Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran al'amuran da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 04/09/2026.

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Haruna Ibrahim Kakangi ya zama sabon shugaban BBC Hausa

    Kafar yaɗa labarai ta BBC ta sanar da naɗa Haruna Ibrahim Kakangi a matsayin sabon shugaban sashen Hausa na BBC.

    Shugabar yankin Afirka na BBC, Juliet Njeri, ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma'a.

    Ta ce naɗin ya biyo bayan tantancewa wanda aka yi har zagaye biyu ana fafatawa tsakanin masu neman matayin.

    Haruna Kakangi ya fara aiki ne a kafar DITV/Alheri Radio, sannan daga bisani ya yi aiki da RFI da BBC Media Action da gidauniyar MacArthur Foundation, kafin daga bisani ya koma sashen Hausa na BBC Hausa.

  2. An kama dan tsohon shugaban ƙasar Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa kan zargin rashawa

    An kama dan tsohon shugaban ƙasar Sri Lanka, Mahinda Rajapaksa, kan zarginsa da hannu a binciken cin hanci da rashawa kan sayen jiragen sama na kamfanin Airbus a shekara ta 2013.

    An tsare Namal Rajapaksa ne bayan wani kwamitin da ke binciken zarge-zargen karɓar rashawa ya gayyace shi domin amsa tambayoyi.

    Ba a bayyana nan take irin tuhume-tuhumen da ake yi masa ba. Iyalan tsohon shugaban ƙasar sun musanta zarge-zargen cewa sun karɓi rashawa daga kamfanonin Turai dangane da sayen jiragen sama goma na kamfanin jirgin sama na kasar, wata yarjejeniya da ta buƙaci amincewar gwamnati.

  3. 'Iran na ƙoƙarin faɗaɗa alaƙa da China'

    Gholamhossein Mohseni-Ejei, shugaban ɓangaren shari’a na Iran, wanda ya ziyarci Indiya domin halartar taron shugabannin ɓangarorin shari’a na ƙasashe mambobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), ya bayyana a wata ganawa da babban alƙalin ƙasar China cewa: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran na da niyyar faɗaɗa alaƙar da ke tsakaninta da China.”

    Mista Ejei ya kuma ce: “Duniya na sauyawa zuwa wani sabon tsarin tafiyar da harkoki, kuma China na taka muhimmiyar rawa wajen wannan sauyi.”

    A cewarsa, an shirya gudanar da taron ƙolin ɓangaren shari’a na Kungiyar Hadin Kan Shanghai (SCO) a Iran a bara, amma aka sauya wurin gudanar da taron sakamakon yakin Amurka da Isra’ila da Iran.

  4. Rikici tsakanin Houthi da gwamnati ya yi ajalin mutum 122 a Yemen

    Rahotanni sun ce aƙalla mutum 122 sun mutu a wani sabon rikici tsakanin dakarun gwamnati masu samun goyon bayan Saudiyya da mayaƙan Houthi a Yemen.

    Rikicin ya ɓarke ne bayan da mayaƙan Houthi suka kaddamar da wani hari ta ƙasa a ranar Alhamis, da nufin ƙwace ikon wasu yankunan bakin teku da ke iyaka da mashigar Bab al-Mandeb a Tekun Bahar Maliya.

    Wakilin BBC ya ce Mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun shafe makonni suna kai hare-hare kan jiragen ruwan dakon mai na Saudiyya da ke amfani da wannan mashigar ruwa a madadin mashigar Hormuz.

    Wannan sabon rikici da ake yi a Yemen na nuna cewa dogon lokacin da aka shafe ana samun sauƙin rikicin ya kusa zuwa ƙarshe.

  5. "Yadda muka kama mata da ba Musulmi ba da hijabi suna satar yara a Abuja"

    Rundunar ƴan sandan Najeriya ta babbar birnin tarayya, Abuja ta ce ta sake damƙe wasu mata biyu, waɗanda ake zargi da sace ƙananan yara suna sayarwa.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron ke ƙorafin yawaitar sace-sacen ƙananan yara a babban birnin tarayyar da ma wasu sassan ƙasar.

    An fara kama matan guda biyu ne a shekarar 2025, bisa zargin satar wasu yara huɗu cikin har da ƴan biyu, aka gurfanar da su gaban kuliya, har ma aka yanke masu hukunci, amma bayan wata huɗu sai suka fito.

    SP Josephine Ade, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan a Abuja ta yi wa BBC bayani dangane da yadda al'amarin ya faru.

    Karanta cikakken labarin a nan: https://www.bbc.com/hausa/articles/cj9xe8wlzjjo

  6. Har yanzu ba mu yanke shawarar tura sojoji zuwa Mashigar Hormuz ba - Korea ta Kudu

    Ofishin shugaban ƙasar Koriya ta Kudu ya sanar cewa har yanzu ba a yanke wata shawara kan tura dakarun sojin ƙasar zuwa Mashigar Hormuz ba.

    Wannan na zuwa ne bayan wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai da suka ce Koriya ta Kudu na shirin aikewa da sojoji zuwa wannan muhimmiyar mashigar ruwa kafin ƙarshen shekarar nan.

    Sai dai ofishin shugaban ƙasar ya bayyana a yau cewa har yanzu ana gudanar da bincike da nazari kan lamarin, kuma ba a cimma matsaya ta karshe ba.

    Koriya ta Kudu na fuskantar matsin lamba daga shugaban Amurka Donald Trump da ya nemi ƙawayen Amurka su taimaka wajen tabbatar da tsaron Mashigar Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga safarar mai a duniya.

    Mashigar Hormuz na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ruwa da ake jigilar ɗanyen mai daga yankin Tekun Fasha zuwa kasuwannin duniya, lamarin da ya sa tsaronta ke da muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasashe masu dogaro da makamashi, ciki har da Koriya ta Kudu.

  7. Mun shirya fuskantar kowane irin ƙalubale - Iran

    Alireza Elhami, kwamandan Hedikwatar Tsaron Sararin Samaniya ta Haɗin Gwiwa ta Khatam al-Anbiya, ya ce Iran ta shirya tsaf domin fuskantar kowace irin arangama ta soja a yanzu da ma nan gaba.

    "Mun shirya kanmu domin kowace irin arangama a yau da kuma nan gaba, kuma za mu ci gaba da kasancewa cikin shiri."

    Elhami ya jaddada cewa, a mahangar Iran, barazanar ba ta ƙare ba.

    A cewarsa, sojojin kariyar sararin samaniya na rundunar sojin Iran da na IRGC sun ƙera wani sabon tsarin kariyar sararin samaniya a lokacin yaƙin baya-bayan nan, inda suka inganta shi, suka tura shi zuwa filin aiki, sannan suka yi amfani da shi.

    Ya ƙara da cewa kariyar sararin samaniyar ƙasar ta samu cikakkiyar dogaro da kai wajen samar da kayan aiki da tsarin da take buƙata, sakamakon amfani da ƙwarewar cikin gida, matasan masana kimiyya, kamfanonin fasaha masu dogaro da ilimi, jami'o'i da kuma gogewar da rundunonin sojin ƙasar suka samu a fagen aiki.

    A cewarsa, Iran yanzu tana da ikon samar da mafi yawan kayan aiki da tsarin kariyar sararin samaniya da take buƙata ta hanyar albarkatun cikin gida.

  8. EU ta bi sawun Amurka wajen killace tattalin arzikin Iran

    Sakataren Baitul Malin Amurka, Scott Besant, ya ce sanarwar ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashen G20, ta bayyana "Tarayyar Turai a hukumance ta shiga shirin killace tattalin arzikin Iran," inda ya ce Amurka "na yaba wa matsayinsu mai ƙarfi da kuma gaggawar ɗauka."

    Mista Besant ya rubuta a shafin sada zumunta na X cewa "Amurka ta yi tsayin daka tare da ƙawayenta domin tabbatar da cewa gwamnatin Iran, wadda muke kallon a matsayin mai aikata laifi, ba za ta iya amfani da tsarin kuɗi na duniya ba wajen tallafa wa burinta na nukiliya, shirye-shiryen makamai, da kuma ƙungiyoyin da take marawa baya.

    Sakataren Baitul Malin na Amurka ya jaddada cewa "Duniya na aikewa gwamnatin Iran da saƙo karara ba za mu tsaya ba har sai an yanke duk wata hanya ta ƙarshe da take samun kuɗaɗe ta cikinta."

    Kwana biyu da suka gabata, Hukumar Tarayyar Turai ta fitar da wata sanarwa a gefen taron ministocin kuɗi da gwamnonin manyan bankunan ƙasashen G20 da aka gudanar a Asheville, inda ta nuna goyon baya ga takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran.

  9. Abin da muka sani game da aikin ceton Nepal

    An ceto ma’aikata biyu da ransu daga tashar samar da wutar lantarki ta ruwa ta Trishuli 3A a Nepal, sama da mako guda bayan wata mummunar ambaliyar ruwa ta kwatsam ta afku a yankin tsaunukan Himalaya.

    Ga abin da aka sani game da ma’aikatan da aka ceto zuwa yanzu, An bayyana sunayensu da Sanjaya Shah da Kabir Maharjan. Hukumomi sun ce an kwashe su ta jirgin sama kai tsaye zuwa wani asibiti a birnin Kathmandu.

    Dukkansu suna da raunuka a hannuwa da ƙafafuwa, waɗanda hukumomi suka ce mai yiwuwa sun samu ne sakamakon rarrafe da suka yi a cikin ramin karkashin ƙasa.

    Ana sa ran za a ceto aƙalla wasu mutum 39 da ke cikin wannan ramin bayan masu aikin ceto sun ji muryoyinsu da sanyin safiyar ranar Juma’a.

    Hotunan bidiyo masu ban tausayi sun nuna lokacin da aka fito da ma’aikatan biyu zuwa waje cikin aminci.

    Har yanzu ana fargabar cewa sama da mutum 150 sun makale a wasu wuraren tashoshin samar da wutar lantarki ta ruwa a Nepal.

    Ɗan’uwan ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto ya ce zuciyarsa ta cika da farin ciki da jin daɗi bayan samun labarin cewa an same shi da rai.

  10. Koriya ta Kudu na shirin tura dakarunta mashigar Hormuz

    Kafofin yaɗa labarai na Koriya ta Kudu sun ruwaito cewa gwamnatin ƙasar na shirye-shiryen tura kayan aiki da sojoji domin tallafawa abin da ake kira “’yancin zirga-zirga a mashigin ruwa na Hormuz”, kuma tana shirin fara wannan aiki kafin ƙarshen shekarar nan.

    Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a ranar Alhamis 3 ga Satumba cewa rahotannin kafafen yaɗa labaran Koriya ta Kudu, waɗanda suka ambaci majiyoyin gwamnati da na soja, sun bayyana cewa Seoul na ɗaukar matakan doka da suka dace domin samun amincewar majalisar dokoki kan wannan tura sojoji.

    Bisa ga waɗannan rahotanni, gwamnatin ta tantance shirin a taron majalisar ministoci, tana shirin miƙa buƙatar amincewa a hukumance ga majalisar dokoki a cikin wannan wata.

    Yiwuwar tura sojojin Koriya ta Kudu na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro a mashigin Hormuz da hare-haren da ake kai wa jiragen kasuwanci suka ƙaru a cikin makonnin baya-bayan nan. Haka kuma, wasu ƙasashe da dama suna nazarin hanyoyin da za su shiga cikin ƙoƙarin kare tsaron harkokin sufuri ta ruwa a wannan muhimmin mashigin ruwa.

    Ya zuwa yanzu, jami’an gwamnatin Koriya ta Kudu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da waɗannan rahotanni.

  11. Mun yi kuka mun kuma yi murna sosai.......

    Matar ɗaya daga cikin ma’aikatan da aka ceto, Kabir Maharjan, mai suna Hirashova, ta shaida wa BBC Nepali irin farin cikin da take ciki bayan an gano mijinta da rai.

    Ta ce "Na ga hotunansa a Facebook. Na yi matuƙar farin ciki. Yanzu suna kawo shi Asibitin Sojoji da ke Kathmandu. Ni ma ina kan hanyata ta zuwa asibitin."

    Ta ƙara da cewa "Tsawon kwanaki 10 ba mu iya cin abinci ko shan ruwa yadda ya kamata ba. Mun kasance cikin tsananin fargaba. Yanzu kuma dukkanmu muna cikin farin ciki. Har ma muna kuka saboda murna."

    Maganganunta na nuna irin wahala, damuwa da tashin hankalin da iyalansu suka shiga a kwanakin da suka gabata, da kuma babban farin cikin da suka samu bayan da aka ceci Kabir da rai.

  12. Najeriya ta musanta hannu a yunƙurin juyin mulkin Nijar

    Najeriya ta musanta zarge-zargen cewa ita ko ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas sun goyi bayan wani yunƙurin juyin mulki da ake zargin an yi a ƙasar Nijar mai maƙwabtaka da ita.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana cewa zarge-zargen da ke yawo da su a shafukan sada zumunta “ba su da tushe bare makama, kuma wani yunƙuri ne na yaudarar jama’a da kuma ɓata sunan Najeriya.”

    Sanarwar ta biyo bayan zargin da wani kyaftin ɗin rundunar sojin Nijar ya yi cewa wasu gwamnatocin ƙasashen waje, ciki har da Faransa, Chadi da Côte d’Ivoire, da kuma mutanen da ke da alaƙa da hambararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, sun shirya tsoma baki cikin wani rikicin da ya faru a wani sansanin soja a birnin Niamey makon da ya gabata.

    Kyaftin Roger Gabriel, kwamandan Bataliya ta Farko ta Sojojin Saman Nijar, ya kuma yi zargin cewa shugaban ƙasar Benin, Patrice Talon, ya samu amincewar Ecowas domin shiga tsakani.

    BBC ta tuntubi gwamnatoci da mutanen da aka ambata a zargin domin neman bayani.

    Faransa ta ƙi cewa komai kai tsaye, amma ta shaida wa BBC cewa duk wani matakin tura sojojinta ƙasashen waje ana yin sa ne tare da haɗin gwiwar ƙasashen abokan hulɗarta.

    Babu dai wanda ya tabbatar da wannan zarge-zargen da Kyaftin Gabriel ya yi, sannan kuma bai gabatar da wata hujja ba a bainar jama’a da za ta tabbatar da ikirarinsa ba.

    Dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar ta yi tsami tun bayan da sojoji suka karɓi mulki a watan Yulin 2023 tare da hamɓarar da Mohamed Bazoum.

    A lokacin, Ecowas ƙarƙashin jagorancin shugaban Najeriya na wancan lokaci, Bola Ahmed Tinubu, ta yi barazanar amfani da ƙarfin soja idan gwamnatin mulkin soji ba ta dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba. Hukumomin sojin Nijar sun yi kakkausar suka ga wannan barazana, lamarin da ya ƙara lalata dangantakar ƙasashen biyu.

    Daga baya Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi, amma ƙungiyar ta cire su a shekarar 2024. Tun daga wannan lokaci Nijar ta fice daga Ecowas tare da Mali da Burkina Faso, kuma ƙasashen uku masu mulkin soja sun kafa nasu ƙawancen yankin.

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce ƙasar ta kasance tana adawa da duk wani canjin gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba.

    “Najeriya ba za ta taɓa goyon bayan karya doka ko sauyin gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba a ko’ina, komai wanda yake da hannu ko ƙasar da abin ya shafa,” in ji sanarwar.

    Ta ce tuni an fayyace matsayar Najeriya a wata sanarwa da aka fitar a ranar 30 ga Agusta bayan rikicin da ya faru a sansanin soja da ke Niamey.

    “Najeriya na kallon duk wani sauyin gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba da matuƙar damuwa. A matsayinta na maƙwabciya mai alaƙar tarihi, ‘yan’uwantaka da al’adu da Nijar, Najeriya ba ta fatan komai sai zaman lafiya, tsaro, dimokuraɗiyya da ci gaba ga Nijar, yankin da kuma Sahel baki ɗaya.”

    Ma’aikatar ta ce Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen goyon bayan matsayar Ecowas da Tarayyar Afirka na kin amincewa da karɓar mulki ta hanyar juyin mulki.

  13. Isra'ila ta saki 'yan ƙasar Lebanon biyar

    Isra’ila ta sanar da cewa za ta saki ‘yan ƙasar Lebanon biyar da ta tsare a kudancin Lebanon.

    A lokaci guda kuma, jami’an Lebanon sun sanar da cewa an miƙa mutum na farko daga cikin rukunin ga rundunar sojin Lebanon.

    Rundunar sojin Lebanon ta bayyana cewa an mayar da ɗaya daga cikin waɗanda ake tsare da su zuwa ƙasar ta hanyar sasancin ta hannun Red Cross.

    Wannan shi ne sakin farko tun bayan tattaunawar watan Agusta tsakanin Beirut da Isra’ila kan sakin wasu fararen hula da aka tsare tun farkon yaƙin Isra’ila da Hezbollah a shekarar 2024.

    Ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ta cikin wata sanarwa ya ce bayan kammala bincike da tambayoyi, an tabbatar da cewa mutanen fararen hula ne, ba mambobin wata ƙungiya da Isra’ila ke ɗauka a matsayin ta’addanci ba ne, kuma ba su shiga ayyukan ta’addanci ba. Saboda haka, babu wani dalilin ci gaba da tsare su.

    Ofishin Netanyahu ya kuma ce wannan matakin ya biyo bayan wani ƙoƙari da aka yi tsakanin Isra’ila da Lebanon domin gano da kuma dawo da gawarwakin shugabannin al’ummar Yahudawan Lebanon waɗanda aka yi garkuwa da su kuma aka kashe su a shekarun 1980 lokacin yaƙin basasar Lebanon da ya ɗauki shekaru 15.

    Karanta ƙarin labari a nan:

  14. Ma'aikatan sun maƙale ne a cikin bututun na kwanaki tara

    Za mu ci gaba da kawo muku rahotannin kan yadda aikin ceto ke gudana a tashar ruwa ta 3A Hydropower da ke Trishuli.

    Hukumomi sun shaida wa BBC cewa ana sa ran za a ceto kimanin mutane 42 da suka maƙale a wurin.

  15. Hotonan yadda aka ceto ma'aikatan

  16. Da gaske ne ana iya sace wa namiji al'aura?

    Sama da mutum 80 ne aka kashe tsakanin watan Oktoban 2025 zuwa Yulin 2026 kan zargin "satar al'aura," da ake kira shafi-mu-lera, kamar yadda sashen yaƙi da labaran bogi na BBC ya bayyana bayan tattara bayanai daga jami'an ƴansanda a ƙasashe shida na Afirka.

    Kisan na da alaƙa da jita-jitar cewa taɓa kafaɗar mutum kawai zai iya sa al'aurarsa ta ragu ko ta ɓace. Ana ƙara rura wutar matsalar ta hanyar amfani da labaran ƙarya da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta.

    "Sun fara ihu ne cewa mun sace al'aurar wani, kuma ba mu da wata hanyar tsira saboda akwai tarin jama'a," in ji wani makanike ɗan ƙasar Tanzaniya Boniface Mgala, wanda ya shaida wa BBC irin wahalar da ya sha a watan Afrilu lokacin da waɗanda suka yi imanin cewa shi barawon al'aura ne suka yi masa dukan tsiya.

    Abin da ya fuskanta ya yi kama da na bidiyon da BBC ta gani: maza suna cewa al'aurarsu ta ɓace ko sun yi rauni bayan sun haɗu da wasu mutane, sannan akwai taron jama'a suna neman waɗanda ake zargi da aikata laifin su mayar da abin da aka yi zargin sun sace.

    Irin waɗannan ikirari sun samo asali ne daga tsoro da camfe-camfe na baya, musamman a cikin al'ummomin da imani da sihiri ya yi karfi. Kafafen sada zumunta sun ƙara wa waɗannan tsoro.

    Karanta cikakken labarin a nan: https://www.bbc.com/hausa/articles/ckgw29xkn9eo

  17. An ceto ma'aikatan da suka maƙale a bututun ruwa a Nepal

    An ceto ma'aikata biyu da ransu a wani bututun madatsar ruwa a Nepal, inda suka shafe kwana tara bayan ambaliyar ruwan da ta yi mummunar ɓarna a yankin Tibet.

    Mahukunta sun ce an ceto Sanjaya Shah da Kbir Maharjan, kuma ana duba lafiyar su a asibiti.

    Aikin ceto na ci gaba da gudana a wurare da dama da bututun ruwa ya wuce, inda ake zaton mutane sun maƙale bayan ambaliyar ruwan.

    Mutane 1,200 suka mutu a mummunar ambaliyan ruwan, kuma wasu dubbai sun rasa muhallin su.

  18. Manyan ayyuka da gwamnatin Tinubu ke iƙrarin yi a arewacin Najeriya

    Martani na ci gaba da baibaye kalaman shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ya bayyana cewa arewacin ƙasar ne ya fi cin moriyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

    Farfesa Yilwatda, a wani taron ƙwararrun jam'iyyar APC da aka yi wa taken "hisabin gwamnatin Tinubu', da aka gudanar ranar Laraba a Abuja, ya ce arewacin Najeriya mafi cin gajiyar romon dimokraɗiyya ta fuskar tattalin arziƙi.

    "Waɗanda za su fi cin gajiyar wannan tattalin arziƙi su ne yankin Arewacin Najeriya, domin yanzu za su riƙa kasuwanci da ƙasashe maƙwabta, su yi hulɗar kasuwanci da Nijar, da Chadi, da Burkina Faso, da Sudan ta Kudu, da Arewacin Kamaru, da Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. Saboda haka, Arewa ce za ta zama sabuwar cibiyar kasuwanci mafi muhimmanci a Najeriya," in jni Yilwatda.

    To sai dai BBC ta tuntuɓi Abdul'aziz Abdul'aziz ɗaya daga cikin mataimakan shugaba Tinubu dangane da ayyukan da ake yi wa arewacin da za su ɗaga likkafar yankin.

    Karanta cikakken labarin a nan: https://www.bbc.com/hausa/articles/cvgyplrn406o

  19. Abu 4 da suka hana Najeriya magance matsalar garkuwa da mutane - C.G. Musa

    Najeriya ta dade tana fama da matsalar satar dalibai daga makarantu, wani abu da ya samo asalin tun a watan Afrilun 2014, lokacin da mayakan Boko Haram suka sace kimanin dalibai 276 daga makarantar ‘yanmata ta Chibok a jihar Borno, wadanda har yanzu wasunsu ba su koma gida ba.

    A halin da ake ciki yanzu ma akwai dalibai da dama da ke hannun ‘yanbindiga wadanda aka sace su daga cikin azuzuwansu a makarantar da suka je daukar darasi. misali shi ne yaran da aka dauke daga kauyen Mussa a jihar Borno, cikinsu har da yara ‘yan kasa da shekara uku, kamar yadda iyaye suka tabbatar.

    Wannan lamari ya dade yana ci wa al’ummar Najeriya tuwo a kwarya, sai dai har yanzu hukumomin kasar sun kasa gano hanyar magance lamarin, domin kuwa ana ci gaba da samun irin wannan matsala akai-akai.

    Shirin sashen Ingilishi na BBC ya zanta da tsohon babban hafsan sojin Najeriya kuma ministan taro na kasar, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, wanda ya lissafa wasu abubuwa da ya ce na daga cikin dalilan da suka sa aka kasa magance matslaar garkuwa da mutane a ƙasar.

    To amma ministan tsaron ƙasar ya ce yanayin dazukan ƙasar da kuma faɗin kan iyakokinta na daga cikin abubuwan da ke kawo cikas wajen yaƙi da masu garkuwa da mutane.

    Karanta cikakken labarin a nan: https://www.bbc.com/hausa/articles/c4g7r3yxlgyo

  20. Buɗewa

    Barkan ku da safiyar ranar Juma'a wadda Hausawa ke yi wa kirari da babbar rana. Da fatan Allah ya ba mu albarkacin wannan rana.

    Kamar kullum yau ma mun dawo muku da shafinmu na kai tsaye da muke kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi mai kama da jakar Magori wato mai ɗauke da komai a cikinsa.