Portugal za ta buga wasan sada zumunta da Najeriya, Gasar kofin duniya
Portugal za ta kara da Najeriya a wasan sada zumunta a Oeiras a daren Laraba a matsayin wani bangare na shirye-shiryen karshe kafin ta je sansanin horo a gasar Kofin Duniya a Florida.
Kocin Portugal, Roberto Martinez, zai yi amfani da wannan damar domin bai wa dukkan ƴan wasansa damar taka leda, ciki har da gola, Diogo Costa, wanda bai yi wasa uku ba, saboda jinya.
“Manufar ita ce Diogo Costa ya buga cikakken mintuna 90, sannan a bai wa sauran ƴan wasa dama su samu mintunan buga wasa da yawa,” in ji Martinez a sansanin horo na ƙasar Portugal.
Cristiano Ronaldo, Bruno Fernandes, Bernardo Silva da Diogo Costa sun yi atisaye a Lisbon tare da tawagar kafin wasan.
Ana sa ran wannan gasar da za a yi a Cnada da Mexico da Amurka za ta kasance ta shida ga Ronaldo zai halarta, abin da zai zama tarihi ga mai shekara 41 wanda ya shafe shekara 20 yana mayar da abin da ake ganin ba zai yiwu ba ya zama al’ada, sau ya sauya ya kuma kafa tarihi.
Martinez ya kuma bayyana cewa yana jin dadɗi da Ronaldo ke kan ganiya, wanda ya ci ƙwallaye 25 a wasa 30 a karkashinsa, adadin da ya fi na kowanne koci da ya horar da shi a baya.
Portugal za ta fara wasanninta na rukuni da DR Congo a ranar 17 ga watan Yuni, sannan za ta kara da Uzbekistan a ranar 23 ga watan Yuni, kafin ta kammala da Colombia a ranar 28 ga watan Yuni.
Ronaldo na san ran lashe kofin duniya a bana, wanda shi ne kaɗai ya gagare shi a tarihinsa na taka leda.

Asalin hoton, Getty Images




