KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 30/09/2026

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai
  • Yadda sheikh Lukuwa
  • Hoto
  • Cyber Truck
  • Abdourahamane Tchiani
  • Atiku Abubakar

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Sojojin Najeriya sun kai hare-hare 364 don tabbatar a tsaro a sassan Najeriya

    .
    Bayanan hoto, Dakarun Sojin Najeriya

    Shalkwatar Tsaro ta Najeriya ta ce dakarunta sun kai hare-hare 367 a sassa daban-daban na ƙasar a watan Satumban 2026 don tabbatar da tsaro.

    Bayanai sun nuna cewa rundunar Operation Enduring Peace ce ta kai mafi yawan hare-haren, da jimillar hare-hare 147, sai Operation Fansan Yamma da hare-hare 115, sannan Operation Whirl Stroke da hare-hare 55.

    Operation Hadin Kai ta samu hare-hare 33, yayin da Operation Savannah Shield kai 13, sannan Operation Udo da ta kai hari huɗu.

    Rundunar Operation Delta Safe kuwa ba ta kai hari ko da gua ba a tsawon watan na Satumba.

    Da yake bayyana nasarorin da sojojin suka samu a sassa daban-daban na ƙasar ranar Laraba, daraktan watsa labarai na rundunar Manjo Janar Michael Onoja, ya ce dakarun sojin na mayar da martani cikin gaggawa.

    Ya ce sojojin na arangama da maharan cikin gaggawa, inda suke amfani da ƙarfin makamai da dabarun yaƙi, tare da dakile hare-haren cikin nasara.

  2. Dangote ya ƙaddamar da ginin matatar mai a Kenya

    .
    Bayanan hoto, .

    Attajirin Afirka kuma ɗan Najeriya, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da aikin gina wata matatar mai a gabar tekun Kenya.

    Shugaban Kenya, William Ruto, ya ce matatar, wadda ake sa ran gina ta zai lakume dala biliyan 18 a yankin Lamu, za ta taimaka wa ƙasar wajen rage tasirin sauye-sauyen farashin makamashi a kasuwannin duniya.

    Aliko Dangote ya ce: "Wannan na nufin Afirka ta zo domin gina Afirka. A yau, ba kawai muna haƙa rami ne domin gina matatar mai ba, a'a, mun buɗe sabon babi na ci gaba a Afirka."

    Wani wakilin BBC ya ce aikin gina matatar ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda aka gudanar da zanga-zanga saboda damuwar da wasu ke nunawa kan yiwuwar illar da aikin zai iya yi wa muhalli.

    Sai dai duk da haka, Dangote na ci gaba da aikin ginin, duk da umarnin da wata kotu ta bayar na dakatar da aikin.

  3. Rundunar sojin Najeriya ta samar da ƙarin bataliyoyi 3 don samar da tsaro a Zamfara

    Dakarun Sojin Najeriya
    Bayanan hoto, Dakarun Sojin Najeriya

    Rundunar Sojin Najeriya ta fara aiki da sabbin bataliyoyin sojinta uku a Jihar Zamfara, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan tsaro da inganta mayar da martani cikin gaggawa.

    A cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Sojoji, Birged ta 1 ta Sojin Najeriya da ke Gusau, ya fitar ranar Talata a shafin X, an ce sabbin bataliyoyin da aka fara aiki da su su ne Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 12 da ke Bakura, da Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 23 da ke Kaura Namoda, da Bataliyar Sojojin Ƙasa ta 28 da ke Anka.

    Ana sa ran bataliyoyin za su faɗaɗa ayyukan rundunar sojin a wuraren da suke gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da tsaron yankunan da aka ɗora musu alhakin kula da su.

    Da yake jawabi a yayin bukukuwan fara aiki da bataliyoyin, Babban Kwamandan Runduna ta 8 ta Sojin Najeriya kuma Kwamandan Sashen Haɗin Gwiwa na Rundunar Yaƙi ta 2, Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, Manjo Janar BP Koughna, wanda Mukaddashin Kwamandan Birged ta 1, Kanal Joseph Umaru, ya wakilta, ya sake jaddada ƙudurin rundunar sojin na ƙarfafa ayyukan tsaro a jihar.

  4. Rikici ya ɓarke tsakanin matuƙan jirgin sama ɗauke da fasinja 170

    Jirgin sama

    Wani jirgin sama da ke tafiya daga Dubai zuwa Tel Aviv, ɗauke da kimanin fasinjoji 170, ya yi saukar gaggawa a Saudiyya bayan da aka ruwaito cewa faɗa ya ɓarke tsakanin matuƙan jirgin.

    Wasu jami'an Isra'ila biyu sun ce ana kyautata zaton mataimakin matuƙin jirgin ya daba wa babban matuƙin wuƙa.

    Yayin da ƙarin bayanai ke fitowa daga fasinjojin jirgin, lamarin na ƙara zama mai ban mamaki da firgitarwa.

    Jirgin ya aika da saƙon gaggawa cewa ana ƙoƙarin ƙwace shi. Sai dai bayanan da ke fitowa yanzu na nuna cewa ana zargin ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ne da yunkurin ƙwace shi, ba wani fasinja ba.

    Fasinjojin da ke cikin jirgin sun bayyana cewa jirgin ya fara gangarowa da sauri, inda ya sauka da kimanin ƙafa dubu 17 cikin ƴan mintuna.

    An ce rikici ya ɓarke tsakanin matuƙin jirgin da mataimakinsa, inda aka daba wa aƙalla ɗaya daga cikinsu wuƙa.

    Wani fasinja ya ce daga bisani wasu mutane suka kutsa cikin ɗakin matuƙan jirgin domin taimakawa wajen shawo kan ɗaya daga cikinsu, kafin su ɗaure shi.

    Hotunan bidiyo da aka ɗauka da wayar salula sun nuna mutane da dama a cikin jirgin jikinsu na ɗauke da jini.

    Yanzu masu bincike za su tantance ko ɗaya daga cikin matuƙan jirgin ya yi niyyar kifar da shi da gangan, da kuma ko akwai wata manufa ta siyasa a bayan lamarin.

    Jirgin na ɗauke da kusan Isra'ilawa 100.

    Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra'ila, Itamar Ben Gvir, ya bayyana lamarin a matsayin harin ta'addanci, yana mai cewa manufar ita ce kashe dukkan mutanen da ke cikin jirgin.

    Wani bidiyo da kafofin yaɗa labaran Isra'ila suka wallafa ya nuna wani da aka ce yana cikin jirgin yana bayyana cewa wani mutum ɗauke da wuƙa ya daba wa ɗaya daga cikin matuƙan jirgin.

    BBC Verify ta binciki bidiyon, kuma ba ta gano wata alamar cewa an sarrafa shi da fasahar AI ba.

    Haka kuma, ba a ga alamar cewa an wallafa bidiyon a intanet kafin faruwar lamarin ba.

    Isra'ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun ƙulla hulɗar diflomasiyya a shekarar 2020 ƙarƙashin yarjejeniyar Abraham Accords da Amurka ta shiga tsakani.

    Yarjejeniyar ta daidaita hulɗar ƙasashen biyu. Kafin wannan yarjejeniya, an hana jiragen Isra'ila bi ta sararin samaniyar Saudiyya.

  5. Kotu ta ɗaure mai shekara 50 kan yi wa ƙaramar yarinya fyaɗe a Jigawa

    Wata babbar kotu a jihar Jigawa ta yanke wa wani mutum mai shekara 50 hukuncin shekara 10 a gidan gyaran hali kan yi wa ƙaramar yarinya ƴar shekara 11 fyaɗe.

    Kotun, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Muhammad El Usman ta samu mutumin mai suna Abubakar Biniya da laifi.

    A cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar shari’a a jihar Jigawa, Abbas Rufa’i Wangara ya fitar, wanda aka yanke wa hukuncin ya aikata laifin ne a watan Janairun 2024 a unguwar Galadanchi da ke Ringim.

    Masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Shari’a sun gabatar da shaidu shida tare da miƙa hujjoji biyar ga kotun, ciki har da rahoton likita, domin tabbatar da zargin.

    Wanda ake tuhuma ya bayar da shaida domin kare kansa, amma bai gabatar da wata shaida ba.

    Da yake yanke hukunci, alƙalin ya ce kotun ta yi la’akari da roƙon sassauci da Biniya ya yi da kuma kasancewar wannan ne karon farko da aka same shi da aikata laifi kafin ta yanke hukuncin.

    Baya ga ɗaurin shekara 10 a gidan gyaran hali, kotun ta umarci Biniya ya biya yarinyar diyyar naira 500,000.

    Kotun ta kuma bayar da umarnin saka sunansa a rajistar masu aikata laifukan cin zarafi ta hanyar lalata ta Jihar Jigawa, wadda Ma’aikatar Shari’a ta jihar ke kula da ita.

    Haka kuma, ta umarci a yi sanarwa a gidajen rediyo, kamar yadda sashe na 3(2), (4) da (5) na dokar hana cin zarafin mutane ya tanada.

    Kotun ta bai wa ɓangarorin da ke shari’ar wa’adin watanni uku su ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

  6. 'Wasu matan ba su san suna ɗauke da cutar da ke sa mace gemu ba'

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon

    Gemu ko gashin bakin da kuke gani a fuskar wasu mata, ba haka kawai ba ne. Larura ce!

    An ware duk watan Satumba domin faɗakar da mutane cewa kimanin kashi 10% na mata suna da larurar rikicewar sinadaran jiki wato PCOS a taƙaice.

    Albarkacin wannan wata, mun zanta da wata mai wayar da kai kuma da ke da wannan cuta domin jin suke fama.

  7. Abin da Mufti Menk ya cewa Rahama Sadau

    Rahama Sadau da Mufti Menk

    Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta koka kan salon wasu kamfanonin tsara tafiye-tafiye na ɗaukar bidiyon masu ibadar Umrah da suka je ƙasa mai tsarki ta kamfaninsu a wani ɓangare na tallata kamfanonin nasu.

    Rahama Sadau ta bayyana damuwarta ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram, inda ta ce tana sha’awar zuwa Umra cikin rukunin jama’a amma salon kamfanonin da ke nema zama ruwan dare na matuƙar sanyaya gwiwa.

    Ta ce ya kamata Umrah ta kasance ibada maimakon mayar da ita wata dama ta samar da hotuna ko bidiyon da za a wallafa a shafukan sada zumunta.

    Saƙon nata ya ja hankalin mutane da dama inda fitaccen malamin addinin Musulunci Mufti Menk, ya yi martani kan saƙon nata inda kuma ya ba ta shawarar kamfanin da za ta iya zuwa umarah ta hannunsu wanda ya ce yana bai wa mahajjata damar gudanar da ibadarsu cikin sirri.

    Sai dai y ace a zamanin da ake ciki, mutane da dama kan samu ƙwarin gwiwar zuwa Umrah ne bayan sun ga wasu sun je amma a caerwa shi “abin da ya fi dacewa shi ne kada ɗaukar hotunan ya zama abin da aka fi mayar da hankali a kai.”

  8. Rukunin ƙarshe na sojin Amurka na ficewa daga Iraƙi

    Sojojin Amurka na ƙarshe na janyewa daga Iraki, abin da ke kawo ƙarshen kasancewar dakarun Amurka a ƙasar tsawon sama da shekara 20.

    Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta yaba da rawar da sojojin suka taka, tana mai cewa sun yi nasarar murƙushe ƙungiyar ISIS a Iraki da ma yankin baki ɗaya.

    Pentagon ta ce janyewar sojojin ta kuma nuna sauyin da ake samu zuwa tsarin tsaro da Iraki za ta jagoranta, tare da samun goyon bayan Amurka ta hanyar hulɗar ƙasashen biyu kamar yadda aka saba.

    Sai dai masana harkokin tsaro a Iraki na gargadin cewa Iran da ƙungiyoyin da take marawa baya za su iya amfani da kafar da janyewar sojojin Amurka za ta haifar domin ƙara faɗaɗa tasirinsu.

    Sojojin Amurka sun fara mamaye Iraki ne shekara 23 da suka gabata, inda suka jagoranci ƙawancen ƙasashe wajen hambarar da gwamnatin Saddam Hussein.

    Daga bisani sojojin Amurka sun sake komawa ƙasar a shekarar 2014 domin yaƙi da ƙungiyar IS.

  9. Ina cikin ƙoshin lafiya kuma na shirya yin aiki gadan-gadan - Tinubu

    Bola Tinubu da manyan jami'an gwamnati

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce yana cikin ƙoshin lafiya kuma a shirye yake ya koma bakin aiki.

    Ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan isarsa filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas bayan kammala hutun aiki na tsawon wata ɗaya a Turai.

    Da yake magana da manema labarai, Shugaba Tinubu ya kuma yi watsi da jita-jitar da ake yi cewa yana fama da rashin lafiya bayan shafe tsawon lokaci yana hutun aiki a Turai.

    Manyan jami’an gwamnati ne suka tarbe shi cikinsu har da gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila, kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq, da kuma manyan jami’an tsaro.

    Ya kuma ce jita-jita wani abu ne da aka saba gani a siyasa, amma ya jaddada cewa yana nan cikin koshin lafiya kuma a shirye yake ya ci gaba da aiki.

    A cewarsa, ya ji daɗin hutun nasa, kuma babu wata matsala da yake fama da ita.

  10. Rasha ta sake kai gagarumin hari kan Kyiv

    Rasha ta sake kai wani mummunan hari ta sama kan yankin Kyiv babban birnin Ukraine cikin dare, inda ta yi amfani da makamai masu linzami da jirage marassa matuƙa.

    Wani babban jami'i ya ce gidaje da dama sun rushe a wata gunduma sakamakon harin, kuma an gano gawar wani yaro a ƙarƙashin baraguzan gine-ginen.

    Ya ce an ceto wasu daga cikin iyalan yaron da suka samu raunuka a harin.

    Rahotanni sun ce harin ya kuma lalata rumbunan ajiya da wasu muhimman kayayyakin more rayuwa, lamarin da ya haifar da katsewar wutar lantarki da kuma tangarda wajen samar da ruwa.

    A baya-bayan nan dai Rasha ta ƙara yawan hare-haren da take kai wa birnin Kyiv cikin dare da kuma rana.

  11. Dangote zai ƙaddamar da aikin gina matatar mai a Kenya

    Dangote

    Nan gaba a yau ne, Attajirin Afirka Aliko Dangote, zai aza harsashin gina wata matatar man fetur a gabar tekun Kenya.

    Shugaban kasar Kenya, William Ruto, ya ce matatar wadda za a gina a yankin Lamu za ta taimaka wajen kare kasar daga sauye-sauyen farashin makamashi a kasuwannin duniya.

    Wakilin BBC ya ce ginin matatar ya haifar da ce-ce-ku-ce, inda aka samu arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga da ke ikirarin cewa filin da za a gina matatar mallakinsu ne.

    Masu zanga-zangar sun kuma nuna damuwa kan yiwuwar illa ga muhalli da aikin zai iya haifarwa.

    Sai dai kuma duk da haka, Dangote na ci gaba da fara aikin ginin duk da umarnin wata kotu da ya bukaci a dakatar da aikin.

    ..
    ..
    ..
  12. Barka da Hantsi

    Jama'a barkan mu da wannan safiya ta Laraba - tabawa ranar samu daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo har ma ku tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.