Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Lahadi 13/09/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Isiyaku Muhammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Trump ya roƙi Zelensky ya dakatar da kai hari kan cibiyoyin man Rasha

    Shugaban Amurka Donald Trump ya buƙaci shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da ya dakatar da kai hare-hare kan cibiyoyin man Rasha.

    Trump ya ɗora alhakin ƙarancin man fetur a kan shugaban Ukraine, ba wai yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ba.

    Sojojin Ukraine sun sanar da cewa sun kai hari kan wasu matatun mai biyu na Rasha a daren jiya, ɗaya a kudancin ƙasar, ɗayan kuma mai tazarar kusan kilomita 900 a gabashin Moscow.

    Hare-haren Ukraine kan wuraren samar da mai na Rasha sun haifar da ƙarancin man fetur a yankuna da dama na ƙasar.

  2. Shettima ya gabatar da jawabin Najeriya a taron BRICS

    Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya gabatar da jawabin Najeriya a taron shugabannin ƙasashen BRICS na shekarar 2026 da ke gudana a New Delhi, India.

    A cikin jawabin da ya gabatar a madadin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, Shettima ya yi kira da a gaggauta sake fasalin tsarin shugabancin duniya da cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa, domin samar da tsarin da ya fi wakilci, adalci da kuma amsa buƙatun ƙasashe.

    Ya ce Najeriya na goyon bayan tsarin da zai yi daidai da sauye-sauyen tattalin arziki daidai yawan jama'a na duniya.

    Mataimakin shugaban ya kuma gayyaci masu zuba jari daga ƙasashen waje da su yi amfani da damarmakin zuba jari da ke Najeriya, yana mai cewa ƙasar na iya zama hanyar shiga babbar kasuwar Afirka a ƙarƙashin yarjejeniyar AfCFTA.

    A gefe guda kuma, Najeriya da India sun sake tabbatar da aniyarsu ta ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu.

    Ministarsu harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta gana da takwaranta na India, Dr. Jaishankar, a yayin taron, inda suka tattauna batutuwan kasuwanci, ilimi, al'adu da kuma harkokin ofishin jakadanci.

    Sun kuma tattauna batun jin daɗin ƴan Najeriya da ke zaune a India, musamman waɗanda suka wuce wa'adin bizar su.

    Ministar ta nemi a ƙara wa'adin afuwar da ake da shi, domin bai wa waɗanda abin ya shafa damar komawa Najeriya da kansu ba tare da fuskantar hukunci ba.

    Bangarorin biyu sun kuma tattauna yiwuwar kulla yarjejeniyar musayar mutanen da aka yanke wa hukunci a gidan yari, da kuma hanyoyin faɗaɗa kasuwanci da zuba jari tsakanin ƙasashen.

    Taron na BRICS India ce ke karɓar baunci a wannan shekara.

  3. Iran na matuƙar son mu tattauna - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran na matuƙar son cimma yarjejeniya da Amurka, yana mai cewa ƙasar na ci gaba da neman a tattauna da ita.

    Trump ya ce ya yi imanin cewa yaƙin da Amurka ke yi da Iran zai ƙare kafin ko kuma jim kaɗan bayan zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka.

    "Iran na son cimma yarjejeniya. Suna ci gaba da kira na. Suna son cimma yarjejeniya, amma dole ne yarjejeniyar ta zama wadda ta dace. Ba zan amince da yarjejeniyar da ba yi daidai ba," in ji shugaban Amurkan ga manema labarai yayin gasar Irish Open.

    Trump ya yi irin wannan magana a makon da ya gabata, inda a ranar Laraba 9 ga watan Satumba ya shaida wa manema labarai cewa yana ganin yaƙin da Iran zai ƙare "nan da nan bayan zaɓen Amurka", yana nufin zaɓen tsakiyar wa'adin da za a gudanar a watan Nuwamba.

    Wannan na zuwa ne a lokacin da Iran ta ce taron da za a gudanar gobe a Oman zai tattauna wata sabuwar hanya ta zirga-zirgar jiragen ruwa ta Mashigin Hormuz.

  4. Dakarun Iran sun gargaɗi jiragen ruwan Amurka da ke tunkarar mashigar Hormuz

    Mataimakin kwamandan rundunar sojojin ruwa ta Juyin Juya Halin Iran, Ali Mohammadi, ya yi tsokaci kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump na cewa yana iko da mashigin Hormuz, inda ya ce: “Idan haka ne, da sunan Allah. Ku kawo ɗaya daga cikin jiragen ruwanku cikin tazarar kilomita 100.”

    Babban jami'in na IRGC ya ce “Amurkawa sun san cewa idan jiragen ruwansu suka kusanto, za su fuskanci martani daga mayaƙan Iran,” sannan ba tare da bayar da cikakken bayani ba, ya yi iƙirarin cewa “an samu irin wannan misali a kwanakin baya.”

    Da yake magana a wani taron dare na magoya bayan gwamnati a birnin Mashhad, ya ce: “A yau... babu sojojin Amurka a Tekun Fasha, Tekun Oman da mashigar Hormuz, sannan babu kayan aikin sojin Amurka da aka jibge a waɗannan yankuna. Idan Amurkawa suka kusanci yankin da aka kayyade, su kansu sun san abin da zai faru da su.”

    A cewarsa, “duk wani jirgin ruwa da ya taso daga Kuwait ko Bahrain, ba tare da togiya ba, yana ƙarƙashin sa ido na rundunar sojojin ruwa ta IRGC, kuma idan aka gano wani take doka, za a ɗauki mataki a kansa bisa ƙa'idojin da aka tanada.”

  5. Ba za mu miƙa wuya ba - Iran

    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya rubuta a shafin X yana sukar hare-haren da ake kai wa ababen more rayuwa na fararen hula da kuma matsin lambar da ake yi wa rayuwar jama'a.

    Ya ce: “Idan Amurkawa masu son yaƙi ne, su fuskanci dakarun sojinmu masu ƙarfin hali. Me ya sa suke kai hari kan ababen more rayuwar fararen hula, abinci da hanyoyin samun abin masarufin jama'a? Idan mutane ne, me ya sa suke hana jama'a ruwa, abinci da magunguna? Ba za a tilasta wa al'ummarmu miƙa wuya ta hanyar ƙarfi da matsin lamba ba. Iran ba za ta miƙa wuya ba.”

    Kalaman Mista Pezeshkian sun zo ne yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar tashe-tashen hankula da kuma musayar hare-hare tsakanin Iran da Amurka.

    A ranar da ta gabata, yayin taron ƙungiyar BRICS a New Delhi, ya ce matsin tattalin arzikin da ake yi wa Iran ya shiga “wani mataki mafi hatsari sosai” bayan yaƙin da aka yi tsakanin Iran da Amurka da Isra'ila.

    A wannan taron, shugaban na Iran ya yi kira ga ƙasashen BRICS da su samar da wata hanya da za ta hana dakile halastacciyar huldar kasuwanci tsakanin ƙasashe sakamakon matsin lambar siyasa da tattalin arziki.

    Ya kuma jaddada muhimmancin faɗaɗa amfani da kuɗaɗen ƙasashen da ke cikin ƙungiyar wajen gudanar da hada-hadar kasuwanci tsakaninsu.

  6. Ƴan Yemen sun tsallaka Djibouti domin gudun hijira

    Djibouti ta ce mutum 1,400 ne suka tsallaka zuwa kasarta daga Yemen a cikin sa'o'i 24 kacal, sakamakon kazamin fada tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da kuma mayakan Houthi.

    Wakilin BBC ya ce Djibouti ta ce rikicin ya raba fararen hular Yemen a Sam ciki har da mata da yara da muhallansu inda a yanzu suke tsallakawa zuwa tekun Bab al Mandeb domin mafaka.

    A cikin 'yan kwanakin nan, mayakan Houthi sun kwace iko da daukacin gabar tekun Bahar Maliya ta bangaren Yemen, lamarin da ya kara karfafa ikonsu a mashigar Bab el-Mandeb, wata muhimmiyar hanyar ruwa da ke kula da zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa Bahar Maliya.

    A wani bangare na rikicin kuma, mayakan Houthi sun ce sun kai hari kan wani sansanin sojin Saudiyya da ke yankin Sharurah.

  7. Iraq ta sake buɗe bakin iyakarta da Iran

    Kamfanin dillancin labaran gwamnatin Iraƙi ya ruwaito cewa an sake buɗe zirga-zirga a mashigai uku na kan iyakar ƙasar da Iran, waɗanda aka rufe bayan wani hari da jirgin sama mara matuƙi ya kai kan bututun mai na Saudiyya mai haɗa gabashi da yammacin ƙasar.

    A cewar rahoton, za a sake fara zirga-zirgar fasinjoji a yau a mashigar Al-Shayb da ke lardin Maysan, wadda ake kira Chadhabeh a Iran, da kuma mashigar Shalamcheh da ke lardin Basra. Haka kuma, za a sake dawo da harkokin kasuwanci a waɗannan mashigai daga baya cikin wannan makon.

    Za a kuma sake fara harkokin kasuwanci a mashigar Mandali da ke lardin Diyala, wadda ake kira tashar kan iyaka ta Somar a Iran, daga ranar Talata.

    A jiya Asabar, gwamnatin Iraƙi ta rufe mashiganta da Iran na ɗan lokaci, bayan da ta gano wurin da aka harba wani jirgin sama mara matuƙi daga cikin ƙasar zuwa Saudiyya.

  8. Ƴanbindiga sun sace malamai shida bayan halartar addu'ar neman nasarar Tinubu

    Ƴansanda a Najeriya sun ce wasu ƴanbindiga sun sace limamai shida a jihar Zamfara da ke arewacin ƙasar.

    Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, lokacin da limaman suka halarci wani taron addu'a na neman nasarar Shugaba Bola Tinubu, wanda ke neman wa'adi na biyu a babban zaɓen da za a gudanar a watan Janairu.

    Sace mutane domin neman kuɗin fansa ya zama babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da dama a Najeriya, ciki har da masu iƙirarin jihadi da kuma ƙungiyoyin ƴanbindiga waɗanda ba su da wata manufa ta aƙida, waɗanda ke neman kuɗin fansa kafin su saki mutanen da suka yi garkuwa da su.

    Rashin tsaro da kuma halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki na daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye yaƙin neman zaɓen da ake gudanarwa a yanzu.

    Sai dai a wata sanarwa da rundunar sojin ta Fansar Yamma ta fitar, ta ce bincikensu ya tabbatar da cewa ba a gidan Abdulaziz Yari aka sace malaman ba.

    "Mun dai samu labarin cewa an sace wasu mutane matafiya da suka taso daga yankin dajin Sububu zuwa Talata Mafara, kuma jami'anmu da haɗin gwiwar sauran jami'an tsaro suna ƙoƙarin ceto," in ji sanarwar.

  9. Ba yaƙi muke yi da Saudiyya ba - Iran

    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran “ba ta yaƙi da Saudiyya.”

    A yau, Saudiyya ta dakatar da aikin bututun mai na Gabas zuwa Yamma, bayan an kai hari kan muhimmin bututun mai na ƙasar a daidai lokacin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta.

    Mista Pezeshkian ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta India Today a gefen taron BRICS da ake gudanarwa a New Delhi cewa: “Ba mu yaƙi da Saudiyya. 'Yan Houthi suna da nasu matsalolin. Na sha faɗa cewa ya kamata dukkan ƙasashen yankin su zauna a teburi guda domin samar da zaman lafiya da tsaro a yankin. Babu wata hujja ko dalili da zai sa mu kasance cikin yaƙi ko rikici da juna.”

    Baghdad da Riyadh dukkansu sun ce harin ya samo asali ne daga Iraƙi, inda ƙungiyoyin mayaƙan da Iran ke marawa baya suke aiki.

    Hare-haren sun biyo bayan wani samame na bazata da 'yan Houthi masu ƙawance da Iran suka kai, wanda ya bai wa ƙungiyar damar ƙwace iko da wata muhimmiyar hanyar ruwa a Gabas ta Tsakiya da ake amfani da ita wajen fitar da mafi yawan man Saudiyya.

  10. 'Dabarar turai wajen taimakon Ukraine a yaƙi na haifar da sakamako mai kyau'

    Mai bai wa gwamnatin Birtaniya shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Jonathan Powell, ya ce dabarar da Turai ke bi wajen goyon bayan Ukraine da kuma kakaba wa Rasha takunkumi na haifar da kyakkyawan sakamako.

    Da yake jawabi a wani taro da aka gudanar a birnin Kyiv, Powell ya ce ya zama wajibi kasashen Turai su kasance cikin shiri don fuskantar kowanne irin kalubale musamman a lokacin hunturun bana, domin ci gaba da matsa wa Moscow lamba.

    Ya ce duk da yiwuwar karancin iskar gas da ake sa ran za a fuskanta, bai kamata Turai ta sassauta takunkumin da ta kakaba wa Rasha ba.

    Jonathan Powell, ya kuma bayyana cewa Ukraine ta riga ta yi nasara a yakin, saboda har yanzu tana kan gaba a fafatawar da ake, sannan kuma Rasha ba za ta iya mamaye daukacin kasar ba. ends

  11. Ebola ta fara lafawa a DR Congo - Gwamnati

    Gwamnatin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ta ce ta yi amannar cewa annobar Ebola da ake fama da ita a yanzu ta fara lafawa.

    Mai magana da yawun gwamnatin kasar ya bayyana a shafinsa na sada zumunta cewa an samu raguwar masu kamuwa da cutar tun daga tsakiyar watan Augustan da ya gabata.

    Wakilin BBC ya ce jami'ai sun ce cibiyoyin lafiya 10 daga cikin 61 na kasar ba su samu ko da mutum guda da ya kamu da cutar ba cikin makonni uku da suka gabata.

    Sai dai ya jaddada cewa har yanzu akwai bukatar a ci gaba da sanya ido tare da daukar matakan kariya domin kauce wa sake yaduwar cutar.

    Gwamnatin kasar ta ce an samu sama da mutum 7,000 da suka kamu da Ebola tun bayan barkewarta a watan Mayu. Hukumomi sun kuma ce kusan rabin wadanda suka kamu da cutar sun rasu.

  12. Yaƙin Yemen ya raba aƙalla mutum 76,000 da muhallansu - MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutum 76,000 ne suka rasa matsugunansu a Yemen tun bayan da mayaƙan Houthi suka sanar da kafa shingen hana zirga-zirgar jiragen ruwa zuwa Saudiyya a watan Yuli.

    A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya, adadin mutanen da aka raba da muhallansu ya ninka sau huɗu cikin makon da ya gabata, yayin da faɗa tsakanin dakarun gwamnati da Houthis masu ƙawance da Iran ke ƙara tsananta.

    A cikin wani rahoto kan “raba mutane da muhallansu da ke ƙara muni cikin gaggawa a Yemen”, Ƙungiyar Ƙasa da Ƙasa ta Kula da Hijira (IOM) ta yi gargadin cewa “sau da yawa iyalai baki ɗaya kan bar gidajensu da daddare, ba tare da wani wuri mai tsaro da za su fake ba.”

    IOM ta ce mafi yawan mutanen da aka raba da muhallansu na faruwa ne a yankunan gabar tekun yammacin ƙasar da kuma lardin Taiz.

    A cewar ƙungiyar, lardin Taiz ne ya fi fuskantar wannan matsala, inda kusan iyalai 8,300, waɗanda adadinsu ya kai kusan mutane 50,000, suka rasa matsugunansu a sassa daban-daban na lardin.

  13. Buɗewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai tsaye daga BBC Hausa muna muku barka da safiyar yau Lahadi.

    Za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin kallon wasu hotuna da bidiyon hirarraki da muke wallafawa tare da yin tsokaci a kai.

    Da fatan ana hutun ƙarshen mako lafiya.