ya ce lamarin abin tashin hankali ne.

    Dama a kan samu tashin gobara a makarantun kwana a Kenya inda a shekarun baya-bayan nan lamari ya janyo mutuwar mutane.

  9. Amurka da Iran sun yi wa juna luguden wuta

    ...

    Asalin hoton, US Navy via Getty Images

    Amurka da Iran sun kai wa juna hare-hare a Gabas ta Tsakiya, abin ya nemi ya jirkita ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi domin kawo ƙarshen yaƙin da ƙasashen biyu ke yi.

    Sojojin Amurka sun ce sun ƙaddamar da abin da suka kira kare kai daga hare-haren da aka kai wa jami'ansu da jirage maras matuƙa inda suka harbo hudu daga cikinsu.

    A matsayin martani, dakarun juyin juya halin Iran sun ce sun kai hari kan wani sansanin sojin Amurka da ke yankin.

    Ba su bayyana ko ina ne ba, to amma an jiyo ƙarar jiniyar ankarar da mutane za a kawo hari ta sama a Kuwait.

    Kafar yaɗa labaran Iran ta ce tun da farko wasu jiragen ruwa sun yi ƙoƙarin wucewa ta Mashigar Hormuz ba tare da neman izini ba daga Tehran abin da ya janyo dakarunsu harba makaman gargaɗi.

  10. Barka da Zuwa

    Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa na marhaba da ɗumbin masu bibiyar mu a wannan ranar Alhamis.

    Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma wainar da ake toyawa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.

    Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo har ma ku tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.