Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Juma'a 11/09/2026

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed

  1. A karon farko tun bayan yaƙin Ukraine, Putin zai halarci taron Brics a India

    Babban birnin Indiya, Delhi, yana cikin shirin ko-ta-kwana gabanin taron shekara-shekara na ƙungiyar ƙasashen BRICS.

    A karon farko tun bayan mamayar da Rasha ta fara yi wa Ukraine gaba ɗaya, Shugaba Vladimir Putin zai halarci taron BRICS da za a gudanar a wajen Rasha.

    Rahotanni daga Delhi sun ce za a kafa matakan tsaro masu matakai huɗu domin kare Mista Putin, baya ga jami’an tsaron da ke tare da shi.

    An jibge dubban jami’an ’yan sanda da sojoji a babban birnin, yayin da aka girke na’urorin gano jirage marasa matuƙa a kewayen wurin da za a gudanar da taron.

  2. Majalisar Najeriya ta dakatar da zuwa Afirka ta Kudu

    Majalisar Dokokin Najeriya ta dakatar da wasu ziyarce-ziyarcen aiki zuwa Afirka ta Kudu, tare da cewa za ta kaurace wa duk wasu ayyukan majalisa da za su kasance a Afirka ta Kudu har zuwa wani lokaci.

    Matakin ya biyo bayan rahotannin kisan kai, hare-hare, tsoratarwa da lalata kadarorin da suka shafi ƴan Najeriya da sauran ƴan Afirka a Afirka ta Kudu. Mahukuntan Afirka ta Kudu sun musanta wasu daga cikin waɗannan ikirari, tare da cewa suna gudanar da bincike kan abubuwan da aka ruwaito.

    A cikin wata sanarwa, Majalisar Dokokin Najeriya ta ce ana “kashewa da rauna ƴan Najeriya da muhallansu, tare da tilasta wa wasu barin sana’o’insu da gidajensu.

    Ƴan majalisar sun kuma buƙaci gwamnatin Afirka ta Kudu ta kare baƙin da ke zaune a ƙasar, ta gudanar da bincike kan hare-haren da aka ruwaito tare da gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a cikinsu.

    A watan Yuni, Najeriya ta fara kwashe ƴan ƙasarta daga Afirka ta Kudu saboda fargabar tsaro. A cewar gwamnatin Najeriya, sama da ƴan Najeriya 1,500 ne suka dawo ƙasar tun daga lokacin.

    Wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Ghana, Malawi da Zimbabwe, su ma sun taimaka wa ƴan ƙasarsu barin Afirka ta Kudu saboda damuwar da ake da ita kan tashin hankalin.

    Majalisar Dokokin Najeriya ta ce matakin da ta ɗauka ba yana nufin kawo ƙarshen dangantakar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu ba.

  3. Yadda gobara ta kashe yara 20 a makaranta a DRC

    Mahukunta sun tabbatar da mutuwar yara ƴan makaranta aƙalla 24, a lokacin da suke ƙoƙarin tserewa daga gobarar da ta tashi a cikin wasu makarantu biyu, a birnin Bukavu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, lamarin da ya janyo ruɗani sosai.

    An kuma bayar da rahoton mutuwar wasu manya a wajen, yayin da hukumomi ke bayyana fargabar ƙaruwar yawan mutanen da za gobarar ta kashe saboda akwai wasu da aka garzaya da su asibiti domin duba lafiyar su.

    Hotunan da aka yaɗa na wajen da abin ya faru sun nuna ƙananan yara a kwance a ƙasa, a cikin asibiti, suna kuka saboda tsananin azabar ƙunar wuta.

    Gidaje 300 wutar ta ƙona, kuma har yanzu ba a gano abin da ya tayar da ita ba.

    Mahukunta sun ce lamarin ya faru ne a birnin Bukavu da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da ke ƙarƙashin ikon ƴan tawaye, inda ake fama da cunkoson jama'a.

    Bayanan da mayaƙan ƴan tawaye da ke iko da wajen suka fitar sun nuna cewa mutanen da suka rasu sun kai 24, amma akwai fargabar adadin zai ƙaru.

    Hotunan da aka yaɗa a kafafen sada zumunta sun nuna ƙananan yara kwance a ƙasa, kuma da alama gawarwaki ne.

    Shaidun da kamfanin dillanci labarai na Reuters ya zanta da su sun ce tun da rana aka kashe wutar, amma ana ci gaba da ganin hayaƙi da ke ɓullowa daga ƙarƙashin gine-ginen da aka rusa domin kashe gibarar.

    Bukavu, babban birnin kudancin lardin Kivu kuma yankin da ya fi cunkoson jama'a a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya faɗa a ƙarƙashin ikon mayaƙan tawaye na M23 ne a watan Faburairun bara.

    Amma gwamnati a Kinshasa ta wallafa sanarwa a shafin X, ba tare da ta bayyana yawan mutanen da gobarar ta kashe ba.

    Sanarwar ta ce "Ma'aikatar ilimi da kula da ƴan ƙasa ta bayyana damuwa matuƙa kan mummunar gobarar da ta tashi,''

    "An yi asarar rayuka da yawa kuma wasu da dama sun ji rauni. Ministan Ilimi na aikewa da ta'aziya ga iyalan waɗanda lamarin ya ritsa da su, kuma ya bayar da umarnin tantance halin da makarantun da abin ya shafa suke ciki, tare da tabbatar da ganin an ci gaba da harkokin karatu.''

    Gobarar biyu sun faru ne bayan wata gobarar ta daban a ƙarshen makon da ya gabat a Kinshasa, inda aka samu asarar rayuka wajen turereniyar neman guduwa daga gobarar da ta tashi a wajen wani ɗakin taro ana tsakiyar biki.

    Gwamnatin ƙasar ta bayar da umarnin tsaurara matakan rigakafi, kuma ta tura jami'ai a sannan ƙasar domin sanya ido da tabbatar da kaucewa tashin gobara a wuraren da mutane ke taruwa.

  4. Ƙungiyar JNIM ta ɗauki alhakin kashe soja a Benin

    Ƙungiyar Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM), reshen ƙungiyar Al-Qaeda a yankin Sahel, ta yi ikirarin kashe wani soja a wani hari da ta kai a Benin, wanda shi ne harin farko da ƙungiyar ta yi ikirari a ƙasar cikin watanni.

    JNIM ta fitar da ikirarin ne ta kafar watsa labaranta ta al-Zallaqa, a tasharta ta musamman da ke ChirpWire, a ranar 10 ga Satumba.

    A cikin taƙaitacciyar sanarwar, ƙungiyar ta ce a ranar 9 ga Satumba ta kashe wani soja a wani hari da ta kai kan wani sansanin sojoji a ƙauyen Kantoro, kusa da garin Guene, a sashen Alibori.

    Wannan shi ne harin farko da JNIM ta yi ikirarin kai wa a Benin tun bayan wasu hare-hare da suka faru a watan Mayu.

    Hare-haren ƙungiyar a Benin sun fi faruwa ne a arewacin ƙasar, musamman a yankunan da ke kusa da iyakar Benin da Nijar.

  5. Mayaƙan Houti sun ƙwace garin Dhubab na gabar tekun Yemen

    Wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Yemen sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Juma’a cewa mayaƙan Houti sun isa Dhubab, wani gari da ke arewacin mashigar ruwan Bab al-Mandab, kuma shi ne wuri mafi kusa da tsibirin Mayun.

    Garin yana yammacin lardin Taiz, a gaɓar tekun yammacin Yemen.

    Majiyoyin Yemen sun kuma bayar da rahoton cewa jiragen yaƙin Saudiyya sun kai hari kan filin jirgin saman Mocha.

    Haka kuma, tashar jiragen ruwa ta Mocha ta faɗa hannun mayaƙan na Houti, waɗanda Iran ke mara wa baya, a cikin ƴan kwanakin nan.

    Samun iko da Dhubab da tsibirin Mayun na da matuƙar muhimmanci wajen mamaye mashigar ruwan Bab al-Mandab.

    Hakan na nufin cewa kusan gaba ɗaya Houthis sun mallaki iko da mashigar ruwan Bab al-Mandab.

    Ƙaruwar ikon mayaƙan a mashigar Bab al-Mandab, da kuma ƙaruwar hare-hare kan jiragen dakon mai a mashigar ruwan Hormuz cikin makon da ya gabata, sun jefa kasuwar mai da makamashi cikin garari. Farashin dizal a Amurka ya kai dala shida kan galan ɗaya a karon farko.

  6. An saki Turawa mata biyu da aka yi garkuwa da su a Nijar

    Wata ƴar ƙasar Austria da wata ƴar ƙasar Switzerland da aka yi garkuwa da su a lokuta daban-daban a arewacin Nijar a shekarar 2025, sun shaƙi iskar ƴanci, kamar yadda kamfanin dillancin labarai mai zaman kansa na Air Info Agadez ya ruwaito a ranar 11 ga Satumba.

    Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance da ta tabbatar da sakin Eva Gretzmacher, ƴar Austria, da Claudia Abbt, ƴar Switzerland.

    An yi garkuwa da matan biyu ne daga gidajensu a Agadez a watan Janairu da Afrilu na 2025, yayin da wasu majiyoyi suka danganta sace su da ƙungiyar IS.

    Rahoton ya ce tun bayan da aka yi garkuwa da su, an yi ƙoƙarin ganin an sake su, amma ba a samu nasara ba.

    Wani ɗan uwan ɗaya daga cikin matan da aka yi garkuwa da su ya shaida wa Air Info Agadez cewa ba su da wani cikakken bayani da ke tabbatar da sakin ta, duk da cewa sun shafe kwanaki suna jiran samun labari mai daɗi.

    Abbt ta shafe shekaru da dama tana zaune a Agadez tare da mijinta ɗan Nijar. Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki alhakin sace ta.

    Gretzmacher, mai shekara 73, ta shafe shekara 28 tana zaune a Agadez kafin a yi garkuwa da ita. Ita ce ta kafa ƙungiyar Amanay, kuma ta kasance mai ruwa da tsaki a ayyukan da suka shafi ilimi da ƙarfafa mata da kare muhalli da al'adu da fasaha.

  7. MDD ta yi gargaɗi kan yaƙin basasar Yemen

    Wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Yemen ya yi gargaɗin cewa wajibi ne ƙasashen duniya su tunkari wani abin da ya kira sabon mataki mafi haɗari na yaƙin basasar ƙasar.

    Hans Grundberg ya ce kwace tashar jiragen ruwa ta Mokha ya bai wa ƙungiyar Houthi mai samun goyon bayan Iran damar kasancewa kai-tsaye a wata muhimmiyar hanya da jiragen ruwa ke bi a duniya.

    Tashar jirgin ruwan ta Mokha na kan Mashigar Bab al-Mandeb, wadda muhimmiyar mashigar ruwa ce da ke da matuƙar tasiri ga safarar mai daga Saudiyya da kuma kasuwancin duniya.

  8. Me ya faru a harin 11 ga Satumba, kuma mutum nawa ne suka mutu?

    Shekara 25 ke nan tun bayan harin da aka kai a ranar Talata, 11 ga Satumba, 2001, lokacin da wasu maharan ƙunar baƙin-wake suka yi juya akalar jiragen fasinja na Amurka, tare da yi musu dirar-mikiya a kan manyan gine-gine biyu a birnin New York, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

    A yau ne za a gudanar da bikin tunawa da waɗanda suka rasa rayukansu a harin a Amurka, inda ake sa ran gudanar da bukukuwa da wasu shirye-shirye daban-daban.

  9. Trump ya ƙi amincewa da buƙatar Saudiyya ta kai wa mayaƙan Houti hari

    A cewar Axios, Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman, ya kira Shugaban Amurka Donald Trump sau biyu a ranar Alhamis, inda ya buƙaci shugaban na Amurka ya kai hari kan mayaƙan Houti.

    A lokaci guda, ƴan Houtin da Iran ke mara wa baya suna ci gaba da kutsawa tare da ƙwace iko da tashar jiragen ruwa ta Mocha, lamarin da ke ƙara musu iko a yankin mashigar ruwan Bab al-Mandab.

    Rahoton ya ce Mista Trump bai amince da wannan buƙata ba, yayin da jami'an Amurka suka jaddada cewa a halin yanzu gwamnatin Amurka ba ta da wani shiri na shiga yaƙi kai tsaye da mayaƙan Houti.

    A safiyar yau kuma, Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran ta fitar da wata sanarwa inda ta yi kira da a kawo ƙarshen katange hanyoyin shiga Yemen ta soji, sannan a fara tattaunawa.

  10. Farawa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai tsaye daga BBC Hausa muna muku barka da safiyar ta Juma'atu babbar rana.

    Za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin kallon wasu hotuna da bidiyon hirarraki da muke wallafawa tare da yin tsokaci a kai.