KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohamed

  1. Ƴan sanda sun rufe wasu muhimman tituna a Nairobi yayin da ake shirin fuskantar zanga-zangar Gen Z a Kenya

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ƴan sanda a Kenya sun rufe wasu muhimman titunanan da ke shiga tsakiyar birnin Nairobi gabanin zagayowar cika shekara biyu da gudanar da zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka yi a ƙasar ƙarkashin jagorancin ƙungiyar Gen-Z.

    Dubban ƴan ƙasar Kenya ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da shirin ƙara harajin da aka yi a watan Yunin 2024, wanda ya kai ga yin kutse a fadar majalisar dokokin ƙasar, daga bisani kuma aka janye ƙudirin dokar kudin da ya janyo cece-kuce.

    Masu zanga-zangar sun ce suna neman a yi hukunci kan fiye da mutane 80 da aka kashe tare da jikkata wasu da dama yayin zanga-zangar ta 2024 da kuma zanga-zangar tunawa da ranar da aka yi a bara.

    Mutane da dama sun maƙale a kan hanya da safiyar ranar Alhamis bayan da jami’an tsaro suka tare hanyar shiga tsakiyar birnin, yayin da aka rufe kasuwanni da makarantu da dama.

    Ana sa ran za a gudanar da zanga-zangar da aka tsara a kan shafukan sada zumunta na intanet a manyan garuruwan da suka haɗa da Nairobi da Mombasa da kuma wasu sassan tsakiyar ƙasar Kenya.

  2. Farashin man fetur ya faɗi zuwa matakin da ya ke kafin yaƙin Iran

    ...

    Asalin hoton, Dallas Morning News via Getty Images

    Farashin man fetur ya faɗi zuwa matakin da ba a taɓa ganin irinsa ba tun kafin yaƙin Iran yayin da zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ke ci gaba da farfaɗowa sannu a hankali.

    Ɗanyen mai nau'in Brent ya faɗi zuwa ƙasa da dala 72.48 farashin da ya kasance a ranar da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu.

    Farashin makamashi ya yi tashin gwauron zabi tun lokacin da Iran ta mayar da martani ga hare-haren ta hanyar rufe mashigar ruwan da ke da matuƙar muhimmanci ga jigilar mai da iskar gas a duniya.

    Farashin danyen man fetur ya ragu matuƙa tun bayan da Amurka da Iran suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a ranar 17 ga watan Yuni wadda ta tanadi wa'adin kwanaki 60 don tattaunawa kan shirin nukiliyar Tehran da sauran matakan kawo ƙarshen yaƙin.

    Wakilan ɓangarorin biyu sun gana a ƙasar Switzerland a ƙarshen makon da ya gabata domin tattaunawa da niyyar kawo ƙarshen yaƙin, wanda ya sa Amurka ta dage wani ɓangare na takunkumin da ta ƙaƙabawa Iran ɗin.

  3. Girgizar ƙasa ta kashe aƙalla mutum 32 a Venezuela, tare da jikkata 700

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata girgizar ƙasa mai ƙarfi ta afku a ƙasar Venezuela, inda ta kashe aƙalla mutum 32, yayin da wasu 700 kuma suka jikkata ta kuma lalata gine-gine a Caracas babban birnin ƙasar.

    Shaidun gani da ido sun an ji ce girgizar kasar mai ƙarfin maki 7.1 har zuwa makwabciyarta Colombia, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Tun da farko dai Hukumar gargaɗi kan guguwarTsunami ta Amurka ta fitar da sanarwar yiwuwar afkuwar guguwar a Venezuela, da tsibirin Virgin Islands da kuma British Virgin Islands, amma yanzu ta janye gargaɗin.

    Hotunan da wakiliyar BBC Vanessa Silva ta ɗauka, sun nuna yadda masu aikin ceto ke neman waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan wani ginin bene da ya ruguje a yankin arewacin Caracas na San Bernardino.

    Rahotannin da ba a tabbatar ba sun nuna cewa aƙalla mutum ɗaya ya mutu a unguwar.

  4. Assalamu Alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiya

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kamar yadda aka sani za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.