Jarumar fim ɗin Wasila ta rasu
Jarumar fina-finan Hausa na Kannywood Wasila Isma'il ta rasu, kamar yadda makusantanta suka tabbatar.
Makusantan marigayiyar sun ce ta rasu ne a jihar Kaduna da safiyar yau Lahadi bayan fama da rashin lafiya.
Ta rasu tana da kimanin shekaru 46, inda ta bar ƴaƴa hudu - mata uku da namiji ɗaya.
Marigayiyar na daga cikin tsoffin jarumai a Kannywood, inda ta samu karɓuwa sosai bayan da ta fito a wani fim mai suna Wasila da ya shahara shekaru sama da 10 da suka wuce, kuma ta fara fara harkar fim ne a 1998.
Jarumar ta yi aiki da gidan rediyon Liberty a Kaduna.