Wasu matasa sun fantsama kan titunan birnin tarayyar Najeriya da wasu jihohi domin nuna ɓacin ransu kan ƙaruwar matsalar tsaro a ƙasar.
Zanga-zangar na zuwa a daidai lokacin da ƙasar ke bikin tunawa da ranar dimokraɗiyyar ƙasar da aka shafe shekaru 27 ba tare da yankewa ba.
Matasan sun buƙaci shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi gaggawar ɗaukar matakin da ya dace domin magance matsalar tsaro a sassan ƙasar.
Ɗan gwagwarmaya Omoyele Sowore ya jagoranci zanga-zangar rashin tsaron a birnin tarayya Abuja, inda ya yi kira ga shugaba Tinubu ya yi gaggawar ceto ɗaliban da aka sace a jihar Oyo.
Sowore ya kuma yi ƙorafi kan matsin rayuwa da ake ciki a Najeriya da rashin samun ci gaba da kuma garkuwa da mutane.
Ya ce ƙasar ba ta samu wani ci gaban da ya kamata ba duk da an shafe shekaru 33 da komawa tsarin ɗimokradiyya, inda ya yi kira ga Tinubu ya yi murabus idan ba zai iya kare rayukan ƴan ƙasar ba.
A jihar Osun ma matasa sun fantsama kan titunan birnin jihar domin nuna damuwarsa kan halin da ƙasar ke ciki.
Ƙungiyoyin sa kai sun shiga zanga-zangar, inda suka soki salon mulkin Bola Tinubu kan matsalar tsaro da tsadar rayuwa a ƙasar.
Wani matashi Saka Lawal ya shaida wa BBC cewa bai taɓa ganin mulkin da ake shan wahala irin na wannan lokacin ba.
"Muna buƙatar shugaba Bola Tinubu ya yi gaggawar magance matsalolin da Najeriya ke ciki kafin abin ya wuce gona da iri" in ji shi.