Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Talata 19/05/2026

  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman Minjibir

  1. Wani Sanatan Republican ya raba gari da gwamnatin Trump

    Wani babban jigo a Republican kuma ɗan majalisar dattawa a Amurka ya raba gari da gwamnatin Trump kan asusun diyyar rage raɗaɗi ga waɗanda gwamnatin da ta gabata ta musgunawa.

    John Tunnn ya shaida wa manema labarai cewa bai gamsu da matakin ba saboda bai ga wani dalilin yin hakan ba.

    Ƴan Democrats sun kira kuɗaɗen da waɗanda aka ɓoye domin raba wa abokan siyasar Trump ba bisa ƙa'ida ba.

    Sai dai mataimakin shugaban Amurkar, JD Vance ya kare matakin inda yake cewa ba gwamnatin Trump ko shi kansa Trump ko iyalan shi za a bai wa kuɗin ba.

  2. Tattaunawar Amurka da Iran na samun tagomashi - JD Vance

    Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance ya ce tattaunawar Amurka da Iran na samun tagomashi, saboda dukkan ɓangarorin ba su son koma wa yaƙin.

    Mista Vance ya ce ana daf da cimma matsaya kan batun mallakar makamin Nukiliiya ga Iran.

    Ya ce shugaba Trump na son a yi tattaunawar cikin aminci, sai dai yace akwai yiyuwar ɗaukar matakin soji idan aka gaza cimma matsaya.

  3. Pantami ya janye daga takarar gwamnan jihar Gombe

    Pantami

    Asalin hoton, Professor Isa Ali Ibrahim Pantami/X

    Tsohon ministan sadarwa na Najeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye daga zaɓen fitar da gwani na gwamnan Gombe na jam’iyyar APC.

    Cikin wani saƙo da Farfesa ya wallafa a shafukansa na sada zumunta ya ce ya ɗauki matakin ne bayan zargin jam’iyyar da karya dokar zaɓe da kuma rashin bin ƙa’idojin gudanar da zaɓen.

    Farfesa Pantami ya ce ya fice daga zaɓen fitar da gwanin da ake sa ran gudanarwa ranar 21 ga Mayu “cikin nuna rashin amincewa da tsarin da aka yi”.

    Ya ci gaba da cewa shugabannin jam’iyyar sun kasa yin bayani a kan yadda aka tsara zaɓen cikin aminci.

    Ya ce an yi watsi da buƙatun da ya gabatar domin neman bayanai kan yadda za a tantance wakilai, da tsarin kaɗa ƙuri’a da wuraren tattara sakamako.

    Pantami ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan tuntuɓa da magoya baya da masu ruwa da tsaki, sakamakon abin da ya kira rashin gaskiya da kura-kurai a zaɓen fitar a gwani na ‘yan takarar majalisar dokoki da APC ta gudanar a jihar kwanan nan.

  4. Sojojin Najeriya sun ce sun kashe mayaƙan ISIS 175

    Rundunar sojin Najeriya ta ce bayanan da ta samu bayan hare-hare da ta ƙaddamar tare da haɗin gwiwar sojojin Amurka a ƙarshen mako ya kashe mayaƙan ƙungiyar ISIS 175.

    Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan adadi ko kuma bayanan waɗanda aka kashen.

    A ranar Juma'a ne shugabannin ƙasashen Amurka da Najeriya suka bayyana kashe wani kwamandan IS, mai suna Abu-Bilal al-Minuki da wasu mayaƙansa a wani hari ta sama da sojojin ƙasashen biyu suka kai gidansa a tafkin Chadi.

    A farkon wannan wata ne sojojin Najeriya suka musanta rahotonnin kisan fararen hula a wasu hare-hare daban-daban a yankunan arewa maso gabasa da arewa maso yammacin ƙasar.

    Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran gudanar da bincike game da batun.

  5. An faɗa wa Tinubu cewa na kitsa kashe shi bayan mun fara mulki - Shettima

    Kashim Shettima

    Asalin hoton, Kashim Shettima/X

    Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya bayyana yadda ya ce wasu suka yi ƙoƙarin haɗa shi da shugaban ƙasa Bola Tinubu, wata uku bayan fara mulkinsu.

    Yayin da yake jawabi a wani taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar tsohon shugaban ƙasar, Janar Yakubu Gowon a Abuja, babban birnin ƙasar, Shettima ya ce wasu mutane da bai ambaci sunayensu ba, waɗanda ya ce daga jiharsa ta Borno suke sun faɗa Shugaba Tinubu cewa Shettiman na kitsa kashe shi domin karɓar mulki.

    “Bayan wata uku da kama mulkinmu, wasu mutane suka faɗa wa Tinubu cewa ina kitsa yadda zan kashe shi domin na karɓi mulkin ƙasar. Daga nan sai ya kirani ya ce zauna mutanenka sun zo sun faɗa min cewa na daina saka tufafin da Shettima ya bani.''

    “Sai dai da kansa Shugaba Tinubun ya ce min bai yarda da labarin nasu ba, saboda lokacin da ka bani tufafin ina matsayin ɗantakara ne, ban ma ci zaɓen fitar da gwani ba, ballanta ka zama mataimakin shugaban ƙasa'', in ji shi.

    Ya ce wasu mutanen sun faɗa wa Tinubun cewa ina shirin amfani da tufafiun domin kashe shi.

    ''Kuma Shugaban ya saka tufafin bayan hakan saboda bai yi imani da hakan ba.''

  6. An dakatar da yajin aikin da direbobin motocin haya suka shiga kan tsadar mai a Kenya

    An dakatar da yajin aikin da direbobin motocin haya suka shiga sakamakon tsadar mai a Kenya, an bada mako guda ne domin ba direbobin damar tattaunawa da gwamnati.

    Hukumomi sun ce an dauki matakin ne saboda shawo kan zanga-zangar da ke neman juyewa ta zama tarzoma daga jiya zuwa yau.

    An samu ƙarin farashin mai da kusan kashi hamsin lamarin da hukumomin ƙasar suka danganta da yaƙin Iran.

    A jiya Litinin an kama daruruan masu zanga-zangar yayin da mutum hudu suka rasu.

    An ga motocin da ba na haya ba na tafiya bisa tituna sai dai suna takatsantsan saboda jiya an kone mota da ta yunkurin wucewa.

  7. Za a daina ɗaukar fasinjojin jirgin ƙasa kyauta a Tehran daga gobe

    Wani mai magana da yawun Majalisar Birnin Tehran na Iran ya ce daga gobe, ranar Laraba, za a daina ɗaukar fasinjojin jirgin ƙsa da na bas ɗin BRT kyauta, inda farashi zai koma yadda yake a tsarin da ake bi kafin rikici.

    Alireza Nadali ya ce an amince da shirin “gyaran tsarin tikitin sufuri” a taron majalisar, sannan an tura shi zuwa kwamitoci na musamman domin ƙarin nazari.

    Ya bayyana cewa shirin ya samu amincewar mambobin majalisa 13 bayan an gabatar da shi da sa hannun mambobi 10 a zaman da aka yi yau.

    Ya ƙara da cewa har sai an kammala cikakken nazari kan wannan shiri, batun ci gaba da ɗaukar fasinjoji kyauta ba zai ƙara kasancewa a ajanda ba.

  8. MSF ta ce hare-hare sun hana dubban mutane samun kulawar lafiya a Sudan ta Kudu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar likitoci ta MSF ta yi gargaɗi cewa halin da ake ciki a Sudan ta Kudu yana ƙara ƙazancewa daidai lokacin da ake samun rahotannin hare-hare kan farar hula.

    Wani raho daga MSF ya ce hare-hare kan ma'aikatanta 12 da wasu cibiyoyinta sun sa farar hular Sudan ta Kudu 760,000 ba sa samun kulawa asibiti.

    An kai hare-haren ne tsakanin Janairun 2025 zuwa Aprilun 2026.

    Sudan ta Kudu ta faɗa yaƙi ne bayan da yarjejeniyar zaman lafiyar 2018 ta rushe. Rikicin mulki tsakanin Shugaba Salva Kiir da Riek Machar ya janyo tashin hankali a ƙasat.

    Machar a yanzu yana fuskantar shari'a kan tuhume-tuhumen kisa da cin amanar ƙasa da aikata laifuka kan bil adama, zarge-zargen da ya musanta.

    MSF ta zargi gwamnati da ɓangaren hamayya da kai hare-hare kan farar hula musamman a jihar Jonglei.

    A wani rahoto, ƙungiyar ta ce gwamnati ta toshe damar MSF ta shiga garin Akobo inda ƙungiyar ke tafiyar da ɗaya daga cikin asibitocin.

    A cewar ƙungiyar, hare-hare 138 aka kai a ƙasar a 2025, lamarin da ya sa dubban mutane suka ji rauni.

  9. EFCC ta kama Saleh Mamman da aka yankewa hukuncin shekara 75

    ...

    Asalin hoton, Sale Mamman/X

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta kama tsohon Ministan Lantarkin ƙasar, Saleh Mamman, wanda kotun tarayya da ke Abuja ta riga ta yanke masa hukunci shekaru 75 a gidan yari kan laifin almundahana.

    Rahotanni sun ce an kama shi ne a jihar Kaduna tare da wasu mutane biyu da ake zargin suna kare shi.

    A yanzu haka, ana gudanar da bincike a gidan da aka kama shi domin gano ƙarin bayanai game da lamarin.

    A ranar Laraba, 13 ga watan Mayu, 2026 ne dai babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa Saleh Mamman hukuncin shekara 75 a gidan yari a kan zargin satar kuɗi sama da naira biliyan 33 da ake cewa ya aikata yayin da yake riƙe da mukaminsa.

    Kotun ta ce ta same shi da laifuka 12 da EFCC ta gabatar, waɗanda suka haɗa da haɗa baki, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma almundahana.

    An yanke masa hukuncin ne a lokacin da ba ya gaban kotu, bayan shari’ar da ta dade ana yi kan zargin da ake masa tun lokacin da yake minista.

  10. Ana buƙatar ƙarin lokaci a tattaunawar Iran da Amurka - Qatar

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta ce tattaunawar tsakanin Amurka da Iran na bukatar ƙarin lokaci kafin a cimma matsaya.

    Mai magana da yawun ma’aikatar, Majid Al-Ansari, ya ce Qatar na goyon bayan ƙoƙarin diflomasiyya na Pakistan, wanda ya nuna aniyar haɗa ɓangarorin domin samun mafita, kuma hakan na buƙatar ƙarin lokaci.

    A wani taron manema labarai da ya gudana ranar Talata, ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin shawo kan rikicin ta hanyar tattaunawa maimakon rikici.

    A jiya kuma, Donald Trump ya bayyana cewa ya soke wani harin da ya shirya kai wa Iran, bayan buƙatar shugabannin Saudiyya da UAE da Qatar.

    Ya ce shugabannin ƙasashen uku sun yi imanin cewa za a iya cimma yarjejeniya wadda za ta zama abin karɓa ga Amurka da kuma ƙasashen yankin.

  11. Gwamnoni da wasu sanatocin da suka samu takarar majalisar dattawa

    ..

    Asalin hoton, BBC COLLAGE

    Jam'iyyar APC mai mulki ta kammala zaɓen fidda gwani na ƴan majalisar dattawa da za su fafata a babban zaɓen kasar na 2027.

    Kuma kamar yadda aka gudanar da na majalisar wakilai, shi ma na majalisar dattawa ya zo da mamaki kasancewar wasu manyan ƴan majalisar dattawan ba su kai bantansu ba kasancewar gwamnoni masu ci da suka kammala wa'adinsu biyu sun maye gurbinsu.

    BBC ta tattaro sunayen da suka fi yin fice da suka tsallake da wadanda ba su kai ga gaci ba, kamar haka:

  12. An ceto ƴan Mali 30 daga hannun masu safarar mutane a Nasarawa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta tarwatsa wata ƙungiyar masu safarar mutane da ke gudanar da ayyukanta a Abuja, babban birnin ƙasar da wasu yankuna maƙwabta.

    Hakan ya sa ƴansanda suka kuɓutar da mutum 30 ƴan asalin Mali da ake zargin an tsare su a jihar Nassarawa.

    A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar, Anthony Placid ya fitar, jami'an sun bankaɗo wasu ayyukan ƙungiyar a wani gida da ke Mararraba da Karu inda ake zargin an killace su.

    Ƴansanda sun ce an kama mutum 13 da ake zargi suna da hannu a ƙungiyar.

    A cewar ƴansanda, an soma bincike ne bayan da aka samu bayanan sirri kan ɓacewar baƙi da dama a Najeriya.

    Placid ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar tana yaudarar matasa daga ƙasashe irinsu Mali da Gabon inda suke yi musu alƙawarin ayyukan yi a Najeriya da kuma damar tsallakawa zuwa Turai.

  13. An dakatar da yajin aiki kan tashin farashin mai a Kenya

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    An dakatar da yajin aiki a Kenya da aka kira saboda tashin farashin man fetur domin bayar da damar tattaunawa tsakanin gwamnati da masu harkar sufuri.

    An dakatar da yajin aikin na tsawon mako guda saboda kawo maslaha a matsalolin da aka gani bayan shiga rana ta biyu ta yajin aikin, lamarin da ya sa afa ta ɗauke a birane da garuruwa.

    Tattaunawar da aka shafe dare ana yi da masu motocin tasi ta tashi baram-baram a jiya Litinin.

    Farashin mai ya ƙaru da kusan kashi 50 sakamakon matsalolin da aka fuskanta wajen samar da shi da ke da alaƙa da yaƙin Iran.

    Tashin hankalin da aka gani a ranar Litinin ya janyo mutuwar mutum huɗu.

  14. Ɗanbindiga ya halaka mutum takwas a Al Ƙahira

    Wani ɗanbindiga ya halaka mutum takwas tare da raunata mutum biyar a Lardin Asyut da ke kudancin Al Ƙahira da ke Masar.

    Ɗanbindigar wanda ya kai harin na ranar Litinin, kamar yadda rahotanni suka cem ya buɗe wuta a wani wata cibiyar sufuri.

    Ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ta ce jami'an tsaro sun gano mutumin bayan ya tsere zuwa wata gona inda suka harbe shi sakamakon musayar wuta.

  15. Hisbah ta kama wani kan zargin 'yin soyayya' da matar aure

    Jami'an hukumar Hisbah a jihar Kebbi sun cafke wani mutum da ya ɓuya cikin jakar Ghana Must Go a gidan wata matar aure a yankin Badariya a Birnin Kebbi.

    Daraktan shari'a a hukumar, Sirajo Kamba ne ya tabbatar da kame mutumin a wata sanarwa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    A cewar Kamba, mazauna yankin sun ankarar da Hisba ne a ranar 18 ga watan Mayu bayan da suka gano wani mutum yana shiga gidan matar.

    "Mazauna unguwar sun yi zargin akwai mu'amalar da ta saɓa shari'ar musulunci tsakanin mutanen biyu, abin da ya sa suka sanar da hukuma.

    "Da samun rahoton ne kuma, hukumar Hisba ta jihar Kebbi ta aike da jami'anta zuwa gidan matar.

    Daraktan ya ce a lokacin da jami'an suka isa gidan, sun nemi su yi bincike a gidan sai dai matar ta ƙi bayar da dama inda ta musanta cewa babu kowa a cikin gidan.

    Daraktan ya kuma ce daga bisa ni ne matar ta amince a yi bincike lamarin da ya sa aka gano wanda ake zargi cikin wata jakar Ghana Must Go.

    Ya ƙara da cewa binciken da aka zurfafa ya nuna cewa akwai alaƙa ta soyayya tsakanin matar mai aure da kuma mutumin.

    Kamba ya ce masoyan sun tabbatar da zargin da ake musu inda ya ce za a gurfanar da su gaban kotu domin fuskantar shari'a bisa tanadin musulunci.

  16. Na janye ƙudirin sake kai wa Iran hari saboda ƙasashen Gulf - Trump

    ..

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya janye ƙudirin kai wa Iran hari jiya Talata saboda ƙasashen yankin Gulf sun buƙaci hakan yayin da ake muhimmiyar tattaunawar sulhu.

    A wani saƙo da ya wallafa a Truth Social, Trump ya ce shugabannin Qatar da Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ne suka buƙaci ya sauya matsaya kan harin.

    Ya ce ba a sanar da shi za a cimma wata yarjejeniya da Amurka za ta amince da ita ba inda ya ƙara da cewa Iran ba za ta mallaki makamin nukiliya ba.

    Sai dai ya gargaɗi cewa Amurka za ta zama a shirye ta kai gagarumin hari kan Iran idan har ba a cimma wata yarjejeniya ba.

    Wani babban kwamandan soji a Iran ya shaida wa Amurka cewa da ta guji sake yin kuskure.

    A ranar 28 ga Fabarairu ne sojojin Isra'ila da Amurka suka ƙaddamar da hare-hare ta sama ikan Iran yayin da Iran ɗin ta mayar da martani ta hanyar harba jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan wasu cibiyoyin Isra'ila da Amurka a sassan Yankin Gulf.

  17. Ukraine ta ƙaddamar da harin jirage mara matuƙa kan Rasha

    ...

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Yankuna da dama na ƙasar Rasha sun ce sun fuskanci hare haren jiragen sama marasa matuƙa na Ukraine.

    Magajin garin Moscow ya ce sun yi nasarar kakkaɓo huɗu daga irin waɗannan jirage da aka hari babban birnin da su.

    Can a yankin Yaroslavl na arewa maso gabas, gwamnan yankin ya sanar da hare haren jiragen da ya bayyana na abokan gaba - Ukraine.

    Ya ce an kai ga dakatar da motoci da sauran ababan hawa a kan titin da ya nufi Moscow, sannan kuma ya buƙaci jama'a da su guji bin wannan hanya.

    Can ma a yankin kudu maso yamma, a kusa da iyaka da Ukraine, gwamnan Rostov ya ce sun kakkaɓe hare-haren jiragen marasa matuƙa.

  18. WHO ta nuna damuwa kan bazuwar cutar Ebola a Congo

    ...

    Asalin hoton, Jospin Mwisha / AFP via Getty Images

    Hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta ce a duk lokacin da ta faɗaɗa bincikenta a kan ɓarkewar cutar Ebola a gabashin jamhuriyar Dumukuradiyyar Congo, sai ta gano shedar cewa lalle cutar ta bazu.

    Wakilin BBC ya ce, wani kuma abin damuwa shi ne, a yanzu ta bazu zuwa yankin da ke da yawan jama'a sosai.

    Hukumomin ƙasar ta Kongo sun ce a yanzu mutanen da cutar ta hallaka sun kai sama da 130 - kuma ana samun ƙaruwar mutanen da suka kamu da cutar.

    To amma kuma gwamnatin ƙasar ta ce akwai jami'ai da ke aiki ba dare ba rana domin gano waɗanda ake ganin sun kamu ko sun yi mu'amala da waɗanda suka kamu.

    Hukumar ta lafiya ta buƙaci jama'a da kada su firgita.

    WHO, ɗin ta ce tana ƙoƙarin ganin ta daƙile bazuwar cutar ne ta hanyar taƙaita zirga-zirgar jama'a, da kuma faɗakar da mutane kan janaizar waɗanda suka rasu, ta hanyar da ta dace don gudun yaɗa cutar.

  19. Matasa sun harbe mutum uku a harin masallaci a San Diego

    ..

    Asalin hoton, EPA

    Wasu matasa biyu sun harbe mutum uku maza a wani masallaci da ke San Diego a California ta Amurka a wani hari da ake zargi na nuna ƙiyayya ne, kafin daga bisani su ɗauki rayuwarsu, kamar yadda ƴansanda suka bayyana.

    Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, sa'oi biyu bayan da mahaifiyar ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ta kira ƴansanda don shaida musu cewa ɗanta ya gudu tare da wani abokinsa kuma da alamu yana tunanin kashe kansa.

    Ƴansanda sun bazama neman matasan biyu lokacin da harin na San Diego ya soma inda suka samu mutum uku da raunuka sanadin harbin bindiga a wajen ginin.

    Jim kaɗan bayan nan sun sake samun wani kiran wayar cewa an ji ƙarar harbin bindiga daga wata mota. Ƴansan sun gano waɗanda ake zargi a mace - masu shekara 17 da 18 cikin wata mota nesa da masallacin.

    Daga cikin matasan akwai wani mai samar da tsaro da ke aiki a masallacin kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen kare harin daga munanana, kamar yadda jami'ai suka ce.

    Hukumomi zuwa yanzu ba su tabbatar da sunayen mutanen ba sai dai mai samar da tsaro a masallacin mahaifi ne ga yara takwas, in ji wani da ya san shi wanda ya faɗa wa CBS.

  20. Maraba

    Masu bibiyar wannan shafi na Kai Tsaye, barka da warhaka. Da fatan mun wayi gari cikin ƙoshin lafiya.

    Kamar kullum, za mu ci gaba da kawo maku labarai kan yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Kuna kuma iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo da tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.