Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 11 ga watan Yuni, 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muslim Muhammad Yusuf da Usman MINJIBIR

  1. Wani ɗan sanda ya mutu a wani samame da aka kai a Toronto

    A ranar Alhamis ne aka harbe wani ɗan sanda a birnin Toronto har lahira a wani samame da aka kai sakamakon harin da aka kai a watan Maris a wajen ƙaramin ofishin jakadancin Amurka.

    Rundunar ƴan sandan Toronto ta ce an harbe ɗan sandan ne a yayin musayar wuta da aka yi a wani katafaren gini da sanyin safiya.

    Daga baya aka tabbatar da rasuwarsa a asibiti.

    Ƴan sanda sun yi ta bincike kan waɗanda ake zargi da yin harbi a ƙaramin ofishin jakadancin Amurka da ke Toronto a cikin watan Maris, abin da hukumomin Amurka da Canada suka bayyana a lokacin a matsayin "al'amarin da ke alaƙa tsaron ƙasa".

    Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, mai suna Zara Jabbi mai shekaru 19, har yanzu ana tsare da shi kuma an bayyana shi a matsayin "mai riƙe da makamai kuma mai haɗari", in ji shugaban ƴan sandan Toronto Myron Demikw.

    "Zan buƙaci duk wanda ya gan shi da ya kira 9-1-1 nan take," in ji Demikw.

    Ƴan sanda sun ce an harbe wani wanda ake zargi a musayar wutan kuma aka kai shi asibiti amma ba a bayyana sunansa ba.

  2. Vance ya ce Netanyahu ya yi 'kuskure' kan waɗansu abubuwa

    Mataimakin shugaban ƙasar Amurka JD Vance ya ce, "Tabbas Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yayi kuskure kan wasu abubuwa'', yayin da alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara tsami cikin ƴan makonnin nan sakamakon yaƙin haɗin gwiwa da su ke yi da Iran.

    Duk da yake Vance ba zai ba da misalai ba, ya shaida wa abokiyar hulɗar BBC ta Amurka CBS News, cewa Netanyahu "yana ƙarfafa tabbatar da muradun ƙasarsa" amma ba koyaushe suke daidaituwa da na Amurka ba.

    Kalaman nasa sun nuna ƙara tabbatar cewa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu na fuskantar barazana cikin ƴan kwanakin nan.

    A baya-bayan nan ne dai rahotanni suka ce shugaban Amurka Donald Trump ya yi arangama da shugaban na Isra'ila kan matakin soji da Isra'ila ke ɗauka a ƙasar Lebanon wanda ya haifar da sake kai hare-hare tare da yin barazana ga tattaunawar sulhu da Tehran.

    Amurka da Iran sun yi musayar wuta a rana ta biyu a jere cikin dare, lamarin da ya kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu da ke aiki tun watan Afrilu.

    Hakan na zuwa ne bayan da Trump ya ce Tehran ta ɗauki lokaci mai tsawo kafin amincewa da yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, ko da yake an sake samun tashin hankali ne sakamakon abubuwan da suka faru a Lebanon, inda Isra'ila ke ci gaba da kai farmaki kan ƙungiyar Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran.

  3. Harin jirgi mara matuƙi ya kashe mutum huɗu a maƙabarta a Sudan

    Wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama guda biyu na Sudan, Doctors Network da Emergency Lawyers sun bayyana cewa, wani harin da jirgin yaƙi mara matuƙi ya kai a wata maƙabarta da ke birnin el-Obeid na ƙasar Sudan ya kashe aƙalla mutum 4 tare da jikkata wasu da dama.

    Duka ƙungiyoyin biyu sun zargi ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF) da kai harin.

    Ƙungiyar Emergency Lawyers ta ce harin wani ɓangare ne na rukunin hare-haren da jiragen yaƙi marasa matuƙa da suka fara kia wa da yammacin ranar Laraba inda aƙalla mutane 23 suka mutu.

    RSF ba ta ce komai ba kan harin ba.

    El-Obeid, wanda a halin yanzu yake hannun sojoji, wani muhimmin fagen daga ne a yaƙin basasar Sudan da aka kwashe shekara uku ana gwabzawa, wanda ya faro bayan da shugabannin sojojin da RSF suka yi takun saka kan alƙiblar ƙasar nan gaba.

    Faɗan dai ya haifar da matsalar jin ƙai mafi muni a duniya inda aka tilastawa sama da mutane miliyan 11 barin gidajensu yayin da wasu miliyan 28 ke fuskantar matsananciyar yunwa.

    Babu sahihan alƙaluma na adadin waɗanda suka mutu, amma ana kyautata zaton ya kai aƙalla 50,000.

  4. Mu na daf da cimma yarjejeniya da Iran - Trump

    Da yake magana a fadar White House, Trump ya ce "Amurka ta yi sulhu kan yaƙin da ta ke yi da Iran ".

    Ya ci gaba da cewa: "Muna kan kammala tattara takardun yarjejeniyar. Za iya kamatawa nan da ƴan kwanaki masu zuwa."

    Trump ya ce "wataƙila za a sanya hannu, mai yiwuwa a Turai" da zarar an kammala tattara takardun, kuma ya kamata a yi "da sauri".

    "Mun ƙulla yarjejeniyar cewa Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba, wanda shi ne maƙasudin abin da ya sa muka yi wannan abun don mu samu hakan. Don haka abu ne babba."

    Trump ya ce za a buɗe mashigar Hormuz "da zarar mun sanya hannu".

    Ya kuma ce ya yi magana da shugabannin yankin da suka haɗa da ƙawayen Amurka na ƙasashen Gulf da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ƙara da cewa: " Yankin Gabas ta tsakiya baki ɗayanta na mauƙar farin ciki".

  5. Farashin ɗanyen mai ya faɗi bayan soke hare-haren Amurka

    Farashin ɗanyen mai ya faɗi a kasuwannin duniya sakamakon soke sabbin hare-haren da Amurka ke kaiwa Iran.

    Brent crude, wanda shi ne ma'aunin man fetur a duniya,yi ragu inda ake sayar da shi ƙasa da dalar Amurka 90 a kowace ganga, bayan sanarwar da Shugaba Donald Trump ya yi na janye shawarar kai hare-haren.

    Farashin gangar mai ya yi ƙasa da dala 100 tun daga makon da ya gabata na watan Mayu, amma bai ragu zuwa farashin da ya ke kafin Amurka da Isra'ila su fara yaƙi da Iran - kafin ɓarkewar rikicin da, ana sayar da Brent Crude ne a kan kusan dala 70 kan kowanne ganga guda.

  6. Trump ya dakatar da hare-haren da ya shirya kai wa Iran

    Shugaba Trump ya dakatar da hare-haren da Amurka ta shirya kai wa Iran yan sa'o'i masu zuwa.

    Trump ya ce an samu ci gaba da tattaunawar da ake yi manyan shugabannin Iran.

    Tunda farko, Trump ya yi barazanar kai munanan hare-hare a wurare masu mahimmanci na Iran.

    Inda ya ce Amurka na dab da kwace tsibirin Kharg.

    Dakatarwar na zuwa ne bayan da Amurka ta sun kwashe dare biyu a jere tana kai munanan hare-hare Iran, inda ita Iran ɗin ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka dake yankin Gabas Ta Tsakiya.

    Wani babban mai shiga tsakani na Iran, Mohammad Baqer Ghalibaf, ya yi gargadin cewa Amurka za ta yi wa kan ta dabaibayin da za ta kwashe shekaru ba ta warware ba.

  7. Iran ta gargaɗi Amurka kan barazanar kai ma ta hari

    Wani babban jami'in Iran ya gargaɗi Amurka game da abin da ya kira shiga cikin wani 'dabaibayin da ba za ta iya fita daga ciki ba'.

    Mohammad Bagher Ghalibaf, kakakin majalisar dokokin Iran kuma babban mai shiga tsakani, ya bayyana a cikin wani sakon da ya wallafa a shafin X cewa "Munanan dabaru da kuma yanke hukunci cikin gaggawa zai sake dagula lamura tsakanin ƙasashen biyu''.

    Ya ce matakan Amurka za su iya "Tarwatsa ɓangaren makamashi da kasuwanni", su kuma jefa haifar da "dabaibayin da za ku kwashe shekaru kafin ku warware".

    "Za ku ga wata Iran ce ta daban," in ji shi.

    Waɗannan kalamai nasa dai na zuwa ne bayan barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na cewa za su kai wa Iran hari a daren nan za kuma su ƙwace tsibirin Kharg.

  8. An yi arangama tsakanin masu zanga-zanga da ƴansanda a Kashmir

    Aƙalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da jami’an tsaro a yankin Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Pakistan, kamar yadda hukumomin yankin suka sanar.

    Kwamitin haɗin gwiwa na Awami Action (JAAC), gamayyar ƙungiyoyin fafutuka, sun yi kira ga jama’a da su yi zanga-zangar nuna adawa da tanadin kujerun majalisa masu yawa ga ƴan gudun hijirar da ba sa zama a yankin, gabanin zaɓe mai zuwa.

    Hukumomin ƙasar sun mayar da martani inda suka zargi ƙungiyar da tayar da zaune tsaye, inda ta da haramta ƙungiyar tare da bayar da ladan kama shugabanninta.

    Sai dai hakan bai hana dubban mutane yin tattaki zuwa Muzaffarabad babban birnin yankin ba, lamarin da ya kai ga ƙazamin atrabu da jami'an tsaro.

    Waɗanda suka mutu sun haɗa da fararen hula 11 da jami'an tsaro huɗu.

  9. Kotu a Thailand ta yanke wa mutum biyu hukuncin kisa bisa laifin kai harin bam

    Wata kotu a ƙasar Thailand ta samu wasu mutane biyu da laifin kai harin ta'addanci mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar ba, tare da yanke musu hukuncin kisa.

    Mutanen biyu ƴan ƙabilar Uyghur waɗanda ƴan tsiraru ne ƙasar China, an same su da laifin shiryawa da tayar da wani babban bam a yammacin ranar 17 ga watan Agustan 2015, kusa da wani wurin ibada da ke tsakiyar birnin Bangkok wanda ya shahara ga masu yawon buɗe ido na ƙasashen waje.

    Mutane 20 ne suka mutu inda sama da 120 suka jikkata.

    Sai dai kura-kuran da aka samu a binciken ƴan sanda, da kuma shari’ar da aka shafe shekara goma ana yi wa mutanen biyu, waɗanda dukkansu suka ƙi amsa laifi, ya bar tambayoyi a kan wannan hukunci.

    Bam ɗin ya fashe ne kusa da ofishin BBC da ke birnin Bangkok.

    Fashewar ta tarwatsa mutanen da suke addu'o'i a wurin ibadar Erawan, sannan kuma ta shafi mahaya babura da ke zaune a bakin hanyar da ke kusa da wurin, inda wasu daga cikinsu suka kone.

    A cikin makonni biyu da kai harin aka damƙe mutanen biyu da a yanzu aka yanke wa hukunci.

  10. An rufe wani ɓangaren ginin Pentagon sakamakon 'gurɓacewar iska'

    An rufe yawancin benaye da ke cikin ginin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon saboda abin da aka bayyana a matsayin "batun rashin ingancin iska", wanda ya sa hukumar magance abubuwa masu haɗari (hazmat) ta kyallace wani ɓangaren ginin.

    ''Matakan tsaron ginin sun gano wani lamari da ke nuni da 'gurɓacewar iska' da ke buƙatar ɗaukar matakan kariya har sai mun tantance muhimmancinsa,” in ji mai magana da yawun Pentagon Sean Parnell.

    Ya ƙara da cewa an tabbatar da matakan tsaro da kariya ga ma;aikata da kuma mutanen da ke zama da aiki a yankin da lamarin ya shafe.

  11. Sakataren tsaron Birtaniya ya yi murabus

    Sakataren tsaron Birtaniya, John Healey, ya yi murabus, bayan ya zargi Firaministan ƙasar da gazawa wajen cika alƙawuran inganta kuɗaɗen da ake kashewa a aikin soji.

    A wasiƙarsa ta Murabus, Mista Healey, ya ce Keir Starmer da ma'aikatar kuɗi ba su fitar da kuɗaɗen da ake buƙata wajen bada tsaron kasa.

    Ya nuna damuwa kan ƙaruwar barazanar tsaro daga Rasha.

    Wakilin BBC ya ce ya ga wasiƙun murabus da dama a rayuwrsa amma bai taɓa ganin mafi ban mamaki irin wannan ba.

    Shirin inganta tsaron ƙasa na Birtaniya na tafiyar hawainiya, inda ma'aikatar tsaro da ta kuɗi suka gagara cimma matsaya kan yada za'a samu kuɗaɗen bunƙasa tsaron ƙasa da aikin soji.

  12. Ba da yawunmu aka ba da umarnin kama Mele Kyari ba - Majalisar Dattawa

    Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ba da yawunta aka bayar da umarnin kama tsohon shugaban kamfanin man fetur na ƙasar, NNPCL, Mele Kyari ba, dangane da binciken zargin batar da wasu kuɗaɗe har Naira tiriliyan 210.

    A yayin wani zama ne dai aka tafka muhawara tsakanin kwamitin binciken kuɗin al'umma na majalisar dattawa kan binciken da suke yi.

    Jaridar The Cable ta ruwaito cewa majalisar ta ce babu wata sanarwa daga gare ta da ke nuna ta amince da umurnin kama Kyari, inda ta yi kira da a guji yaɗa bayanan da za su iya haifar da ruɗani kuma za ta ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

    Majalisar ta kuma soki kalaman Sanata Adams Oshiomhole na bayyana kamfanin a matsayin "matattarar ɓarayi".

    Ta jaddada cewa duk wani mataki da za a ɗauka dole ya cika ka’idoji da matakan da doka ta tanada.

    Shi ma kwamitin da ke jagorantar binciken, ya ce kalaman da Oshiomhole ya yi ba da yawunta ya yi ba.

    Sai dai wata sanarwa ta ambato Kyari na nuna rashin jin daɗinsa game da umurnin, kuma a yanzu haka ya fita ƙasar waje domin duba lafiyarsa.

  13. Ƴan Indiya uku sun mutu a harin da Amurka ta kai kan wani jirgin ruwan dakon mai

    An tabbatar da mutuwar wasu ma’aikatan ruwa guda uku ƴan ƙasar Indiya bayan da sojojin Amurka suka kai hari kan wani jirgin ruwan dakon man fetur a mashigin tekun Oman da ta zarga da keta dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran.

    A ranar Laraba ne aka kai wa jirgin MT Settebello hari, yayin da ta ke ɗauke da ma’aikatan Indiya 24, inda aka ceto 21 daga cikinsu.

    A wani sakon da ya wallafa a shafin X, ministan sufurin jiragen ruwa na Indiya Sarbananda Sonowal ya ce nan ba da jimawa ba za a dawo da gawarwakin mutanen uku gida.

    Amurka ta kai hari kan jiragen ruwa guda uku a cikin tekun Gulf a wannan makon, dukkansu ɗauke da ƴan ƙarasr Indiya.

    A ranar alhamis, Delhi ya ce dukkan ma'aikatan jirgin 20 da ke cikin jirnin ruwa mai suna Jalveer suna cikin koshin lafiya bayan wani harin da aka kai kan jirgin a Oman.

    Kwanaki uku a baya an ceto ma'aikatan Indiya 24 da ke cikin jirgin ruwan dakon mai mai suna Marivex kafin ya nutse. Cibiyar gudanar da lamuran tsaro ta Amurka (Centcom) ta tabbatar da kai hari kan jiragen ruwan biyu.

    A cikin wani sakon da aka wallafa a dandalin X, CENTCOM ta ce ɗaya daga cikin jiragen yaƙinta ya kai hari kan wani jirgin ruwan dakon mai sakamakon abin da ya bayyana a matsayin rashin bin umarni daga ɓangaren ma'aikatan jirgin.

  14. Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da dokar ƙirƙiro ƴan sandan jihohi

    Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da ƙudurin dokar ƙirƙirar ƴan sandan jihohi.

    An amince da ƙudurin ne bayan kaɗa ƙuri'a a zauren majalisar a yau Alhamis, inda kakakin majalisar Abbas Tajuddeen ya jagoranci zaman.

    Abbas ya ce, ƴan majalisa 288 ne suka amince da ƙudurin, yayin da 4 suka ƙi amincewa da shi.

    Ƴan majalisar sun amince da ƙudurin ne ta hanyar ɗaga hannu saboda na'urar kaɗa ƙuri'ar ba ta a aiki a lokacin.

    Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, Majalisar Dattawa ma ta amince da ƙudurin samar da ƴan sandan jihohin bayan yi masa karatu na biyu.

    Shugaban Majalisar Godswill Akpabio ya ce ƴan majalisar za su kaɗa ƙuri'a kan ƙudurin a zama na gaba, inda ta miƙa shi zuwa kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na majalisar.

  15. NDC ce ke yi wa Obi da Kwankwaso alfarma ba su ba - Dickson

    Jagoran jam'iyyar adawa ta NDC a Najeriya Sanata Seriake Dickson ya yi zazzafan martani da gargaɗi ga magoya bayan ɗantakarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peter Obi da mataimakinsa Rabiu Musa Kwankwaso kan yunƙurin ɓata sunan jam'iyyar.

    A wata hira da gidan talabijin na Arise, tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya ce jam'iyyar ce ke yi wa ƴan takarar alfarma ba wai su ke mata ba.

    Dickson ya nuna takaicinsa kan abin da ya ce wasu magoya bayan ƴan siyasar na yi wajen ganin sun ɓata sunan jam'iyyar da bijirewa dokokinta, inda ya ce ya yi aiki tuƙuru wajen kafa jam'iyyar kuma ta samu karɓuwa tun kafin ƴan siyasar adawar su shiga cikinta.

    A ƴan kwanakin nan dai ana ta samun tankiya tsakanin magoya bayan Obi da Kwankwaso da kuma shugabannin jam'iyyar tun bayan rahotannin sauya wasu ƴan takara a jihohi daban-daban.

    Sai dai jagoran jam'iyyar ya ce ko sisin kwabo Obi da Kwankwaso ba su bayar wajen kafa jam'iyyar ba, tare da gargaɗin magoya bayansu da su je su kafa tasu jam'iyyar idan suna ganin abu ne mai sauƙi ko kuma ba za su iya bin dokokin jam'iyyar ba.

  16. Farashin mai ya tashi bayan barazanar Trump ta kai hari Iran

    Farashin mai ya ƙaru da kusan dala biyu bayan da shugaba Donald Trump ya yi barazanar kai "zazzafan hari" kan Iran cikin dare tare da karɓe ikon mai da gas ɗinta.

    Farashin ɗanyen mai samfurin Brent ya ƙaru zuwa dala 94 kan kowace ganga cikin ƙanƙanin lokaci, duk da yake ya sauƙa ƙasa kaɗan.

    Trump ya wallafa barazanar ne a shafinsa na Truth Social, a yayin da ƙasashen biyu suka ci gaba da yi wa juna ruwan wuta.

    "Nan kusa za mu karɓe iko da tsibirin Kharg da wasu albarkatun man ƙasar, kuma za mu yi iko da fannin makamashinta, kamar yadda muka yi wa Venezuela, kuma hakan yana yi wa Venezuela da Amurka tasiri," in ji Trump

  17. Amurka za ta 'ragargaji' Iran cikin dare - Trump

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta ƙaddamar da "zafafan hare-hare" kan Iran cikin daren yau.

    Trump ya wallafa hakan ne a shafinsa na Truth Social, a yayin da ƙasashen biyu suka ci gaba da yi wa juna ruwan wuta.

    Ya ce za su karɓe tsibirin Kharg da kuma wasu cibiyoyin manta, kuma za su dawo ƙarƙashin ikonta kamar yadda suka yi wa Venezuela.

    "Amurka za ta ragargaji Iran sosai a daren yau (Duk da yake mun kassara sojin ruwanta da na'urar sararin samaniya da jiragen yaƙinta kuma mun karya lagon rundunar tsaronta)

    "Nan kusa za mu karɓe iko da tsibirin Kharg da wasu albarkatun man ƙasar, kuma za mu yi iko da fannin makamashinta, kamar yadda muka yi wa Venezuela, kuma hakan yana yi wa Venezuela da Amurka tasiri," in ji Trump

    Tun bayan da aka fara yaƙin, Trump ke ta barazanar karɓe iko da tsibirin Kharg, wajen da tarin man ƙasar Iran yake.

  18. Ƴan adawa ne ke kambama matsalar tsaro domin ɓata sunan Tinubu - Matawalle

    Ƙaramin Ministan tsaro na Najeriya, Bello Muhammad Matawalle ya zargi ƴan adawar ƙasar da zuzuta matsalar tsaro domin ɓata sunan shugaba Bola Tinubu.

    Matawalle ya yi zargin cewa suna yaɗa farfaganda domin cimma wata manufar siyasa da kauda hankalin mutane kan ci gaban da ake samu a ƙasar.

    Ya ce ana samun nasarori sosai a yaƙi da matsalar tsaro da dakarun Najeriya ke yi musamman a yankin arewacin maso yammacin ƙasar.

    "Babu wata farfaganda ko yarfen siyasa da za su kauda hankalin shugaban ƙasa kan cika alƙawuran da ya yi wa ƴan Najeriya," in ji shi.

    Wata sanarwa da mai taimaka wa Ministan kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil ya fitar, ta ambato Matawalle na cewa "duk da irin waɗannan suka da ake yi, Tinubu na da farin jini a arewacin ƙasar."

    Ministan ya ce Tinubu ne zai lashe zaɓen 2027 musamman a arewacin ƙasar saboda suna ganin irin nasarorin da ake samu.

    "Ƴan adawar suna ganin irin ci gaban da ake samu a yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar, sai dai su yaɗa farfaganda kawai" in ji Matawalle.

    Ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙara ƙaimi wajen yaƙar ƴan bindiga a jiihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna da Kebbi, kuma ana ganin sakamako mai kyau.

    "Al'ummar yankin suna ganin irin ƙoƙarin da ake yi... muna da tabbacin cewa ƴan Najeriya na goyon bayan sauye-sauyen da ake samu".

  19. Ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afrika ta Kudu sun isa Legas

    Jirgin farko na ƴan Najeriya da aka kwashe daga Afrika ta Kudu sun isa gida da safiyar yau Alhamis.

    Mutanen da aka kwashe su kusan 270 sun sauka ne a filin jirgin saman ƙasar da ke jihar Legas.

    Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya yi jigilar mutanen, yayin da gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyin dukkan kuɗaɗen kwashe su.

    Ƙasashen Afrika da dama sun kwashe mutanensu daga Afrika ta Kudu saboda hare-haren ƙyamar baƙi da ke faruwa a ƙasar.

    Ghana da Mozambique sun riga sun kwashe ɗaruruwan 'yan ƙasarsu.

    Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana nazarin matakin da za ta ɗauka domin maida martani game da abin da ke faruwa.

    Hukumomi sun ce zuwa yanzu an tantance sama da ƴan Najeriya 500 da za su koma gida, kuma ana ci gaba da tantancewar.

  20. Ƴan asalin Najeriya 14 da za su buga kofin duniya a 2026

    Super Eagles ba ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 da za a fara daga ranar 11 ga watan Yuni ba a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    To sai dai tana da ƴan wasa 14 ƴan asalin Najeriya da za su wakilce ta da za a kara tsakanin kasashe 48 a karon farko a tarihin gasar.

    Saboda haka, kasa shiga gasar da Najeriya ta yi ta bana, bai hanata samun ƴan ƙwallonta da za su wakilce ta a babbar gasar tamaula ta duniya.

    Kenan Najeriya tana da wakilci na daban a gasar—wanda ba a kan sunan ƙasa kai tsaye bane—amma ta hanyar ƴan ƙwallo fiye da 14 masu asalin Najeriya da za su wakilci ƙasashe takwas daban-daban a gasar da za a gudanar.