Za mu ci gaba da rufe tasoshin ruwan Iran har sai an kammala cimma matsaya - Trump

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce sojojin ƙasar za su ci gaba da datsewar da suke yi wa tasoshin ruwan Iran har sai an kammala cimma matakin ƙarashe na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ƙasashen biyu.
Tun da farko Shugaba Trump ya ce an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ƙasashen, yayin da ake tattauna matakin ƙarshe na yarjejeniyar.
''Za mu ci gaba da rufe tasoshin ruwansu har sai an kammala cimma matsaya, kowane ɓangare ya amince aka kuma sanya hannu'', in ji shi.
"Ba za mu yi kuskure ba, dangantakarmu da Iran za ta ci gaba da zama mai muhimmanci. Kuma ina so su fahimci cewa ba za su taɓa ƙera makamin nukiliya ba'', in ji Shugaba Trump.





















