Tattalin arzikin Iran na fuskantar ƙalubale saboda yaƙi da takunkumi
Sabbin alƙaluman gwamnati daga Iran sun nuna cewa tattalin arzikin ƙasar na ci gaba da fuskantar ƙalubale sakamakon yaƙin da take yi da Amurka da kuma takunkuman tattalin arziki da aka ƙaƙaba mata.
Bisa ga bayanan, yawan kuɗaɗen da ƙasar ke samarwa a cikin gida (GDP) ya ragu da sama da kashi 10 cikin 100 idan aka kwatanta da na bara.
Haka kuma, kayayyakin da Iran ke fitarwa zuwa ƙasashen waje sun ragu da fiye da kashi ɗaya bisa uku, yayin da Amurka ke ci gaba da matsa mata lamba ta hanyar takunkuman tattalin arziki.
Kazalika, hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ta ƙaru sosai, inda ta kai aƙalla kashi 70 cikin 100, lamarin da ke ƙara tsananta wa al'ummar ƙasar matsin rayuwa.
Masana na ganin waɗannan alamu na nuna irin girman tasirin yaƙi da takunkuman da ke addabar tattalin arzikin Iran.