Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku bubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 01 ga watan Yulin 2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. An zargi gwamnatin Habasha da sake tura sojoji zuwa gabashin Tigray

    Ƙungiyar TPLF ta zargi gwamnatin Habasha da sake tura sojoji daga yammacin Tigray zuwa gabashin yankin, matakin da ta ce zai iya ƙara tsananta rikici a yankin.

    A wani taron manema labarai da aka yi ranar 30 ga Yuni, shugabar ofishin TPLF, Fetlework Gebrezighiabher, ta ce duk da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Pretoria, gwamnatin na ci gaba da takurawa al’ummar Tigray, har ma ta zarge ta da kashe fararen hula.

    Tun da farko, TPLF ta ce gwamnati na kokarin mamaye yankin Tigray da sojoji tare da shirye-shiryen sake fara yaƙi, yayin da gwamnatin Habasha ta maida martani da cewa TPLF ce ke shirin tayar da rikici.

    A ɓangaren ƙasa da kasa, Tarayyar Turai da Amurka sun nuna damuwa kan ƙarin fargabar rikici, suna kira da a aiwatar da yarjejeniyar Pretoria gaba daya, sai dai TPLF ta yi watsi da wannan kira.

  2. Ɗalibai 35 da aka sace lokacin rubuta jarabawa na hannun ƴanbidiga - Ƴansanda

    Ƴansandan Najeriya sun tabbatar da cewa aƙalla ɗalibai 36 tare da wani ma’aikacin makaranta guda ɗaya ne har yanzu ke hannun ƴan bindiga bayan da suka sace su a harin da suka kai ranar Litinin.

    Ƴanbindigar sun kai musu harin ne a yayin da suke rubuta jarabawar kammala makarantar sakandare ta NECO a wata da ke jihar Borno.

    Ƴansandan sun ce sun riga sun tantance adadin mutanen da aka sace, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin ceto su.

    Tuni dai aka kuɓutar da mutane 10, ciki har da mataimakin shugaban makarantar.

    An kai harin ne a garin Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira Uba, inda ɗaliban ke tsaka da rubuta jarabawa.

    Harin na zuwa ne bayan wasu makamantan hare-haren a yankin, inda ake ci gaba da bincike a dazukan da ke maƙwaftaka domin gano inda waɗanda aka sace suke da kuma ceto su.

  3. Najeriya za ta nemi diyya daga Afrika ta Kudu

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta nemi a biya diyya kan dukiya da wuraren kasuwancin ‘yan ƙasarta da suka bari a Afirka ta Kudu yayin da ake mayar da su gida sakamakon hare-haren nuna ƙyamar baƙi.

    Muƙaddashin babban jakadan Najeriya a Afirka ta Kudu, Alexander Ajayi ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da ya yi da kafar watsa labarai ta Channels da ke Najeriya, inda ya ce gwamnati ta fara tattara bayanai kan dukiyar da ƴan ƙasar suka bari, domin tuntubar gwamnatin Afirka ta Kudu kan yadda za a biya diyya.

    Ya ce an buƙaci ƴan Najeriyan da ke dawowa su rubuta cikakken bayanin kadarorinsu da suka hada da kantuna da motoci da sauran dukiya, yana mai cewa shirin ba zai tsaya ga mayar da su gida kawai ba, gwamnati na kuma da ƙudurin kare jarin ƴan kasarta.

    A gefe guda kuma, wasu karin ƴan Najeriya 271 sun isa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas, bayan kwaso su daga Afirka ta Kudu, inda suka gargaɗi sauran ƴan kasa da su guji zuwa can.

    A jiya ne dai wasu ƴan Afirka ta Kudu suka gudanar da zanga-zangar ƙyamar baƙi bayan cikar wa’adin da aka ba ƴan ƙasashen waje da ba su da takaddar zama a ƙasar su fice, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a ƙasar.

  4. Ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliya a sassan jihar Legas

    Ruwan sama mai ƙarfi da aka shafe sa’o’i ana yi a ranar Talata ya haddasa ambaliya a sassan birnin Legas da ke kudancin Najeriya, lamarin da ya janyo tsaiko ga zirga-zirgar jama’a tare da jefa mazauna da dama cikin matsala.

    Gwamnatin Jihar ta bukaci mazauna su kwantar da hankulansu, tana mai cewa tana sa ido kan halin da ake ciki da kuma kokarin shawo kan matsalar ambaliyar da ta sake kunno kai a makonnin baya-bayan nan.

    Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar, Tokunbo Wahab, ya bayyana cewa ruwan saman ya zo da tsananin yawa cikin kankanin lokaci, wanda ya haddasa cunkoso a magudanan ruwa tare da janyo ambaliya a yankuna kamar Victoria Island, Lekki, Ikeja, Gbagada, Mushin da Mafoluku.

    Ya kuma ce ba Legas kaɗai irin wannan ruwan sama mai ƙarfi ya shafa ba, domin an samu makamancin haka a wasu sassan Afirka da ma Arewacin Amurka.

    Gwamnatin ta kuma gargaɗi jama’a da su guji zubar da shara a magudanan ruwa da kuma yin gine-gine a wuraren da ke hana ruwa gudana domin rage illar ambaliya a nan gaba.

  5. Za a rufe Tehran ranar Talata saboda jana’izar Ayatollah Khamenei

    Gwamnatin Iran ta sanar da cewa za a rufe babban birnin kasar, Tehran, a ranar Talata 6 ga watan Yuli, domin sauƙaƙa gudanar da jana’izar Ayatollah Ali Khamenei da kuma bai wa masu makoki damar fita daga birnin cikin sauki bayan halartar tarukan da za a gudanar.

    Mai magana da yawun gwamnatin, Fatemeh Mohajerani, ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin taimakawa wajen sauƙaka zirga-zirgar dubban mutanen da suka halarci jana’izar jagoran addinin ƙasar.

    Ta kuma bayyana cewa an ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar zaman makoki a faɗin Iran baki ɗaya.

    Ana sa ran binne Ayatollah Ali Khamenei a birnin Mashhad ranar Alhamis 8 ga watan Yuli.

    An tsara gudanar da tarukan jana’iza da alhini a biranen Tehran, Qom da Mashhad daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Yuli.

    Haka kuma, za a gudanar da wasu tarukan tunawa da shi a biranen Bagadaza, Kazmin, Karbala da Najaf a ƙasar Iraq.

    Ayatollah Ali Khamenei ya rasu ne sakamakon hare-haren saman da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, inda suka kai harin a gidansa sai dai har yanzu ba a binne shi ba.

  6. Assalamu alaikum!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda muke kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.