Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 29 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Kocin ƙwallon ƙafar Koriya ta Kudu ya yi murabus bayan rashin nasara a gasar cin kofin duniya

    Hong Myung-bo ya yi murabus daga muƙaminsa na kocin tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar Koriya ta Kudu bayan da suka kasa tsallakewa zuwa zagayen gaba na gasar cin kofin duniya. \

    Ƙungiyar ta yi fatan za ta iya tsallakewa zuwa zagaye na gaba a gasar a matsayin ɗaya daga ƙasashe takwas na alfarma, amma hakan ya ci tura ranar Asabar.

    Ficewar da wuri ya haifar da suka a gida, inda shugaban ƙasar Lee Jae Myung ya yi kira da a gudanar da bincike kan dalilan da suka sa tawagar ta kasa taka rawar gani.

    Hong ya nemi afuwar magoya bayansa ranar Lahadi kuma ya ce alhakin "ya rataya ne a wuya ta ni kaɗai a matsayina na kociyan ƙungiyar".

    Koriya ta Kudu wadda ke matsayi na 32 a jerin ƙasashen da suka fi hazaƙa a fagen ƙwallon ƙafa, ta ci wasa ɗaya da kuma sha kashi a wsanni biyu a gasar cin kofin duniya ta, inda ta ƙare a bayan Mexico da Afrika ta Kudu, wadanda ke matsayi na 15 da 60 a duniya.

  2. Iran ta buƙaci mu yi wata ganawar a Qatar - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran ta nemi a yi wata ganawa da Amurka a ranar Talata a birnin Doha na ƙasar Qatar, bayan da ƙasashen biyu suka sake kai wa junansu hare-hare a kwanakin baya, lamarin da ke barazana ga tsagaita wuta da ake ƙoƙarin tabbatarwa

    Fadar White House ta ce manyan masu tattaunawa na Amurka, Jared Kushner da Steve Witkoff, za su halarci taron, inda kuma Trump ke fatan ganin an ci gaba da tattaunawar sulhun ba tare da tangarɗa ba.

    Haka kuma ta bayyana cewa za a gudanar da wasu tattaunawa a gefe domin ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar da ke tsakanin ɓangarorin.

    Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Kazem Gharibabadi, ya musanta cewa za a yi irin waɗannan tattaunawar a wannan makon, yana mai cewa har yanzu ba a kammala shiri kan ranar da wurin ganawar ba, kuma ana masu shiga tsakani na ci gaba da shawarwari kan yadda tattaunawar za ta kasance.

  3. Hotunan ɓarnar da girgizar ƙasar Venezuela ta haddasa

    Ga wasu hotuna da ke nuna ɓarnar da girgizar ƙasa ta haddasa a Venezuela, inda gine-gine suka rushe ƙurmus suka koma tarkace. Rahotanni sun nuna cewa girgizar ƙasar ta janyo asarar rayuka sama da 1,400 tare da lalata gidaje da kadarori.

  4. 'Iran da Amurka za su ci gaba da tattaunawa a Doha nan da kwanaki'

    Wata majiya da ke da masaniya kan tattaunawar Iran da Amurka ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa tawagogin ƙasashen biyu na aiki kan yadda za a ci gaba da aiwatar da tattaunawar yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka kuma ana sa ran za su gana ne a birnin Doha cikin kwanaki masu zuwa.

    Majiyar ta kuma bayyana cewa masu shiga tsakani sun buƙaci kafa hanyoyin sadarwa tsakanin ɓangarorin domin rage tashin hankali da kuma kauce wa duk wasu rikice-rikice, tare da ci gaba da tattaunawar fasaha a lokaci guda.

    A halin yanzu, shugaban tawagar Iran, Kazem Gharibabadi, wanda ke ƙasar Oman, ya sanar da gudanar da taron farko na kwamitin hadin gwiwa kan mashigar Hormuz tsakanin ƙasashen biyu a birnin Muscat.

    Rahotanni sun nuna cewa wannan yunƙuri na daga cikin matakan diflomasiyya da ake ɗauka domin rage rikici tare da tabbatar da zaman lafiya, musamman kan batun tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci ga harkokin mai a duniya.

  5. Har yanzu gwamnati ba ta tuntuɓe mu ba - Iyalan Shugaban Miyetti-Allah

    Iyalan shugaban ƙungiyar Miyetti-Allah, Alhaji Ardo Risku da aka kashe a jihar Benue sun koka cewa har yanzu gwamnati ba ta tuntuɓe su ba tun bayan faruwar lamarin, duk da alƙawuran da ake yi na cewa za a ɗauki mataki kamar yadda babban ɗan marigayin, Muhammad Idris ya shaida wa BBC.

    Wannan na zuwa ne bayan da rundunar ’yansandan jihar Benue ta tabbatar da kama mutum 10 da ake zargi da hannu a kisan shugaban da wasu mutum uku, waɗanda aka harbe su a ranar Juma’a yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida daga wani taro da ya shafi tsaron jihar.

    Gwamnatin jihar Benue ta bayyana cewa ta yi Allah wadai da kisan tare da ƙaddamar da bincike, amma iyalan marigayin sun ce ba su ji wani sakamako kai tsaye daga gwamnati ba.

    Sun bayyana cewa har yanzu suna jiran a tuntuɓe su domin ganin an yi musu bayani kan matakan da ake ɗauka.

    Babban ɗan ya ce a ranar da aka kashe shi, ya je ya gaishe shi da safe, inda ya shaida masa cewa DPO na karamar hukumar Ohimini ya kira shi domin wani taro. “Sai ya kira wasu mutum uku su tafi tare, suka hau babur suka nufi inda za a yi taron,” in ji shi.

    Ya ƙara da cewa sun samu labarin kisan ne bayan sallar Juma’a, lokacin da suka ga mutane sun taru ana cewa an ga wasu mutane a bakin hanya an harbe su.

    “Mun kira wayoyinsu ba su shiga ba, daga nan muka tafi wurin muka tarar ’yansanda sun riga mu, sun ɗauki gawarwakin,” in ji shi, yana mai korafin cewa, “tun daga lokacin DPO bai kira mu ba, gwamnatin ma ba ta tuntuɓe mu ba.”

    Benue na daga cikin jihohin arewa ta tsakiyar Najeriya da ke fama da matsalar rashin tsaro, inda ake samun yawaitar fito na fito tsakanin manoma da makiyaya.

    Gwamnatin Najeriya da kuma na jihar sun sha iƙirarin cewa suna yin bakin ƙoƙarinsu wajen shawo kan lamarin, sai dai har yanzu abin ya ci tura.

    Wani rahoto na Majalisar dokokin Amurka ya zargi ƙungiyoyin makiyaya da kasancewa cikin masu hannu wajen 'gallaza wa Kiristoci' a Najeriya, lamarin da ƙungiyoyin suka musanta.

  6. Ko sakamakon zaɓen 2023 zai iya zama madubin na 2027?

    Tun bayan da jam'iyyun siyasa a Najeriya suka kammala zaɓukar fitar da gwanayen da za su tsaya musu takara a zaɓukan 2027, wasu ƴanƙasar suka soma hasashen sakamakon zaɓen da ke tafe ta hanyar kwatanta shi da na 2023 da ya gabata.

    Bisa ga bayanan zaɓukan fitar da gwanayen ƴantakarar da suka fatata a 2023 ne za su sake karawa a zaɓen na 2027.

    Hakan ne ma ya sa wasu ƴanƙasar ke amfani da lissafin sakamakon 2023 domin hasashen sakamakon 2027.

    To sai dai masana da masu sharhin siyasar ƙasar na cewa sakamakon 2023 ba zai zama madubin na 2027 ba.

    A watan Janairun 2027 ne dai za a yi zaɓen shugaban ƙasa a Najeriyar, ƙasar da ta fi kowa yawan al'umma a nahiyar Afirka.

  7. Mutum biyar sun mutu, takwas sun jikkata a hatsarin mota a Neja

    An tabbatar da mutuwar mutum biyar, yayin da wasu takwas suka jikkata sakamakon hatsarin mota da ya faru a ranar Lahadi a yankin Agaie da ke ƙaramar hukumar Agaie a jihar Neja.

    Jami’in hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) a yankin, Hussaini Guregi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

    Ya ce hatsarin ya shafi wata babbar mota ɗauke da kimanin fasinjoji 40 da kuma wata tankar mai.

    Motar na kan hanyarta ne daga Gusau a jihar Zamfara zuwa Shagamu a jihar Ogun lokacin da hatsarin ya afku.

    Guregi ya bayyana cewa mutane biyar sun mutu nan take, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Kwamishinan Agaie domin samun kulawa.

  8. Gwamnatin Najeriya za ta ci gaba da aikin kwaso ’yan Najeriya daga Afirka ta Kudu

    Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kwaso ’yan ƙasar daga Afirka ta Kudu, inda ake samun fargabar hare-haren ƙyamar baƙi dab da zanga-zangar da ake shirin yi a ranar 30 ga Yuni.

    An ce wani jirgin Air Peace ya tashi daga Najeriya a ranar Litinin, tare da shirin kwaso wasu daga cikin ’yan ƙasar zuwa Legas a safiyar Talata.

    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya ce wannan mataki na daga cikin shirin gwamnati na ba da dama ga ’yan ƙasar da ke son dawowa gida cikin aminci.

    Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shirin kwashe ’yan Najeriya kafin fara zanga-zangar adawa da baƙi a Afirka ta Kudu.

    Rahotanni sun nuna cewa fiye da ’yan Najeriya 700 na maƙale har yanzu a Afirka ta Kudu, kwanaki kaɗan kafin wa’adin da wasu ƙungiyoyin masu ƙyamar baƙi suka bayar ya cika.

    An kuma ce jinkirin fitar da kuɗin aikin kwaso ƴan ƙasar ya janyo tsaiko, lamarin da ya bar mutane da dama cikin barazana yayin da damuwar kai musu hare-hare ke ƙaruwa.

    Duk da haka, gwamnatin ta shawarci ’yan Najeriya da za su ci gaba da zama a Afirka ta Kudu su kasance cikin taka-tsantsan, su guji wuraren da ake zanga-zanga, tare da riƙa sadarwa da ofishin jakadancin Najeriya domin samun bayanai.

  9. Iran ta ƙara ƙaimi wajen yin kutse ta intanet tun bayan fara yaƙi - Isra'ila

    Babban jami’in tsaron intanet na Isra’ila ya ce Iran ta ƙara ƙaimi wajen yin kutse ta intanet tun bayan fara yaƙi tsakanin ƙasashen biyu.

    Yossi Karadi ya bayyana cewa an samu ƙaruwa a kutsen intanet daga Iran a cikin watannin baya-bayan nan.

    A wata hira da ya yi da jaridar Die Welt ta Jamus, Karadi ya ce a watan Yunin 2025, lokacin da Isra’ila ke gudanar da hare-haren soji kan Iran, sun gano kusan kutse ta intanet daga Iran 1,600.

    Amma a cikin makonni huɗu na baya-bayan nan na Yunin 2026, adadin ya ƙaru zuwa kusan 4,800.

    Ya ƙara da cewa masu yin kusten daga Iran ƙwararru ne sosai inda ya kuma ce dole ne a ɗauki lamarin da muhimmanci.

    Karadi ya kuma ce kutsen da Iran take yi ta intanet ɗin na harin muhimman cibiyoyin ƙasa, da ƙananan da matsakaitan kamfanoni kamar na lauyoyi da masu binciken kuɗi, da kuma jama’a baki ɗaya.

  10. Hare-haren saman Pakistan a Afghanistan sun hallaka mutane da dama

    Wani kakakin gwamnatin Taliban ya ce hare-haren sama da Pakistan ta kai kan yankuna a Afghanistan sun yi sanadiyyar kashe da jikkata fararen hula da dama, ciki har da mata da yara, a lardunan Paktika, Paktia da Kunar.

    Zabihullah Mujahid ya bayyana matakin na Pakistan a matsayin hari na “ban tsoro da ta’addanci,” yana mai cewa abin da ya faru ya saɓawa dokokin kasa da kasa ne.

    A wasu hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta, an ga yara da fararen hula da suka jikkata sakamakon hare-haren.

    Sai dai a nata ɓangaren, Pakistan ta ce ta kai harin ne kan wuraren da ke karkashin mayaƙan Tehreek-e-Taliban Pakistan (TTP) da Jamaat-ul-Ahrar, inda ta ce ta kashe aƙalla mayaƙa 25.

    Jami’an Taliban sun ce aƙalla mutane 38 ne suka rasa rayukansu a hare-haren na daren jiya, inda mataimakin kakakin gwamnatin ya ƙara da cewa mutum 30 daga cikinsu sun mutu ne a kauyen Mandokhel da ke gundumar Samkani a lardin Paktia kadai.

  11. 'Iran da Amurka sun amince su rage tashin hankali da ci gaba da tattaunawa'

    Wani jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa Iran da Amurka sun amince su dakatar da kai wa juna hare-hare tare da ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar zaman lafiya.

    A cewarsa, za a ci gaba da tattaunawa kan dukkan fannoni na yarjejeniyar, yayin da ɓangarorin biyu za su ƙaurace wa ƙara tsananta rikici a halin yanzu, tare da bai wa jiragen ruwa damar zirga-zirga cikin ‘yanci.

    Duk da wannan bayani, har yanzu Iran ba ta tabbatar da rahoton ba.

    A ‘yan kwanakin nan dai, rikici ya ƙara tsananta sakamakon taƙaddama kan tafiyar da mashigar Hormuz, tare da kai wa juna hare-hare tsakanin Iran da Amurka, lamarin da ya ƙara yawan fargabar rushewar tsagaita wutar da ake ƙoƙarin cimmawa.

    Jami’in na Amurka, wanda ya nemi a sakaya sunansa, bai bayyana lokacin da kuma wurin da za a ci gaba da tattaunawar ba, sai dai wasu majiyoyi sun ce ana sa ran ɓangarorin biyu za su sake haɗuwa a Doha, babban birnin Qatar, domin ci gaba da tattaunawa, yayin da kowanne ɓangare ke zargin ɗayan da karya yarjejeniyar da aka cimma a baya-bayan nan.

  12. Za mu ɗauki tsauraran matakai kan duk wanda ya karya yarjejeniya - Iran

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa za ta ɗauki tsauraran matakai kan duk wani ɓangare da ya karya yarjejeniyar da aka ƙulla, yana mai cewa irin wannan mataki na iya kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron yankin.

    Araqchi, wanda ya kai ziyara ƙasar Iraki, ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da Shugaban ƙasar, Nizar Amidi, inda ya ce karya wasu sashe-sashe na yarjejeniyar da Amurka da kuma Isra’ila suka yi musamman sashe na farko ya zama babban tarnaki ga ƙoƙarin dawo da kwanciyar hankali a yankin.

    Ya ƙara da cewa Iran na ƙoƙarin aiwatar da yarjejeniyar cikin gaskiya tare da bin ƙa’idar kowane ɓangare ya cika nauyin da ya rataya a kansa.

    Sai dai ya jaddada cewa Iran ba za ta lamunci duk wani saba yarjejeniyar ba, yana mai nanata cewa za su ɗauki matakan da suka dace domin kare muradun ƙasarsu da kuma tabbatar da dorewar zaman lafiya a yankin.

    Haka kuma, ya yi kira ga sauran ɓangarorin da ke cikin yarjejeniyar da su mutunta alƙawurran da suka ɗauka, yana mai cewa haɗin gwiwa da gaskiya su ne ginshikin warware rikice-rikice da ke addabar yankin Gabas ta Tsakiya.

  13. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.