Trump ya yi barazanar janye sojojin Amurka daga Sifaniya da Italiya saboda yaƙin Iran
Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana duba yiwuwar janye sojojin ƙasarsa daga Italiya da Sifaniya, sakamakon adawa da yaƙin Iran da ƙasashen biyu ke yi.
Mista Trump ya bayyana matakin ne kwana guda bayan irinsa da ya yi kan Jamus.
Cikin wani jawabi da ya yi daga fadarsa, Shugaba Trump ya ce ''yana duba yiwuwar ɗaukar matakin, saboda babu wani taimako da Italiya ta bayar a yaƙin da Amurka ta yi da Iran, sannan ya bayyana Sifaniya a matsayin mafi muni''.
Trump ya bayyana a ranar Laraba cewa Amurka na duba yiwuwar rage yawan sojojinta a Jamus, yayin yake samun saɓani da shugaban gwamnatin ƙasar, Friedrich Merz kan yaƙin na Iran






