Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 01 ga watan Agustan 2026

Taƙaitattu

  • Latsa nan domin shiga zaurenmu na Whattsapp
  • Trump ya musanta zargin Iran da kutse kan tsarin samar da ruwa a Minnesota
  • Iran ta ce za ta rufe mashigar Hormuz idan Amurka ta ci gaba da kai hare-hare
  • Farashin mai ya ƙaru saboda fargabar cikas ga jigilar mai ta Mashigar Hormuz
  • Masu ba Trump shawara sun nuna adawa da shirin kai sabbin hare-hare kan Iran
Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Isiyaku Muhammad

  1. Ana zargin Boko Haram da kashe sojojin Nijar 14

    Nijar

    Asalin hoton, ORTN

    Ana zargin mayaƙan Boko Haram da kashe sojojin Nijar 14 tare da jikkata wasu da dama a garin N'Guigmi da ke yankin Diffa a kudu maso gabashin ƙasar, kamar yadda shafin Actu Niger mai zaman kansa ya ruwaito.

    Rahoton ya ce, bisa bayanan da aka samu daga mazauna yankin, maharan ɗauke da manyan makamai sun kai hari ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe a ranar 31 ga Yuli, inda suka farmaki sansanin jami'an tsaro da ke wajen garin N'Guigmi a yankin Diffa.

    An binne sojojin da aka kashe a wannan rana da yamma, a wani taro da Gwamnan Diffa, Manjo Janar Mahamadou Ibrahim Bagadoma, ya halarta, inda ya isar da saƙon ta'aziyyar manyan shugabannin Nijar ga iyalan mamatan tare da ƙarfafa gwiwar sojojin da ke bakin aiki.

    Rahoton ya ƙara da cewa harin ya jawo martani mai ƙarfi daga dakarun Nijar, waɗanda suka ƙaddamar da farmakin ramuwar gayya domin daƙile maharan.

    Sojojin sun ce sun kashe wasu daga cikin maharan, sannan suka fara wani samame da sintiri domin bibiyar sauran waɗanda suka tsere a yankin Tafkin Chadi, inda suka ce sun daɗe suna haddasa tashe-tashen hankula.

    Yankin Diffa, wanda ke iyaka da Chadi a gabas da Najeriya a kudu, ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da suka fi fama da hare-haren Boko Haram tun bayan da rikicin ya bazu zuwa Nijar a shekarar 2015.

  2. Harin Isra'ila ya yi ajalin mutum biyu a Gaza bayan Hamas ta sanar da ajiye makami

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum biyu sun mutu sakamakon hare-haren sama da Isra'ila ta kai a Zirin Gaza, kwana guda bayan da Hamas ta amince da wata yarjejeniya da nufin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi da Isra'ila.

    Yarjejeniyar ta haɗa da mika makaman Hamas da kuma janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza.

    An kashe mutum ɗaya a wani unguwa da ke arewacin birnin Gaza, yayin da ɗayan ya mutu a tsakiyar Zirin Gaza.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kai harin ne kan mayaƙan Hamas, amma ba su bayar da ƙarin bayani kan harin ba.

    Hukumar kare fararen hula ta Gaza ta ce wani harin Isra'ila ya lalata rumbun adana kayayyakin magunguna na Asibitin Al-Aqsa sosai.

    Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinawa ta bayyana harin a matsayin "mummunan laifi."

    A nata ɓangaren, sojojin Isra'ila sun musanta cewa suna kai hari kan asibitoci, sai dai sun sha cewa Hamas na amfani da cibiyoyin kiwon lafiya wajen ɓoye mayaƙa da kayayyakin yaƙi.

  3. Na rabu da matata ne saboda rashin daidaiton ‘Genotype’ - A Zango

    Adam A Zango

    Asalin hoton, Adam A Zango/Facebook

    Fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, ya tabbatar da rabuwa da matarsa Maimuna Musa, wadda aka fi sani da Maimuna Pretty.

    A wani rubuta da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, jarumin ya ce jininsu ne suka gano ya zo ɗaya, shi ya sa suka amince su rabu.

    "Da gaske mun rabu da matata saboda mun gano muna da jini iri ɗaya. Ita AS ce nima AS ne. Don haka kada a mayar da wannan al'amarin namu ya zama wata maganar daban, ko kuma a riƙa yaɗa ƙarya," in ji shi.

    Zango ya ƙara da cewa ya yi wannan rubutun ne domin ya yi wa magoya bayansa cikakken bayanin abin da ke faruwa.

    Ya wallafa wani faifan bidiyo a ƙasan rubutun, inda ya ƙara da cewa, "za ku iya gani wannan bidiyon an naɗe shi ne a jiya da take barin gidana cikin nishaɗi."

  4. Jirgin kamun kifin Iran ɗauke da mutum 17 ya ɓace a Tekun Oman

    Kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ta ce wani jirgin kamun kifi mai suna Shahin 2, wanda ke ɗauke da ma’aikata 17, ya ɓace tun ranar 7 ga Mayu, a farkon kwanakin tsagaita wutar yaƙi tsakanin Iran da Amurka.

    Rahoton ya ce ba a sake jin duriyar jirgin ba bayan da jirage masu saukar ungulu na Amurka suka harbe fitilun gargaɗi kan wasu jiragen kamun kifi a Tekun Oman domin tarwatsa su.

    A cewar IRNA, ma’aikatan jirgin duka masunta ne daga garin Konarak da ke lardin Hormozgan na Iran.

    An bayyana cewa an samu sadarwa ta ƙarshe da jirgin ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe a ranar 7 ga Mayu, yayin da yake tafiyar kusan mil 70 daga gabar tekun Oman.

    Navid Baloch, ɗan’uwan kyaftin ɗin jirgin, ya ce sauran masunta sun ba da labarin cewa jirgin saman Amurka ya tarwatsa jiragen da ke yankin inda cikin rabin sa’a bayan haka dukkan jiragen suka sake haɗuwa, sai dai Shahin 2 kaɗai aka kasa gano inda yake.

    Tun bayan 21 ga Maris, yankin Tekun Fasha da Tekun Oman na ci gaba da kasancewa cibiyar rikice-rikicen soja da matsalolin tsaro da suka shafi yaƙin da ake yi a yankin.

  5. Rayuwar Bayahude guda ɗaya ta kai ta Falasɗinawa miliyan 10 - Lauyan Isra'ila

    Isra'ila

    Matsugunin Yahudawa na Havat Gilad da ke cikin Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, ya faɗaɗa a kan wasu tuddai, inda rumfuna da ƙananan gidaje ke bayyana daga ƙauyukan Falasɗinawa da ke maƙwabtaka da shi.

    A ƙarshen makon da ya gabata, an samu hare-haren da wasu matsugunan Yahudawa suka kai kan ƙauyukan Falasɗinawa da ke yankin, bayan da aka kashe wani jami'in tsaron Havat Gilad a wata arangama tsakanin Falasɗinawa da Isra'ilawa a ƙauyen Tal ranar Juma'a.

    A arangamar kuma, Falasɗinawa huɗu da wani sojan Isra'ila sun mutu, sai dai har yanzu ana saɓani kan abin da ya haddasa rikicin tun farko.

    Bayan shafe kwanakin ƙarshen mako yana tattaunawa da Falasɗinawa da ke zaune a yankunan da ke kewaye da Havat Gilad, wakilin BBC ya shiga matsugunin domin tattaunawa da ɗaya daga cikin mutanen game da tashin hankalin da kuma faɗaɗa matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan.

    Ba kasafai kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa irin su BBC ke samun damar shiga irin waɗannan matsugunai ba. Amma a wannan karon, Yehuda Shimon, lauya da ke aiki da wata ƙungiya mai kare Isra'ilawan da aka kama rikici da Falaɗinawa ya shaida wa BBC cewa hare-haren da aka kai kan ƙauyukan Falasɗinawa a ƙarshen makon sun kasance ramuwar gayya ne saboda kashe jami'in tsaron matsugunin.

    Ya ce: "Ina ganin yanzu da suka kashe ɗan Isra'ila guda ɗaya, ya kamata mu kashe duk mutanen Tal da Sarra, har ma da na Jit da Farata." yana kiran sunayen ƙauyukan Falasɗinawa mafi kusa da matsugunin Havat Gilad.

    Lokacin da wakilin BBC ya tambaye shi ko hakan na nufin yana daidaita rayuwar Bayahude guda da rayuwar ɗaruruwan ko dubban Falasɗinawa, sai ya amsa: "A'a, miliyoyi. Rayuwar Bayahude guda ɗaya ta kai ta Falasɗinawa miliyan 10."

    Da aka ƙalubalance shi cewa kalamansa na nuna wariyar launin fata, bai musanta ba.

    Ya ce: "Eh, na sani. Amma wannan ita ce gaskiya, domin Allah ne ya zaɓe mu, kuma saboda haka ne kuke kishi."

  6. Gwamnatin Zamfara za ta yi amfani da fasahar zamani wajen inganta tsaro

    Zamfara

    Asalin hoton, Habib Gajam/Facebook

    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa hedkwatar kamfanin Huawei da ke birnin Shenzhen na ƙasar Sin, inda suka tattauna da manyan jami'an kamfanin kan haɗin gwiwa wajen bunƙasa fasahar zamani a jihar.

    A yayin ganawar, gwamnatin Zamfara ta gabatar da shirinta na gina jihar da za ta dogara da fasahar zamani wajen inganta gudanar da mulki, ƙarfafa tsaro da faɗaɗa hanyoyin sadarwar zamani.

    A wata sanarwa da babban sakataren hukumar bunƙasa fasahar zamani ta jihar, Habib Gajam ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce jami'an Huawei sun bayyana irin fasahohin da suke da su da kuma nasarorin da suka samu wajen aiwatar da ayyukan gwamnati na zamani da sauya tsarin fasaha a ƙasashe daban-daban.

    Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa tana sa ran wannan tattaunawa za ta haifar da ayyukan da za su bunƙasa tattalin arziki, inganta rayuwar al'umma, tare da mayar da jihar ɗaya daga cikin cibiyoyin fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire a Arewacin Najeriya.

  7. Jakadun Amurka sun gargaɗi ’yan ƙasarsu a Gabas ta Tsakiya su shirya ficewa daga yankin

    Ofishin Jakadancin Amurka da ke Bagadaza da kuma ofishin jakadancin ƙasar a Erbil sun fitar da sanarwar tsaro, suna gargaɗin ’yan ƙasarsu da ke Gabas ta Tsakiya da su kasance cikin shiri idan ya zama dole su bar yankin.

    Sanarwar ta ce rikicin da ke ƙara ƙamari a yankin ya sa yanayin tsaro ya kasance mai sarƙakiya, tare da yiwuwar samun wata sabuwar ƙazancewar lamura.

    An kuma gargadi matafiya cewa za a soke zirga-zirgar jiragen sama tare da rufe sararin samaniya na wucin gadi da kuma tangardar tafiye-tafiye.

    Sanarwar ta buƙaci ’yan Amurka da ke yankin su yi la’akari da ficewa ko kuma su kasance cikin shirin barin yankin idan rikicin ya ƙara tsananta.

    Ofisoshin jakadancin Amurka da ke Amman a Jordan da kuma Urushalima ma sun fitar da irin wannan gargaɗi.

  8. Matar babban jami’in kula da kuɗaɗen ISWAP da ɗanta sun miƙa wuya ga sojoji

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce matar babban jami'in kula da harkokin kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP tare da ɗanta mai shekara 11 sun miƙa wuya ga dakarunta na Operation Hadin Kai ta ƙauyen Kusuma da ke Jihar Borno.

    Sojojin sun ce binciken farko ya nuna cewa mijin matar, wanda ya kasance babban kwamandan ISWAP ya miƙa wuya a ranar 25 ga Yuli kuma shi ne ya umarce ta da ta fito daga maɓoyarsu tare da ɗansu.

    Sanarwar spjojin ta ce mayaƙan sun tsere a wani samame ta daban da sojojin suka kai a yankin Turoh bayan samun bayanan sirri.

    Bayan binciken yankin, dakarun sun kwato babura biyu da kuma tarin miyagun ƙwayoyi da mayaƙan suka bari a baya, yayin da rundunar ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa hare-haren da suka dogara da sahihan bayanan sirri.

  9. Isra'ila ta ce an jikkata jami'in sojinta a artabu da Hezbollah

    Sojojin Isra'ila sun sanar da cewa an jikkata wani jami'in sojinsu a daren jiya yayin wata arangama da mayaƙan Hezbollah a kudancin Lebanon, duk da cewa ana ci gaba da tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin.

    A cikin wata sanarwa, rundunar sojin Isra'ila ta ce wanda ya jikkata jami'in soja ne, sai dai ba ta bayyana girman rauninsa ba.

    Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce ya tuntuɓi Hezbollah domin jin ta bakin ƙungiyar kan lamarin, amma ba ta mayar da martani ba.

    Hezbollah dai ba ta ɗauki alhakin kai wani hari ba kusan tsawon wata ɗaya da rabi.

  10. Iran ta ce ƙasashen Musulmi su sake nazarin alaƙa da Amurka

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Iran ta yi kira ga ƙasashen Musulmi da su sake nazarin alaƙa da haɗin gwiwarsu da Amurka, tana mai cewa sauyin yanayin siyasa da tsaro a yankin ya sa hakan ya zama wajibi.

    Babban kwamandan Hedikwatar rundunar sojin Iran, Ali Abdullahi, ya ce Amurka na ƙara rura wutar rikici a yankin, kuma ya kamata ƙasashen Musulmi su yi taka-tsantsan wajen ci gaba da ba ta goyon baya ko haɗin kai.

    Ya kuma yi gargaɗin cewa duk wata ƙasa da ta amince a yi amfani da yankinta ko cibiyoyinta domin taimaka wa Amurka a yaƙin da ake yi na iya shiga cikin rikicin.

    Abdullahi ya ce ma'aunin ƙarfi a yankin ya sauya, yana mai jaddada cewa Iran za ta ɗauki duk wani sansani ko kadarorin Amurka da ake amfani da su a kanta a matsayin halastattun wuraren da za ta iya kai wa hari.

  11. PDP tsagin Turaki ta miƙa sunan Jonathan ga INEC a matsayin ɗan takararta a zaɓen 2027

    ...

    Asalin hoton, @kabiruturakisan

    Jam'iyyar PDP tsagin Kabiru Turaki ta ce ta miƙa sunan tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

    Tsagin ya bayyana hakan ne ta bakin kakakin kwamitin riƙon ƙwarya na jam'iyyar, Ini Ememobong, a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja.

    A cewarsa, rikicin shugabanci da ya dabaibaye PDP bayan hukuncin Kotun Ƙoli ya haifar da kafa kwamitin riƙon ƙwarya domin tafiyar da harkokin jam'iyyar da kuma gudanar da muhimman ayyukanta.

    Tsagin Turakin ya nace cewa shi ne halastaccen shugabancin PDP, wanda ya tsayar da Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa tare da sauran 'yan takarar gwamnoni, majalisun dokoki na tarayya da na jihohi.

    Haka kuma ya ce ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke kwanan nan dangane da rikicin shugabancin jam'iyyar.

  12. Ƙarar da aka ji ya biyo bayan fashewar wani bom tun na yaƙin Iraki - Iran

    Jami'an yankin Islamabad ta Yamma a lardin Kermanshah na Iran sun ce ƙarar fashewar da aka ji a yankin ta samo asali ne daga wani bom da ya rage tun lokacin yaƙin Iran da Iraq, bayan da gobara ta tashi a wurin.

    Gwamnan yankin ya ce fashewar ta auku ne kusa da gadar hanyar zobe ta gabashin birnin, inda aka tura jami'an tsaro da agaji nan take bayan jin ƙarar.

    A cewarsa, zafin gobarar da ta tashi a wurin ne ya haddasa fashewar tsohon bam ɗin da ya rage tun daga yaƙin Iran da Iraq na tsawon shekara takwas.

    Tun da farko, kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an ji wata ƙarar fashewa a kusa da Islamabad ta Yamma, lamarin da ya haifar da hasashe kan musabbabinta kafin hukumomi su yi bayani.

  13. An ji ƙarar fashewa a yammacin Islamabad da ke Iran

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an ji ƙarar wata fashewa a kusa da yankin Yammacin Islamabad da ke lardin Kermanshah.

    Rahotannin sun ce har yanzu ba a tantance ainihin wurin da fashewar ta auku ko abin da ya haddasa ta ba.

    Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba zuwa yanzu, yayin da ake ci gaba da jiran ƙarin bayani game da abin da ya faru.

  14. Iran ta gargaɗi Birtaniya kan duk wata haɗin gwiwa a harin da za a kai mata

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya gargaɗi Birtaniya cewa duk wata haɗin gwiwa ko taimako da za ta bayar wajen kai hari kan Iran ba abu ne da ƙasarsa za ta amince da shi ba.

    A wata tattaunawar waya da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, Ed Miliband, Araqchi ya ce bai halatta a yi amfani da yankin wata ƙasa ko cibiyoyinta wajen kai hari kan wata ƙasa ba, yana mai cewa hakan na iya kasancewa "aikin ta'addanci" a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa, kuma ƙasar da aka kai wa hari na da haƙƙin kare kanta.

    A cewar Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Miliband ya bayyana cewa Birtaniya ba ta shiga yaƙi da Iran, kuma ta fi goyon bayan amfani da hanyoyin diflomasiyya wajen rage zaman ɗarɗar a yankin.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Miliband ya ce ya tattauna da Ministan Harkokin Wajen Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, kan hanyoyin rage tashin hankali a Gabas ta Tsakiya da kuma kare 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigar Hormuz.

  15. Sojojin Najeriya sun kama mutum shida kan zargin taimakawa ISWAP a Borno

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta na Operation Hadin Kai sun kama mutum shida da ake zargi da taimaka wa mayaƙan ISWAP wajen gudanar da ayyukansu a Damasak da ke Jihar Borno.

    A cewar rundunar, an kama mutanen ne a ranar 27 ga Yulin 2026 bayan wasu bayanan sirri sun nuna cewa suna taimaka wa ƙungiyar wajen samar da kuɗaɗe ta hanyar saye da sayar da shanu a kasuwannin Gubio, Damasak da Ajuwango.

    Sojojin sun ce sun ƙwace makamai da mota da kuma kuɗi Naira 317,950 daga hannun waɗanda ake zargin.

    Rundunar ta bayyana cewa waɗanda aka kama na ci gaba da fuskantar bincike, tana mai jaddada aniyarta ta ci gaba da lalata hanyoyin samar da kuɗi da kayan aiki ga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.

  16. Masu ba Trump shawara sun nuna adawa da shirin kai sabbin hare-hare kan Iran

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga kafofin watsa labarai ta CBS da Wall Street Journal sun ce wasu masu ba shugaban Amurka Donald Trump shawara sun nuna adawa da wani shirin da ake zargin Amurka da Isra'ila na yi na kai sabbin hare-hare kan cibiyoyin makamashi a Iran.

    Rahotannin sun ce an tattauna shirin a wani taron majalisar ministocin Trump da aka gudanar a Camp David, inda wasu daga cikin masu ba shi shawara na siyasa suka yi watsi da batun ƙaddamar da sabon farmakin.

    CBS ta ruwaito cewa Amurka da Isra'ila na duba yiwuwar kai hare-hare masu ƙarfi kan muhimman cibiyoyin makamashin Iran, yayin da Wall Street Journal ta ce Trump ya amince da wani sabon shiri domin ƙara matsin lamba ga Tehran.

    Fadar White House ba ta tabbatar da rahotannin kai hare-haren ba kai tsaye, amma kuma ba ta musanta su ba, tana mai jaddada cewa Amurka ba za ta bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

    Yayin da yaƙin Iran ya shiga wata na shida, har yanzu ɓangarorin biyu na ci gaba da tsayawa kan matsayinsu, inda Amurka ke neman Iran ta dakatar da shirinta na nukiliya, yayin da Tehran ta ƙi ja da baya.

  17. Farashin mai ya ƙaru saboda fargabar cikas ga jigilar mai ta Mashigar Hormuz

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen mai ya tashi a kasuwannin duniya bayan fargabar cewa rikicin da ke yankin zai iya haddasa cikas ga jigilar mai ta Mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar da ake amfani da ita wajen safarar mai.

    Farashin ɗanyen mai na Brent ya ƙaru da kashi 1.2 cikin ɗari zuwa dala 90.12 kan ganga, yayin da ɗanyen man Amurka ya tashi da kashi 1.3 cikin ɗari zuwa dala 84.67.

    Hauhawar farashin ta biyo bayan rahotannin cewa an dakatar da wasu jiragen dakon mai ko kuma aka tilasta musu sauya hanya ta mashigar Hormuz.

    Yaƙin Iran ya rage yawan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, yayin da barazanar mayaƙan Houthi kan jiragen ruwa a Bab al-Mandab ke ƙara jefa sauran hanyoyin fitar da mai cikin haɗari.

  18. Iran ta ce za ta rufe mashigar Hormuz idan Amurka ta ci gaba da kai hare-hare

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Ali Akbar Zolghadr, ya ce Iran za ta rufe mashigar ruwa ta Hormuz idan Amurka ta ci gaba da kai hare-hare ko takaita zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

    Ya gargaɗi cewa hakan zai iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin duniya, kasuwar makamashi da kuma Amurka.

    A lokaci guda, kafofin yaɗa labarai na Iran sun ruwaito cewa Tehran ta shirya wani faɗaɗɗen shiri na mayar da martani idan Amurka ta kai hari.

    Wani babban jami'in tsaro da ba a bayyana sunansa ba ya ce rahotannin yiwuwar harin Amurka da Isra'ila kan Iran "rashin hankali ne", yana mai cewa martanin Iran zai haɗa da kai hari kan muhimman cibiyoyin Isra'ila da na makamashin Amurka a yankin.

  19. Trump ya musanta zargin Iran da kutse kan tsarin samar da ruwa a Minnesota

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce bai yarda cewa Iran ce ke da hannu a kuste ta intanet da aka yi kan tsarin samar da ruwa na jihar Minnesota ba, duk da cewa wasu rahotanni sun nuna cewa wasu jami'an Amurka na zargin Tehran da hannu a lamarin.

    Da yake magana a wani taron majalisar ministocinsa, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito, Trump ya ce: "Mun ji an yi kutse ta intanet a Minnesota kuma ana ɗora laifin kan Iran. Ni ban yarda da hakan ba."

    Maimakon haka, Trump ya dora alhakin kan jami'an jihar da Gwamnan Minnesota mai jam'iyyar Democrat, Tim Walz, ba tare da gabatar da wata hujja da ke goyon bayan zarginsa ba.

    A nasa martanin, Gwamna Tim Walz ya ce Donald Trump ya san waɗanda ke da alhakin kutsen, yana mai ƙara da cewa irin an samu iran waɗannan kusten a wasu jihohin Amurka ma.

  20. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiya

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.