Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne na kai tsaye da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Asabar 12/09/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Isiyaku Muhammed da Muslim Muhammad Yusuf

  1. An ji ƙarar fashewar abubuwa biyu a Iran

    Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayar da rahoton jin ƙarar fashewar abubuwa aƙalla biyu a tsibirin Qeshm.

    Kamfanin dillancin labarai na IRNA ya rawaito, yana ambaton majiyoyin yankin, cewa an ji waɗannan ƙarar ne daga teku.

    Zuwa yanzu, ba a fitar da ƙarin bayani kan abin da ya haddasa fashewar ko kuma ko akwai asarar rayuka ba.

    Ana sa ran samun ƙarin bayani kan wannan lamari.

  2. Celine Dione ta koma waƙa bayan fama da jinya

    Shahararriyar mawaƙiya ƴar ƙasar Kanada, Celine Dion, tana shirin kome da aka daɗe ana jira, inda za ta fara daga cikin wasanni guda 16 da za ta gabatar a birnin Paris cikin makonni masu zuwa.

    Wannan bikin raƙashewar ne na farko da za a ga Celion Dion bayan shekaru.

    Shekara huɗu da suka gabata, an gano cewa Celine Dion na fama da wata cutar jijiyoyi mai wuyar sha'ani mai suna Stiff Person Syndrome, wadda ta shafi muryarta ta waƙa. Wannan ya tilasta mata soke shirye-shirye da dama tare da jefa ta cikin ƙalubalen ci gaba da gabatar da waƙoƙi.

    Yayin da take barin otel ɗinta zuwa wurin taron waƙar, ta fito ta gaishe da magoya bayanta, inda ɗaruruwan magoya baya ne suka yi dafifi a kusa da otel ɗin tun bayan isowarta Faransa mako biyu da suka gabata.

    Har ila yau, ta yabawa wani matashin masoyinta da ya jira ta a wajen otel ɗin, wanda ya bayyana cewa burinsa tun yana ƙarami ya cika bayan Celine Dion ta amince da buƙatarsa ta rera waƙar haɗin gwiwa tare da shi.

  3. Yadda aka yi jana'izar sarki mafi ƙarancin shekaru

    An yi jana'izar Sarki Oyo Nyimba Kabamba Iguru Rukidi IV na Masarautar Tooro da ke yammacin ƙasar Uganda, wanda ya rasu a watan da ya gabata bayan fama da cutar daji. An binne shi a Makabartar Sarakunan Karambi da ke yammacin Uganda.

    Sarkin, wanda ya hau karagar mulki a ranar 12 ga Satumba, 1995 bayan rasuwar mahaifinsa, an binne shi ne a daidai ranar da aka naɗa shi sarki shekara 31 da suka gabata.

    An gudanar da jana'izarsa ne cikin sirri bisa al'adun masarautar Tooro, inda ƴan uwa da abokai na kusa kaɗai suka halarta.

    Dangane da tsofaffin dokokin binne sarakuna, ba a ba jama'a ko kafafen yaɗa labarai damar halartar lokutan ƙarshe na jana'izar ba, kuma ba a yarda da amfani da kyamarori a wajen kabarin ba.

    Da misalin ƙarfe 9:16 na safe agogon Uganda, akwatin gawarsa wanda aka lulluɓe da tutocin masarautar Tooro masu launin rawaya da shuɗi, ya bar Fadar Karuziika da ke Fort Portal a karo na ƙarshe domin zuwa wurin binne shi.

    Dubban masu jimami sun hallara a Cocin St. John’s Cathedral, cocin da kakansa, Omukama Rukidi III, ya gina kuma inda aka yi masa wankan tsarki tun yana yaro.

    Daga cikin mahalarta jana'izar akwai jami'an gwamnati, manyan baƙi, da wakilan masarautu da masarautun gargajiya daga ƙasashen Uganda, Kenya, Sudan ta Kudu, Najeriya da Eswatini.

    Cocin Uganda ta sanar da shirinta na dasa itatuwa miliyan 15 domin tunawa da marigayin, a matsayin girmamawa ga jajircewarsa na dogon lokaci wajen kare muhalli da yaƙi da lalacewar yanayi.

  4. Tinubu ya yi alhinin rasuwar Bamanga Tukur

    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma tsohon gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, Alhaji Bamanga Muhammad Tukur, wanda ya rasu yana da shekara 90 a duniya.

    A cikin saƙon ta'aziyyarsa, Shugaba Tinubu ya bayyana rasuwar Alhaji Bamanga Tukur, wanda ke riƙe da sarautar Tafidan Adamawa, a matsayin wani giɓi da aka rasa a tarihin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.

    Shugaban ya ce marigayin ya kasance fitaccen jagora wanda ya taka rawar gani a fannoni da dama da suka haɗa da aikin gwamnati, shugabanci, harkokin kasuwanci, siyasa da kuma bunƙasa kasuwancin Afirka.

    An haifi Alhaji Bamanga Tukur ne a ranar 15 ga Satumba, 1935. Ya yi fice a matakin ƙasa lokacin da ya kasance Babban Manajan Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) daga shekarar 1975 zuwa 1982, inda ya taimaka wajen zamanantar da ayyukan tashoshin jiragen ruwa da inganta harkokin sufurin teku a ƙasar.

    Shugaba Tinubu ya tuno da yadda Bamanga Tukur ya shiga siyasa a Jamhuriya ta Biyu, abin da ya kai ga zaɓensa a matsayin Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola a shekarar 1983. Jihar Gongola ta wancan lokaci ita ce ta rabu zuwa jihohin Adamawa da Taraba na yanzu.

    Bayan kammala aikinsa a siyasa, marigayin ya yi fice a harkokin kasuwanci inda ya jagoranci kamfanonin BHI Holdings da DADDO Group of Companies, waɗanda ke da hannun jari a fannoni kamar masana'antu, noma, sufuri da kasuwanci.

    Haka kuma ya taɓa zama Ministan Masana'antu na Tarayya a gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha daga shekarar 1993 zuwa 1995.

    A nahiyar Afirka kuwa, Bamanga Tukur ya kasance babban mai rajin farfaɗo da tattalin arzikin Afirka. Ya yi aiki a matsayin Shugaban African Business Roundtable da kuma shugaban NEPAD Business Group, inda ya riƙa fafutukar bunƙasa cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka, ƙarfafa zaman kansa a harkokin kasuwanci da ci gaba mai ɗorewa.

    Marigayin ya kuma kasance Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa daga Maris 2012 zuwa Janairu 2014. Shugaba Tinubu ya yaba da gudunmawar da ya bayar wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya ta hanyar tabbatar da ladabtarwa a cikin jam'iyya da kuma samar da haɗin kai.

    A cewar Shugaba Tinubu: "Alhaji Bamanga Tukur mutum ne mai ilimi, karamci da mutunci. Ya kasance mai kishin hidima ga al'umma da kuma mai cikakken yarda da ƙarfin da Najeriya ke da shi na samun ci gaba. Ƙasar nan za ta yi matuƙar kewar hikimarsa da shawarwarinsa na uba," kamar yadda Bayo Onanuga mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai.

    Shugaban Ƙasar ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan Tukur, masarautar Adamawa, gwamnatin da al'ummar Jihar Adamawa, da kuma dukkan al'ummar siyasa da kasuwanci a Najeriya da faɗin Afirka.

  5. Najeriya ta nuna ɓacin ranta da kisan ƴan ƙasarta biyu a Afrika ta Kudu

    Gwamnatin Najeriya ta ce tana cikin tsananin ɓacin rai kan kisan ƴan ƙasarta biyu - Bishop Taiwo Michael Fakunle da James Uchechukwu Nwankwo - a cikin mako guda a Johannesburg da Cape Town.

    A cewar Ma’aikatar Harkokin Waje, Bishop Fakunle ya mutu ne bayan da aka kai masa hari a gidansa, yayin da Nwankwo ya rasu sakamakon tsananin azabar bincike a hannun jami’an ƴan sandan Afrika ta Kudu suka yi masa.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar, Oluwafemi Adeniyi, ya fitar, Najeriya ta ce lamarin ya ƙara nuna ƙayamar baƙi da ake yi da kai musu hare‑hare musamman ƴan Afrika, a ƙasar — tana mai cewa abin da ya faru ya nuna gazawar hukumomin tsaro wajen kare rayukan baƙi.

    Sanarwar ta yi kira ga hukumomin Afrika ta Kudu da su gudanar da bincike mai zurfi kuma cikin gaggawa domin gano masu laifi da gurfanar da su.

    Najeriya ta ce ta gabatar da batun ƙyamar baƙi ga shugabannin ECOWAS da AU, kuma tana nazarin ƙarin matakan diflomasiyya domin kare ƴan ƙasarta a Afrika ta Kudun.

  6. PRP ta ce zarge-zargen da ake yi wa Sanata Shehu Buba ƙoƙarin ɓata suna ne

    Jam'iyyar adawa ta PRP a Najeriya, ta ce zarge-zargen da ake dangantawa da ɗan takararta na gwamnan Bauchi, Sanata Shehu Buba, na alaƙa da ayyukan ƴan bindiga yunƙuri ne na ɓata masa suna.

    Jam'iyyar ta ce ba ta so yin tsokaci kan zarge-zargen ba, saboda gudun ƙara ba su muhimmanci ko kuma taimaka wa abin da ta kira wata maƙarƙashiya.

    Sai dai PRP ta ce a yanzu dole ta yi magana akai saboda ta gamsu cewa wani akwai wani "mugun nufi" kan ɗantakarar.

    A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Ƙasa na jam'iyyar, Kwamared Muhammed Ishaq, ya fitar, PRP ta ce waɗannan zarge‑zargen "ƙage ne da aka ƙulla domin rage karɓuwar ɗan takararta", tana mai cewa masu yaɗa su na jin tsoron shaharar Sanata Buba da yiwuwar nasararsa a zaben gwamna.

    Jam'iyyar ta ce waɗanda ke da hujjar aikata wani laifi a kan Sanata Buba su gabatar da ita ga hukumomin da abin ya shafa domin su ɗauki matakin da doka ta tanada.

    PRP ta ce tana da yaƙini kan Sanata Shehu Buba, wanda ke wakiltar Bauchi a Majalisar Dattawa, kuma ta bayyana shi a matsayin ɗan ƙasa da ya taka rawar gani wajen ƙoƙarin daƙile matsalar tsaro da ta addabi ƙasar.

    Jam'iyyar ta ce tana ganin abokan hamayyar Sanata Shehu Buba da masu sukar sa na jin barazana ne saboda yaɗuwar farin jinin da yake da shi, shi ya sa suka koma yaɗa zarge-zargen da ta kira na ƙarya da ɓata suna.

    PRP ta tunatar da masu yaɗa irin labari cewa Sashe na 127(c) na Dokar Zaɓe ta 2026 ya haramta wallafa bayanan ƙarya da ke ɓata sunan ɗantakara, tare da tanadin tara ko zaman gidan yari ga masu aikata hakan.

  7. Tsohon shugaban PDP, Bamanga Tukur, ya rasu

    Tsohon shugaban Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na ƙasa, Bamanga Muhammad Tukur, ya rasu yana da shekara 91.

    Ɗaya daga cikin ƴaƴansa ne ya tabbatar wa BBC, inda ya ce mahaifin nasu ya rasu ne a gidansa da ke Abuja bayan shafe lokaci yana fama da rashin lafiya.

    Tukur, wanda ya taɓa zama gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, ya riƙe shugaban PDP na ƙasa daga shekarar 2012 zuwa 2014, a wani lokaci da jam’iyyar ta fuskanci ƙalubalen siyasa masu yawa.

    Ya kuma kasance fitaccen ɗan kasuwa kuma ɗan siyasa wanda ya riƙe muƙamai daban-daban na gwamnati a tsawon rayuwarsa ta siyasa a Najeriya.

  8. Wataƙila Iran na da hannu a harin bututun man Saudiyya

    Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ke ziyara a Jamhuriyar Ireland, ya shaida wa manema labarai cewa Iran ce "wataƙila" ke da alhakin harin baya-bayan nan da aka kai kan bututun mai na Saudiyya mai suna East-West Pipeline.

    "Ina ganin su ne. Wataƙila su ne," in ji shi a Dublin, yana mayar da martani ga tambayar wani ɗan jarida kan ko Iran ce ke da alhakin harin.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyya ta sanar sa'o'i kaɗan da suka gabata cewa jiragen sama marasa matuƙa da suka kai hari kan bututun man ƙasar sun taso ne daga Iraq.

    A jawabinsa, Donald Trump ya maimaita kalaman da ya yi kwanaki kaɗan da suka gabata.

    Ya ce yaƙin da Iran zai ƙare bayan zaɓukan tsakiyar wa'adin mulki da za a gudanar a Amurka a watan Nuwamba.

    Mista Trump ya kuma ce farashin mai zai ragu da zarar yaƙin ya ƙare.

  9. Shugaban Nijar ya yi sauye-sauye a shugabancin sojoji bayan yunƙurin juyin mulki

    Shugaban mulkin soja na Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya sauke babban hafsan sojin ƙasar, Manjo Janar Moussa Salaou Barmou, tare da maye gurbinsa da Birgediya Janar Mahaman Sani Kiaou, wanda shi ne babban hafsan rundunar sojojin ƙasa a halin yanzu.

    Hakan ya fito ne a wani rahoto da shafin labarai mai zaman kansa na Actu Niger ya wallafa a ranar 11 ga Satumba.

    Ma’aikatar Tsaro ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa, tana mai cewa matakin ya zo ne bisa wata dokar shugaban ƙasa.

    Rahoton ya ce: “Ba a bayar da wani bayani kan dalilin cire Barmou daga muƙaminsa ba, duk da cewa yana riƙe da wannan matsayi tun bayan karɓar mulki."

    Korarsa daga muƙamin na daga cikin manyan sauye-sauyen da aka yi a rundunar sojin Nijar tun bayan juyin mulkin da ya kai Tchiani kan karagar mulki, kamar yadda rahoton ya bayyana.

    Hakan ya kuma biyo bayan yunƙurin juyin mulkin da aka ruwaito ya faru a ranar 29 ga Agusta.

  10. Ƙarfin sojin Iran ya zarce tunanin maƙiya - IRGC

    A cewar rahotannin kafafen yaɗa labarai na Iran, manyan kwamandojin rundunar sojin ƙasar da na dakarun juyin-juya-halin (IRGC) sun gudanar da taro a yau.

    A taron, sun jaddada haɗin kai tsakanin sojojin ƙasa da IRGC, suna bayyana wannan haɗin kai a matsayin abu mai muhimmanci da zai ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen tunkarar abin da suka kira “makircin maƙiya.”

    A wannan taro, Ahmad Vahidi, kwamandan IRGC, ya ce: “Ƙarfin sojin rundunar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya zarce tunanin maƙiya. A wannan yaƙi, sun gani da idonsu cewa hasashensu na ƙarya game da ƙarfin sojojinmu ba daidai ba ne, kuma ainihin ƙarfin sojin Iran na ƙara bayyana a filin daga.”

    Shi ma Babban Kwamandan Sojojin Iran, Amir Hatami, ya ce a wannan yaƙi:

    “Duk wani ko da ƙaramin hari da aka kai wa Iran, sojojin ƙasa da na IRGC sun mayar da martani cikin haɗin kai, cikin sauri, cikin hikima, kuma da ƙarfi.”

    Babban kwamandan sojojin ya kuma bayyana cewa Iran ba za ta yi sulhu ko sassauci kan muradunta da buƙatun ƙasa ba.

  11. Ebola ta kashe sama da mutum 3,000 a Congo

    Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta tabbatar da cewa cutar Ebola da ta barke a kasar har ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum dubu uku, a yanzu ta bazu zuwa wani sabon yanki na kasar.

    Gwamnan lardin South Ubangi da ke arewa maso yammacin kasar ya ce gwaje-gwaje sun tabbatar da nau'in cutar Ebolar na Bundibugyo, wanda ke haddasa barkewar cutar da ake fama da ita a yanzu.

    Gwamnan ya bukaci mazauna yankin da su bi ka'idojin kariya da rigakafi, ciki har da yawaita wanke hannu da kuma kauce wa tarukan jama'a.

    Wakilin BBC ya ce fargabar da ake yi lalle ita ce za ta iya yaduwa zuwa iyaka cikin wasu kasashen. Lardin South Ubangi na iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Jamhuriyar Kongo-Brazzaville.

  12. Shugaban China da na Rasha da na Iran za su haɗu a taron BRICS a India

    Shugabannin kasashe 11 da suka hada da shugaban Rasha Vladimir Putin, da shugaban China Xi Jinping, da kuma shugaban Iran Masoud Pezeshkian za su hadu a birnin Delhi a wannan karshen makon domin halartar taron kungiyar BRICS.

    An kafa kungiyar ne a matsayin kishiya da za ta kalubalanci tasirin Amurka da kasashen Yammacin Turai a harkokin duniya.

    Sai dai yakin da ake fama da shi a Gabas ta Tsakiya ya fito da bambance-bambancen ra'ayi da ke tsakanin mambobin kungiyar.

    Daya daga cikin kasashen kungiyar, - Hadaddiyar Daular Larabawa, ta fuskanci hare-haren jirage marasa matuka da makamai masu linzami sau da dama daga wata kasar kungiyar, wato Iran.

    Ana sa ran tattaunawar za ta mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi samar da isasshen abinci da makamashi da karfafa hanyoyin samar da kayayyaki, da kasuwanci da fasaha, da kuma yin garambawul ga cibiyoyin duniya.

  13. Wani samfurin AI ya kauce wa matakan kariya tare da yin kutse

    Kamfanin kirkirarriyar basira - na OpenAI ya tabbatar da wani cewa wasu samfuransa, na AI din sun kauce wa wasu matakan kariya inda suka je suka yi kutse domin kai hari kan wani shafin intanet.

    OpenAI ya ce samfuransa da yake gwadawa sun kai hari kan wata manhaja mai suna RubyGems a watan Mayu, wata biyu kafin harin da ya yi fice kan shafin Hugging Face.

    Kamfanin na OpenAI ya ce a kutsen abin da samfuran nasa suka yi ba wani mai illa ba ne, sun dai tattaro bayanan da aka riga aka sani ne.

    Sai dai masu gudanar da RubyGems sun ce lamarin ya tilasta musu dakatar da bude sababbin shafuka na wani dan lokaci domin tabbatar da tsaro.

    Wannan sabon rahoto na kara nuna damuwa da fargabar da ake yi cewa fa, idan har ba a gaggauta daukar matakai ba to fa kirkirarriyar basira ta AI - ka iya kaiwa matakin da dan'Adam ba zai iya sarrafa ta ba.

  14. Saudiyya ta rufe muhimmin bututun mai bayan hari daga Iraq

    Rahotanni sun ce Saudiyya ta rufe wani muhimmin bututun mai da ake tura danyen mai zuwa gabar Tekun Bahar Maliya, ta cikinsa - wanda ke ba da damar kauce wa amfani da Mashigar ruwa ta Hormuz, bayan wani hari da jirage marasa matuka suka kai masa daga cikin Iraki.

    Wakilin BBC ya ce bututun na samar da kashi hudu ko biyar na man duniya a watannin nan.

    Gwamnatin Saudiyya ba ta bayyana wadanda ke da alhakin harin ba, amma ta ce irin wadannan hare-hare a baya suna da alaka da kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran.

    Lamarin na zuwa ne yayin da kungiyar Houthi da ke kawance da Iran ta ce ta kwace iko da daukacin gabar tekun Bahar Maliya ta Yemen, lamarin da ke kara karfafa matsayinta a wata muhimmiyar hanyar safarar kayayyaki ta ruwa.

    Kungiyar ta Houthi ta kuma ce za ta hana zirga-zirgar jiragen ruwa na Saudiyya a Mashigar Bab al-Mandab, abin da zai kara matsin lamba kan kasuwar man fetur ta duniya - inda samar da man zai kara raguwa.

  15. Farawa

    Masu bibiyarmu a wannan shafi na kai tsaye daga BBC Hausa muna muku barka da safiyar ta Juma'atu babbar rana.

    Za ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin kallon wasu hotuna da bidiyon hirarraki da muke wallafawa tare da yin tsokaci a kai.