Ƴan adawa ne ke kambama matsalar tsaro domin ɓata sunan Tinubu - Matawalle

Asalin hoton, @Bellomatawalle1/X
Ƙaramin Ministan tsaro na Najeriya, Bello Muhammad Matawalle ya zargi ƴan adawar ƙasar da zuzuta matsalar tsaro domin ɓata sunan shugaba Bola Tinubu.
Matawalle ya yi zargin cewa suna yaɗa farfaganda domin cimma wata manufar siyasa da kauda hankalin mutane kan ci gaban da ake samu a ƙasar.
Ya ce ana samun nasarori sosai a yaƙi da matsalar tsaro da dakarun Najeriya ke yi musamman a yankin arewacin maso yammacin ƙasar.
"Babu wata farfaganda ko yarfen siyasa da za su kauda hankalin shugaban ƙasa kan cika alƙawuran da ya yi wa ƴan Najeriya," in ji shi.
Wata sanarwa da mai taimaka wa Ministan kan harkokin yaɗa labarai, Ahmad Dan-Wudil ya fitar, ta ambato Matawalle na cewa "duk da irin waɗannan suka da ake yi, Tinubu na da farin jini a arewacin ƙasar."
Ministan ya ce Tinubu ne zai lashe zaɓen 2027 musamman a arewacin ƙasar saboda suna ganin irin nasarorin da ake samu.
"Ƴan adawar suna ganin irin ci gaban da ake samu a yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar, sai dai su yaɗa farfaganda kawai" in ji Matawalle.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙara ƙaimi wajen yaƙar ƴan bindiga a jiihohin Sokoto, Zamfara, Katsina, Kaduna da Kebbi, kuma ana ganin sakamako mai kyau.
"Al'ummar yankin suna ganin irin ƙoƙarin da ake yi... muna da tabbacin cewa ƴan Najeriya na goyon bayan sauye-sauyen da ake samu".





















