Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi 26 ga watan Yulin 2026.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Brazil ta hana ƴan Amurka masu sa ido kan zaɓe bizar shiga ƙasar

    Wasu rahotanni sun ce Brazil ta ƙi ba wasu jami'an Amurka biyu biza, waɗanda suka shirya zuwa kasar domin duba aka shirya yin zaben kasar wanda za a yi a watan Oktoba.

    Majiyoyin diflomasiyya sun ce jami'an na son nuna shakku kan sahihancin tsarin zaɓen Brazil, zargin da Amurka ta musanta zargin, inda ta bayyana shi a matsayin "ƙarya marar tushe".

    A zaɓen da ke tafe, Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva (Lula) zai fafata da Flavio Bolsonaro, wanda jam'iyyar Liberal mai ra'ayin mazan jiya ta amince da shi a hukumance a matsayin ɗan takararta a ranar Asabar.

    Flavio Bolsonaro na daga cikin abokan siyasar Shugaban Amurka Donald Trump, kuma ya sha bayyana shakkunsa kan amincin tsarin zaɓen da ake yi ta hanyar na'urar kwamfuta a Brazil din.

    Mahaifinsa, tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro, na zaman hukuncin daurin kurkuku bayan an same shi da laifin shirya wani yunkurin juyin mulki, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

  2. Ana ci gaba aiki ceto waɗanda gobarar dajin Spain ta rutsa da su

    Firaministan Sifaniya, Pedro Sánchez, ya ce 'yan kwana-kwana na ci gaba da aiki domin ceto rayuka yayin da gobarar daji ke ci gaba da ruruwa a yankunan da ke yammacin birnin Madrid.

    Sánchez ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara yankin da gobarar ta shafa, inda aka umarci sama da mutum 90,000 su fice daga gidajensu ko kuma su zauna a cikin gidajen ba fita saboda matakan kariya.

    A babban birnin kansa, mazauna na sanya safar fuska tare da rufe tagogin gidajensu yayin da hayaƙi da kauri na gobarar ke bazuwa.

    A wani lamari daban, mutum daya ya rasu sakamakon wata gobarar a gabashin ƙasar. Gwamnatin kasar ta Sifaniya ta ayyana dokar ta-baci ta ƙasa, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin shawo kan gobarar.

    Ana kuma fatan cewa sauyin yanayi da ake sa ran samu nan gaba kaɗan zai taimaka wa jami'an agaji da na kashe gobara wajen dakile yaɗuwar wutar.

  3. Faransa ta umarci ƙarin mutum 55,000 su fice daga gidajensu saboda gobarar daji

    Hukumomi a kudu maso yammacin Faransa sun umarci karin mutum 55,000 da su fice daga gidajensu a yankunan da ke kusa da birnin Bordeaux, yayin da mummunar gobarar daji ke ci gaba da bazuwa.

    A yanzu, kusan mutum dubu 250 ne aka umarta su bar gidajensu saboda barazanar gobarar. Firaministan Faransa ya yi gargadin cewa yanayin da ba ya da kyau, ciki har da iska mai ƙarfi da tsananin zafi, na ƙara daburta ƙoƙarin da jami'an kashe gobara ke yi na shawo kan lamarin.

    Wakilin BBC ya ce rahotannin da aka bayar da farko ranar Asabar na cewa kila tsananin gobarar dajin da ke ta'annati a Faransa ya ragu.

    A wani mataki na musamman, gwamnatin Faransa ta tura wani katafaren jirgin sama na soji na dakon kaya karo na farko domin watsa sinadaran kashe gobara a yankunan da gobarar ta fi ƙamari a kusa da birnin na Bordeaux.

  4. Ƴansanda na neman matashin da ya kutsa taron masu neman jinsi a Jamus

    'Yan sanda a birnin Berlin na Jamus sun shafe dare suna neman direban wata mota da ta kutsa cikin taron mutane a ɗaya daga cikin manyan tarukan masu neman jinsi daya a Turai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mace daya da jikkata mutum 16.

    Wakilin BBC ya ce 'yansanda na amafani da jirgin sama mai saukar ungulu da fitilu masu haske a neman wanda ake zargin a cikin duhun wannan waje na tsakiyar Berlin.

    Hukumomi sun ce babban wanda ake zargin matashi ne mai shekara 21 mai suna Abdul B, kuma yana da alaka da masu tsattsauran ra'ayi na ikirarin jihadi.

    'Yan sanda sun kuma ce an caka wa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa wuƙa bayan aƙalla mutum ɗaya daga cikin maharan ya fito daga cikin motar kafin ya tsere daga wurin.

    Dubban mutane ne suka halarci taron na shekara-shekara na masu rajin kare haƙƙin masu neman jinsi daya, a babban birnin na Jamus, gangamin da ake wa lakabi da Christopher Street Day.

  5. Trump zai dakatar da yunƙurin faɗaɗa hare-hare a Iran

    Rahotanni da dama daga Amurka sun ce Shugaba Donald Trump ya yanke shawara, a halin yanzu aƙalla, kada ya ƙara faɗaɗa hare-haren sojin Amurka kan Iran.

    Rahotannin sun ce Trump ya ɗauki matakin ne shekaran jiya Juma'a, bayan da wasu jami'ai suka nuna damuwa game da raguwar makamai masu linzami na kariya na Patriot, masu tsada sosai, da kuma yiwuwar matakin ya haifar da saɓani tsakaninsa da ƙawayen Amurka na ƙasashen Larabawa da ke yankin Tekun Fasha.

    Har yanzu babu wata sanarwa a hukumance kan lamarin, sai dai Fadar White House ta ce Trump koyaushe ya fi son a warware matsaloli ta hanyar diflomasiyya.

    Daren Juma'a ne karo na farko cikin kusan mako biyu da ba a kai hare-haren sama na Amurka kan Iran ba. Haka kuma ba a kai irin waɗannan hare-hare ba a daren Asabar.

  6. Farawa

    Barka da zuwa shafin BBC Hausa na kai-tsaye wanda ke kawo muku labaran duk muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da saurarn sassan duniya a wannan rana ta Lahadi.

    Aisha Babangida ke sake fatan kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za kuma ku iya yin tsokaci a shafukanmun na sada zumunta: facebook, X, instagram, YouTube sai kuma zaurenmu na WhatssApp.