Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 21/02/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Asabar 21/02/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Ana ci gaba da ƙirga ƙuri'u bayan kammala zaɓen Abuja

    Masu zaɓe

    An fara ƙirga ƙuri'i bayan kammala kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukukomin Abuja.

    Wakilan BBC da suka zagaya wasu rumfunan sun bayar da rahoton cewa ba a samu fitowa masu zaɓe sosai a wasu rumfunan ba.

    Hukumomin birnin dai sun saka dokar taƙaita zirga-zirga a faɗin birnin.

    Masu zaɓe
  2. Makeken jirgin ruwan Amurka na ci gaba da shawagi a Gabas ta Tsakiya

    Jirgin ruwa

    Asalin hoton, David Parody

    Sashen tantance labarai na BBC Verify da ke ci gaba da sanya idanu kan makeken jirgin dakon kayan aikin soji na Amurka mai suna USSG ya wuce ta gaɓar ruwan Gibraltar.

    Rahotonni sun nuna cewa an asamu ƙaruwar girke kayan aikin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, tun bayan ƙarin matsin lamba da gwamnatin Trump ke yi wa Tehran.

    Sashen Persia na BBC ya ce a cikin kwana biyu an samu ƙarin aika kayan aiki da jirage kusan sau 50 zuwa yankin

    A baya-bayan nan ne Trump ya bai wa Iran wa'adin kwana 10 da ta amince da yarjejeniyar nukiliya ko ya ɗauki matakin soji a kanta.

  3. An samu ƙarancin fitowar masu zaɓen cike gurbi a Kano

    masu zaɓe

    Rahotannin da ke fitowa daga jihar Kano sun nuna cewa an samu ƙarancin fitowar mutane zaɓukan cike gurbin wasu ƴan majalisar dokokin jihar biyu.

    An gudanar da zaɓukan a rumfunan zaɓe 1,014 a faɗin ƙananan hukumomin Ungogo da Municipal.

    Bayanai sun nuna cewa duk da isar jami'an zaɓe rumfunan a kan lokaci, da dama mutane sun ƙi fita zaɓukan.

    Hukumar zaɓen ƙasar dai ba ta saka sunan jam'iyyar NNPP da ADC da PDP a kan takardar kaɗa ƙuri'a ba.

    Kawo yanzu dai babu rahoton wani tashin hankali a zaɓukan.

    Jami'an tsaro sun ƙarfafa tsaro a wuraren da ake gudanar da zaɓukan.

  4. Zaɓen Abuja ba zai zama zakaran gwajin dafin zaɓen 2027 ba - Masana

    zaɓe

    Yayin da wasu ke ganin zɓen ƙananan hukukomin Abuja zai zama zakaran gwajin dafi ga zaɓukan 2027 masu zuwa, saboda fara aiki da sabuwar dokar zaɓe ta 2025, masana na ganin ba haka ba ne.

    A cikin makon nan ne dai shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zaɓen ƙasar da aka yi wa gyaran fuska.

    Hakan ce ta sa wasu da dama ke ganin zaɓen zai haska hanya ko makomar zaɓuka shekarar mai zuwa.

    To sai dai masana harkokin siyasa na ganin ba haka lamarin yake ba.

    Farfesa Abubakar Umar Kari, masanin harkokin siyasa, kuma malami a Jami'ar Abuja na daga cikin masu wannan ra'ayi.

    A hirarsa da BBC Malamin jami'ar ya ce har yanzu jam'iyyun hamayya na ƙoƙarin daidaita ne.

    ''Idan ka kula har yanzu jam'iyyun adawar ƙasar suna neman bakin zaren ne, ba su gama kafuwa ba, musamman jam'iyyar ADC'', in ji shi

    Ya ƙara da cewa sakamakon zaɓen ba zai zama manuniya ga makomar zaɓukan 2027 ba, kodayake ya ce zaɓen zai iya zama gwaji ga hukumar zaɓen ƙasar.

    ''Saboda hakan zai nuna cewa ko ta shirya wa zaɓukan ko akasin haka, musamman gwajin sabbin na'urorin zaɓen da hukumar ta ce za a yi gwajinsu'', in ji masanin siyasar.

  5. Birtaniya na shirin cire Andrew daga jerin madagan Sarautar ƙasar

    Andrew

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Birtaniya na duba yiwuwar ɓullo da wata doka da za ta cire Andrew Mountbatten-Windsor daga jerin masu jiran gadon sarautar ƙasar.

    Ministan tsaron ƙasar Luke Pollard ya shaida wa BBC cewa matakin - wanda zai hana Andrew zama sarkin Birtnaiya har abada - shi ne abin abin da ya ''dace a wannan lokaci,'' ba tare da la'akari da sakamakon binciken ƴansanda ba.

    A yanzu haka Andrew, wanda ƙanin Sarki Charles III ne, shi ne na takwas cikin jerin mutanen da ke jiran gadon sarautar ƙasar, duk da cire masa muƙamin ''yarima'' da aka masa a watan Oktoban da ya gabata.

    Tsohon yariman dai na fuskantar matsin lamba kan alaƙarsa da Jeffrey Epstein, fitaccen kawalin nan na Amurka.

    A ranar Alhamis da maraice ne aka saki Andrew bayan kwashe sa'o'i 11 yana fuskantar tuhumar aikata da ba daidai da ofishin gwamnati.

    Andrew dai ya sha musanta aikata laifi.

  6. INEC ta gargaɗi masu sayen ƙuri'a a zaben Abuja

    Amupitan

    Asalin hoton, INEC

    Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta gargaɗi masu sayen ƙuri'a a zaɓukan Abuja.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X, ta wallafa lambobin wayar da za a sanar da ita a duk wurin da aka ga hakan na faruwa.

    Ana gudanar zaɓukan shugabannin ƙananna hukukomin birnin shida da kansiloli 62.

    INEC ta ce akwai rumfunan zaɓe 2,822 a birnin Abuja.

    A cewar hukumar zaɓen fiye da mutum miliyan 1.6 ne suka yi rajistar zaɓe a birnin.

  7. Ana ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen Abuja

    mai zaɓe

    Masu zaɓe sun ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓukan ƙananan hukumomin birnin Abuja.

    mai zabe

    Wakilin BBC da ya zagaya wasu rumfunan zaɓen ya ce an samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'ar.

    mai zaɓe
    mai zaɓe

    Zaɓen dai shi ne na farko da INEc ke jagoranta tun bayan yi wa dokokin zaɓen gyaran fuska.

    zaɓe

    An dai samar da jami'an tsaro a rumfunan zaɓen domin bayar da tsaro a lokacin zaɓen.

    zaɓe
  8. INEC ta cire NNPP da ADC a zaɓukan cike gurbin Kano

    Kwankwaso

    Asalin hoton, Kwankwaso

    Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ba ta shigar da jami'iyyun NNPP da ADC da kuma PDP ba cikin zaɓukan cike gurbi na Kano.

    NNPP - wadda a baya-bayan nan gwamnanta na Kano ya koma APC - ta zargi INEC ta hana ƴantararta shiga zaɓukan saboda zargin ''rashin cancanta''.

    Sai dai cikin wani jawabi da ya yi wa manema labarai a jihar, kwamishinan zaɓen Kano, Abdul Zango ya ce hukumar ta bai wa kowace jam'iyya dama.

    To amma cikin sunayen ƴan takara na ƙarshe da hukumar ta fitar sun nuna babu sunayen ƴantakarar jam'iyyun NNPP da PDP da kuma ADC.

    Ana gudanar da zaɓukan cike gurbin ƴanmajalisu biyu a Munincipal da Ungogo bayan rasuwar ƴan majalisun.

    A cikin watan Janairun da ya gabata ne gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya fice daga jam'iyyar NNPP da aka zaɓe shi cikinta a 2023 zuwa APC.

  9. Gwamnatin Tinubu ba ta da tsarin kawar da matsalar tsaro - Amnesty

    AMNESTY INTERNATIONAL

    Asalin hoton, AMNESTY INTERNATIONAL

    Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta ce aƙalla mutum 323 aka kashe a ƙasar tun bayan kamawar watan Fabrairun da muke ciki.

    Cikin wani saƙo da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X, ta ce an kashe mutanen ne a ƙauyuka daban-daban na jihohin Benue da Katsina da Kwara da Kebbi da Neja da kuma Zamfara.

    Ƙungiyar ta ɗora wa shugaban ƙasar Bola Tinubu da gwamnatinsa laifin kasa magance matsalar kashe-kashen da ƴanbindiga suka kwashe shekaru ana yi a ƙasar

    ''Kashe-kashen babu gaira da rashin kataɓus daga hukumomi na magance matsalar tare da kama masu laifin don gurfanar da su a gaban shari'a na ci gaba da zama barazana ga ƴancin rayuwa a Najeriya'', kamar yadda ƙungiyar ta bayyana.

  10. Muhimman bayanai game da zaɓen Abuja

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Dokar zaɓen da aka yi wa gyaran fuska za ta fara aiki a yau Asabar a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Abuja.

    Za dai a gudanar da zaɓukan a ƙananan hukumomin birnin shida da mazaɓu 62.

    A tsakiyar makon nan ne shugaban kasar Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabbbin gyare-gyaren da aka yi wa dokar zaɓen.

    Ga bayani masu muhimman ci game da zaɓen a wannan bidiyo da Abba Auwalu ya haɗa mana.

  11. Tinubu ya buƙaci a bi doka da tsari a zaɓukan Abuja

    Tinubu

    Asalin hoton, Fadar shugaban Najeriya

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya buƙaci mazauna birnin Abuja su fito domin kaɗa ƙuri'un cikin tsari da bin dokokin hukumar zaɓe.

    Cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar a ranar Juma'a, shugaban ƙasar ya buƙaci masu kaɗa ƙuri'a su kauce wa tayar da fitina.

    ''Shi tsarin dimokraɗiyya ana jin daɗinsa ne kawai ta hanyar kwanciyar hankali, nutsuwa da kuma mutunta juna'', in ji sanarwar.

    Haka ma shugaban ƙasar ya buƙaci hukumar INEC ta bi tsari ta hanyar tabbatar da tantance masu zaɓe a kan lokaci.

    Sannan ya yi kira ga hukumar ta tabbatar ta yi aiki da sabbin dokokin zaɓe na 2026 da aka yi wa gyaran fuska.

  12. An fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen Abuja

    Masu zaɓe

    Masu zaɓe sun fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja, babban birnin Najeriya.

    Kayan zabe

    Kimanin mutum miliyan 1.5 ne suka karɓi katunan zaɓe a birnin, a cewar hukumar zaɓen ƙasar.

    kayan zaɓe

    Sai dai wakilin BBC da ya zagaya wasu rumfunan ya ce ba a samu fitowar masu zaɓe yadda ya kamata ba.

    masu zaɓe

    Shugaban ƙasar Bola Tinubu dai ya yi kira ga mazauna birnin su fito domin kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen.

    masu zaɓe
  13. Masu zaɓe na duba sunayensu a wasu rumfuna

    wasu mutane

    Masu zaɓe na ci gaba da duba sunayensu a wasu rumfunan zaɓen birnin Abuja.

    mata

    Bayanai sun nuna cewa an samu jinkirin isar jami'an zaɓe wasu rumfunan birnin Abuja.

    ma'aikatan zaɓe

    Hukumar zaɓen ƙasar ta ce mutum fiye da milyan 1.5 ne suka karɓi katunan zaɓensu a Abuja.

    Masu zaɓe

    An gudanar da zaɓen ne a ƙananna hukumomi shida na birnin.

    masu zaɓe
  14. Ana zaɓen cike gurbi a jihohin Kano da Rivers

    Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/Facebook

    Baya ga Abuja babban birnin Najeriya da ake gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi, hukumar zaɓen na jagorantar zaɓukan cike gurbi a jihohin Kano da Rivers.

    A jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar ana gudanar da zaɓukan ƴanmajalisun dokokin jihar na ƙananan hukumomin Munincipal da Ungogo.

    Haka ma a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin ƙasar, ana gudanar da zaɓukan cike gurbi na ƴanmajalisun dokokin jihar a gundumomin Ahoada East II da Khana II.

    Tuni dai Shugaba Tinubu ya yi kira ga jami'an tsaro su tabbatar da doka a zaman lafiya a lokacin zaɓukan.

  15. Hotunan yadda birnin Abuja ya zama fayau saboda zaɓe

    Titin Abuja

    Birnin Abuja ya zama fayau babu kowa sakamakon dokar taƙaita zirga-zirga da hukumomin birnin suka sanya saboda zaɓen ƙananan hukumomin birnin.

    Titin Abuja

    Tun da farko ofishin ministan babban birnin Najeriya ya fitar da wata sanarwa a ranar Alhamis, wadda a ciki ya umarci mutane su zauna a gida, in ba waɗanda aikinsu ya zama dole ba.

    Abuja

    Yau ne dai ake gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin birnin shida da kansilolinsu.

    Abuja

    Kasuwanni da sauran harkokin yau da kullum sun kasance a rufe.

    Abuja
  16. Trump ya ce zai ci gaba amfani da wani haraji da ya laftawa ƙasashe

    Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaba Trump ya bayyana wani sabon shiri na ci gaba amfani da wani haraji da ya laftawa ƙasashen duniya bayan da Kotun Koli ta soke yawancin waɗanda ya sanya a baya, da ta kira haramtattu.

    Mista Trump ya soki hukuncin da kakkausar murya, inda ya ce a yanzu zai sake gabatar da harajin kashi goma cikin 100 kan ƙasashen duniya ƙarƙashin wata dokar ta daban.

    'Yan Democrat sun yi maraba da shiga tsakani na Kotun Kolin ta yi.

  17. Sallama

    Masu bin shafin BBC Hausa-kai tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar

    Abdullahi Bello Diginza ke fstaan kun wayi gari lafiya.

    Ku ci gaba da biyo domin samun labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a fadin duniya.