Naim Qassem, babban sakataren ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, ya sake yin watsi da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Lebanon da Isra'ila a ranar Juma'a, yana mai cewa ƙungiyar da Iran ke mara wa baya ba za ta "miƙa wuya" ba hakan nan.
A cikin wani jawabi da aka watsa ta gidan talabijin na Al-Manar, Qassem ya ce: "Ba mu lamunta da yarjejeniyar tsarin ba, kuma muna neman a soke ta."
Lebanon da Isra'ila sun shiga tattaunawa kai tsaye ƙarƙashin sasancin Amurka bayan yaƙin da ya fara ranar 2 ga Maris, lokacin da Hezbollah ta kai hari kan Isra'ila, wanda daga baya ya biyo bayan hare-hare masu yawa da kuma mamayar sojojin Isra'ila ta ƙasa a Lebanon, inda jami'an Lebanon sun ce fiye da mutum 4,300 ne suka mutu a yaƙin.
A tattaunawar da aka yi a ƙarshen watan Yuni, ɓangarorin biyu sun cimma wata yarjejeniya, wadda ta tanadi kwance ɗamarar Hezbollah, janye sojojin Isra'ila daga kudancin Lebanon a hankali, da kuma tura sojojin Lebanon zuwa yankin.
Sai dai Naim Qassem ya bayyana yarjejeniyar a matsayin "haramtacciya, wadda aka yi ba bisa ƙa'ia ba, kuma abin wulaƙanci kuma mai rusa ƴancin Lebanon."
Ya kuma ce Hezbollah na adawa da kafa yankunan gwaji da kuma duk wata hanya ta sa ido ko tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar.
Haka kuma, ya nuna goyon bayansa ga aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta watan Nuwamban 2024, wadda aka cimma domin kawo ƙarshen yaƙin da ya gabata tsakanin Hezbollah da Isra'ila.