Yawan mutanen da suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar Ebola a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya haura 6,000.
Alƙaluman da ma’aikatar lafiya ta ƙasar ta fitar, sun nuna cewa adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar yanzu ya zarce 12,000.
Ƙoƙarin daƙile yaɗuwar cutar ya fuskanci ƙalubale sakamakon faɗace-faɗace tsakanin sojojin gwamnati da ƙungiyoyin 'yan tawaye a yankin.
A halin yanzu babu allurar riga-kafi ko magani da aka amince da shi don nau’in cutar na Bundibugyo.
Sai dai, ana gudanar da gwaje-gwaje da dama kan wasu alluran riga-kafi a sassa daban-daban na Gabashi da Tsakiyar Afirka.
Ƴan cirani kusan 2,000 sun isa tsibirin Crete na Girka
Asalin hoton, Reuters
Gwamnatin Girka ta ce sa'o'i 48 da suka gabata sun kasance mafi wahala a bana, dangane da yawan ƴan cirani da suka isa kasar, inda kusan mutum 2,000 suka isa tsibirin Crete.
An ceto sama da mutum dubu ɗaya daga cikin kwale-kwale, yayin da ɗaruruwan wasu kuma suka isa tsibirin a karshen mako.
Cibiyoyin tarbar ƴan cirani na yankin na fama da cunkoso, kuma ana sa ran za a kwashe bakin hauren zuwa sansanonin karɓarsu da ke babban yankin ƙasar a cikin kwanaki masu zuwa.
Girka na ɗaya daga cikin ƙasashen Tarayyar Turai biyar da suka sanar da shirinsu na buɗe cibiyar mayar da ƴan cirani zuwa Rwanda a shekara mai zuwa.
Zaɓen gwaji ya nuna cewa har yanzu INEC ba ta shirya ba - ADC
Asalin hoton, ADC/X
Jam’iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta ƙalubalanci hukumar zaɓen ƙasar INEC, da ta bayyana inda ainihin hotunan takardun sakamakon zaɓe da aka ɗora a shafin hukumar suke, bayan da ta ce ta binciki takardun sakamakon zaɓen gwaji guda 37,712 ba tare da gano lokaci da kuma daga wajen da aka aika su ba.
Jam’iyyar ta bayyana damuwar cewa rashin irin waɗannan bayanai na iya sanya wahala a tabbatar da lokacin da aka ɗauki hotunan sakamakon zaɓen, inda ta ce alamu sun nuna cewa har yanzu INEC ba ta shiryawa babban zaɓen 2027 ba.
Ta kuma buƙaci INEC ta gabatar da hujjojin da ke nuna cewa an adana ainihin bayanan yadda ya kamata kuma babu yiwuwar a sauya su a ɓoye.
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC, Phrank Shaibu, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce cibiyar sa ido kan zaɓe na jam’iyyar ya binciki takardun sakamako na gwaji guda 37,712 da ke kan shafin INEC zuwa ƙarfe 11 na safe ranar 29 ga Nuwamba, kuma bai gano bayanan da suka kamata ba.
Ya ce INEC na da alhakin tabbatar wa jama’a cewa ainihin hotunan sakamakon na nan yadda suke kuma za a iya bincikarsu yanda ya dace.
ADC ta yi gargaɗin cewa ingancin tsarin zaɓe na iya fuskantar barazana idan za a iya sauya alkaluman masu rajista da na sakamakon zaɓe lokaci guda ba tare da wata shaida da za ta nuna an yi sauyin ba.
Nijar ta ƙaƙaba takunkumi kan kamfanin mai na China CNPC
Asalin hoton, REUTERS/SCANPIX
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sanar da kakaba takunkumai kan kamfanonin mai na China uku, wato China National Petroleum Corporation (CNPC) da rassan kamfanin na WAPCO da SORAZ, saboda gaza cika sharuɗan da aka cimma na bunƙasa samar da mai.
Wata sanarwa da sojojin suka mulkin suka fitar kuma aka karanta a babban gidan talabijin na ƙasar, ta ce kamfanin man na China ya kasa cika alkawarin da aka cimma da shi a watan Mayun 2026 na samarwa da kuma fitar da mai.
Ministan harkokin wajen ƙasar, Bakary Yaou Sangaré, wanda ke jagorantar kwamitin tattaunawa kan batun man fetur, ya ce wannan mataki ya zo ne bayan karewar wa'adin kwanaki 45 da aka bai wa kamfanin a watan Oktoban 2026.
Gwamnatin Nijar ta shiga takun tsaka da kamfanonin sama da shekara biyu da suka wuce, inda aka ƙori shugabannin kamfanin da wasu ma'aikata daga ƙasar.
A yanzu, Nijar ta buƙaci kamfanonin su mayar da kuɗaɗen shiga da suka samu daga fitar da mai a ƙasar tun 2024, wanda gwamnatin ta ce ya kai sama da dala biliyan 5.
Yadda jima'i ke ƙara fita daga ran matasa - Bincike, Michelle Roberts, Editan lafiya na dijital
Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike ya nuna cewa al'ummar Birtaniya, musamman matasa, na yin jima'i a ƙasa da yadda al'ummomin da suka gabace su ke yi, ko kuma ba sa yin sa kwata-kwata, duk da cewa da yawa daga cikinsu na kallon fina-finan batsa da kuma aika wa juna saƙonni ko hotunan batsa ta intanet.
Wannan ne karon farko da binciken da aka fi sani da Natsal, wanda ke nazarin rayuwar jima'i ta al'ummar Birtaniya, ya haɗa tambayoyi kan yadda mutane ke amfani da intanet wajen mu'amalarsu ta jima'i.
Binciken ya nuna cewa rabin mutanen da shekarunsu ke tsakanin 16 zuwa 24 sun aika ko kuma sun karɓi hotunan batsa ta wayoyinsu a cikin shekarar da ta gabata.
Yaƙin Sudan na ƙara tsananta matsalar ƙarancin abinci a ƙasar - MDD
Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yaƙin da ake yi a Sudan da kuma fari da aka daɗe ana fama da shi, na ƙara tsananta matsalar ƙarancin abinci, lamarin da ke jefa mutane da dama cikin yunwa.
Farashin kayan abinci ya ninƙa fiye da sau biyu cikin shekara guda da ta gabata.
Rashin isasshen ruwan sama ya lalata amfanin gona, wanda ya tilasta wa iyalai da dama barin gidajensu domin neman abinci da sauran hanyoyin rayuwa.
MDD ta ce faɗa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF ya kawo cikas ga samar da man fetur.
Haka kuma, hare-haren jirage marasa matuƙa da aka kai kan ababen more rayuwa sun haddasa katsewar wutar lantarki da ruwa a sassa da dama na ƙasar.
WHO ta yi kira ga Amurka ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Cuba
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Ghebreyesus, ya yi kira ga Amurka da ta janye takunkuman tattalin arzikin da ta ƙaƙaba wa Cuba.
A wani saƙo da ya wallafa a shafukan sada zumunta bayan ziyarar da ya kai ƙasar, Tedros ya ce ya ga yadda ma'aikatan lafiya ke kula da yara a asibitoci duk da ƙalubalen da suke fuskanta.
Amurka dai ta ƙara tsaurara takunkumanta kan Cuba, ciki har da ƙarin takunkumai da hana shiga da mai.
Lamarin ya yi matuƙar tasiri ga tattalin arzikin ƙasar tare da janyo yawaitar katsewar wutar lantarki.
Gwamnan Plateau ya gargaɗi masu hannu a kai hare-hare jihar
Asalin hoton, X/Caleb Mutfwang
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya gargaɗi mutanen da ke da hannu a kashe-kashe da sauran ayyukan ta'addanci a jihar cewa, gwamnatinsa a shirye take ta yi amfani da dukkan karfin da take da shi domin murkushe su.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Jos yayin bikin yaye jami'an tsaron dazuka 1,000 da aka horas, karkashin shirin horas da jami'an tsaron dazuka na shugaban Najeriya, wanda tsari ne na haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.
Mutfwang ya ce shirin na daga cikin tsare-tsare na ɓangaren tsaro na shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa ɗaukar aiki da horar da jami'an zai taimaka wajen karfafa ayyukan tsaro, musamman a yankunan da ake yawan kai hare-hare da kuma cikin dazuka.
Gwamnan ya yaba jami'an da aka ɗora wa alhakin tsaron al'umma, yana mai cewa sadaukarwar da suka yi ba za ta tafi a banza ba.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa shekaru da yawa na sakaci, rashin kula da kuma rashin haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, ya bai wa ɓata-gari damar cin karensu babu babbaka.
Sai dai ya yi watsi da batun cewa rikicin da ake fama da shi a Filato rikicin makiyaya da manoma ne kaɗai, inda ya ce wasu daga cikin hare-haren na da nufin yi wa jihar zagon ƙasa.
Mutfwang ya zargi wasu ƙungiyoyin 'yanbindiga da ke kai hare-hare a arewaci da kuma tsakiyar Filato, da fitowa daga wajen jihar domin addabar al'ummomi, kashe mazauna yankuna da kuma kwace filayensu.
Ambaliya ta shafi mutum sama da miliyan ɗaya a Peru
Asalin hoton, Getty Images
Mamakon ruwan sama na ci gaba da addabar arewacin ƙasar Peru, inda hukumomi suka ce yanzu sama da mutum miliyan ɗaya ne abin ya shafa.
Sun yi gargaɗin cewa akwai barazanar zaftarewar ƙasa baya ga ambaliyar ruwa da ta mamaye birane da dama.
Jami'ai sun fara raba ruwan sha a kwalabe da tankokin ruwa bayan lalacewar wasu cibiyoyin tace ruwan kasar.
Mazauna biranen da lamarin yafi ƙamari sun ce ba a kula da magudanan ruwa yadda ya kamata ba.
Sun kuma buƙaci Shugabar ƙasar, ta cika alkawarin da ta yi na ziyartar yankunan da ambaliyar ta shafa.
Jami’ar Northwest ta haramta wa ɗalibai bai wa malamai kyautuka
Asalin hoton, Northwest University Kano
Jami’ar Northwest da ke jihar Kano ta haramta wa ɗalibai da malamai daga bayarwa ko kuma karɓar kyautuka a tsakaninsu, inda ta yi gargadin cewa duk wanda aka samu da laifin karya wannan umarni zai fuskanci hukunci.
Jami’ar ta bayyana wannan ɗabi’a ta bayar da kayutuka a matsayin cin hanci da kuma babban laifi na rashin ɗa’a, tana mai jaddada cewa haramcin ya shafi ma’aikata da ɗalibai baki ɗaya, ba tare da la’akari da manufar bayar da kyautar ba.
Rajistra na jami’ar, Isyaku Adamu, ne ya sanar da haramcin cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu ɗalibai sun bai wa malamai kyaututtuka da sunan karrama su a matsayin waɗanda suka hazaƙa.
A cewarsa, irin wannan ɗabi’a na iya lalata martabar jami’ar tare da saɓa wa tanade-tanaden dokokin aikin jami'ar na 2025 da aka yi wa garambawul.
Jami’ar ta bayyana karara cewa bayarwa da karɓar kyautukan yana a matsyain cin hanci da zai iya ɓata ƙimar ta.
“Saboda haka, duk wani ma’aikaci ko ɗalibin da aka samu yana bayarwa ko karɓar kyauta za a tuhume shi da aikata babban laifi. Kuma za a ɗauki mataki nan take kan malami ko ɗalibin da aka samu da laifi," in ji Adamu.
Netanyahu na shirin ganawa da babban abokin hamayyarsa Eisenkot
Asalin hoton, EPA/ Reuters
Firaministan rikon ƙwarya na Isra’ila, Benjamin Netanyahu, zai gana da babban abokin hamayyarsa, Gadi Eisenkot, a safiyar Lahadi.
Ana sa ran za su tattauna yiwuwar kafa gwamnati bayan zaɓen watan da ya gabata wanda bai samar da cikakken rinjaye ba.
Ganawar za ta gudana ne a wani otal da ke bakin teku kusa da Tel Aviv, bayan da Netanyahu ya ba da shawarar miƙa ragamar mulki na ɗan lokaci ga Gadi a wata gwamnati ta haɗin kai.
Wakilin BBC ya ce an kasa samun wanda ya yi rinjaye tsakanin Netanyahu da Gadi a zaɓen da aka gudanar watan da ya gabata.
Sifaniya na gudanar da babban zaɓe a yau Lahadi
Asalin hoton, EPA
Al'ummar Sifaniya na kaɗa ƙuri'a yau Lahadi a wani zaɓen gaggawa da Firaministan kasar Pedro San-ches ya nemi a yi bayan majalisa ta yi watsi da wasu matakan gaggawa da gwamnatinsa ta gabatar domin magance matsalolin muhalli.
Sai dai kuri'un jin ra'ayin jama'a na nuna cewa jam'iyyarsa ta Socialist na iya fuskantar rashin nasara, yayin da ake alakanta gwamnatin da zarge-zargen cin hanci da kuma wasu munanan haɗurran jirgin ƙasa da suka faru kasar.
A ranar Juma'a, Sanchez ya shaida wa magoya bayansa cewa har yanzu suna da damar yin nasara.
Masu nazarin siyasa dai na hasashen cewa jam'iyyar People's Party za ta karɓi mulki tare da goyon bayan jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Vox.
Buɗewa
Masu bibiyar mu barkan mu da warhaka.
Ku kasance da mu a wannan shafi domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta da kuma sauran sassan duniya.
Za ku iya tafka muhawara kan labaran da muke kawo muku a shafukan mu na sada zumunta.