KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 11 ga watan Agustan 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Usman MINJIBIR

  1. Alhakin rufe mashigar Hormuz ya kan Amurka - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce ya kamata ƙasashen duniya da su ɗora wa Amurka alhakin duk wata illa ta tsaro da tattalin arziki da ka iya tasowa sakamakon toshe tasoshin ruwanta a mashigar Hormuz.

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawar waya da takwaransa na Jamus, Johann Wadephul, inda ya ce matakan da Amurka ke ɗauka a yankin ne suka haddasa rashin tsaro a mashigar.

    Araqchi ya ce Iran na ci gaba da tattaunawa da Oman domin nemo wata amintacciyar hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz.

    Ya kuma zargi Amurka da Isra'ila da haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin ta hanyar hare-haren soji da yake cewa suna kai wa Iran.

    A cewar kafafen yaɗa labaran Iran, ministan ya jaddada cewa samar da tsaro a mashigar Hormuz na bukatar kawo ƙarshen abin da ya kira matakan tsoma bakin Amurka ba bisa ƙa'ida ba, ciki har da toshe zirga-zirgar jiragen ruwa da sauran ayyukan da ya ce sun saɓa wa alƙawurran ƙasar.

  2. Zan mayar wa Netanyahu martani kan watsi da shirin zaman lafiyar Gaza - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce nan ba da jimawa ba zai mayar wa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu martani, bayan Netanyahu ya yi watsi da shirin zaman lafiya na Gaza mai kunshe da batutuwa 15.

    Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Fadar White House, inda ya ce zai wallafa martaninsa a shafinsa na Truth Social.

    Ya ce yana da amsar da yake ganin ta dace, kuma zai wallafa ta a shafin.

    Duk da rashin amincewar Netanyahu da shirin, Trump ya ce har yanzu dangantakarsa da firaministan tana nan da kyau sosai.

    Netanyahu ya ƙi amincewa da shirin, yana mai cewa Isra’ila ba za ta amince da janye dakarunta daga Gaza ba matukar Hamas ba ta mika makamanta gaba daya ba.

  3. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.