Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran ta yi atisaye a Washington
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Iran da ta isa Amurka da safiyar yau ta gudanar da atisaye domin shirin tunkarar wasan da za ta yi da Masar ranar Asabar a filin wasa na Jami'ar Washington da ke Seattle.
Hukumar ƙwallon ƙafar Iran ba ta fitar da cikakkun bayanai kan wannan atisayen ba, amma ƴan wasa 29 ne suka halarta.
Kamfanin yaɗa labarai na Iran ya ruwaito cewa, a gobe Juma'a ne tawagar ƙasar Iran za ta gudanar da atisaye a filin wasan da za ta fafata da tawagar ƙasar Masar ranar Asabar.
Wasan da za ta yi da ta Masar a ranar Asabar, zai yanke hukunci kan makomar tawagar ƙwallon ƙafar Iran a gasar cin kofin duniya.
Iran ta buga wasanninta biyu na farko ne a Los Angeles (Southern California), amma wasanta da Masar za a yi ne a Seattle (jihar Washington) da ke kusa da iyakar Amurka da Kanada.