Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da shirin HOPE-SP na dala biliyan 1 domin agaza wa marasa ƙarfi a ƙasar, inda ta ce shirin zai sauya yanayin tallafin da ake yi zuwa na ɓullo da hanyoyin dogaro da kai.
Shirin mai suna Household Prosperity and Economic Social Protection Project (HOPE-SP), an ƙiyasta zai ci dala biliyan 1, a wani mataki da ke nuna sauyin tsarin tallafin jinƙai daga bayar da tallafi na ɗan lokaci zuwa samar da hanyoyi da gwamnatin ta ce masu ɗorewa da za su taimaka wa jama’a su fita daga talauci.
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ce ta ƙaddamar da shirin a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ta yaba wa ministan harkokin jinƙai da rage talauci, Dr. Bernard Doro, da tawagarsa bisa ƙoƙarin da suke yi.
An tsara sauye-sauyen ne domin inganta yadda ake gano da tantance gidajen da ke cikin buƙata, da kuma tabbatar da cewa tallafi ya isa ga waɗanda suka fi cancanta. Haka kuma, za su ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin shirye-shiryen jinƙai da na rage talauci, tare da samar da tallafin gaggawa yayin fuskantar matsaloli da kuma ƙara gaskiya da riƙon amana.
Ministan ya ce ɗaya daga cikin muhimman abubuwan shirin shi ne One Humanitarian, One Poverty Response System (OHOPRS), wanda zai haɗa shirye-shiryen agaji, zamantakewa da rage talauci cikin tsari guda na ƙasa.
"Tsarin zai yi amfani da rajista guda, hanyoyin isar da tallafi na zamani, ingantaccen tsarin kuɗaɗe da bayanan sirri na zamani domin yanke shawara cikin gaggawa."
Babban Sakatare na Ma’aikatar, Olubunmi Olusanya, ya ce sauye-sauyen za su ƙarfafa haɗin gwiwa da riƙon amana, yana mai jaddada cewa babban ma’aunin nasara shi ne ganin sauyi na zahiri a rayuwar ‘yan Najeriya masu buƙata. Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, da sauran masu ruwa da tsaki, ciki har da Ministan Tsare-tsaren Kasafin Kuɗi da Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, da abokan hulɗar kamar Tarayyar Turai da Bankin Duniya, sun yaba da ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na ƙarfafa tsarin ayyukan jin jinƙai a Najeriya.