Kotu ta ɗaure Saleh Mamman shekara 75 kan badaƙalar kuɗi

Asalin hoton, @EngrSMamman
Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yanke wa tsohon ministan lantarki a Najeriya shekara 75 a gidan yari kan almundahanar fiye da naira biliyan 33.
Alƙalin James Omotosho ya yanke hukuncin bayan ya samu Mamman da laifin aikata laifuka 12 da hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa ta'annati EFCC ta tuhume shi da su masu alaƙa da haɗa baki da almundahana.
EFCC ta tabbatar da hukuncin kotun a saƙon da ta wallafa a shafinta na Fesbuk.
Alƙali Omotosho ya ce ya kamata hukuncin zaman gidan yarin ya soma aiki daga ranar da aka kama mai laifin kasancewar an yanke hukuncin ne ba ya harabar kotun.
Kotun ta kuma umarci hukumomin tsaro da su kamo tsohon ministan a duk inda yake sannan kuma a miƙa wa gwamnati kuɗaɗe da dukiyoyin da aka ƙwato daga hannunsa.
Kotun ta kuma nemi Mamman da ya mayar da naira biliyan 22 na kuɗaɗen aikin samar da cibiyoyin lantarki na Mambila da Zungeru.
An gabatar da Mamman gaban babbar kotun tarayya a Abuja cikin Yulin 2024 bisa tuhume-tuhume 12 da ke da alaƙa da haɗin baki da almundahana. Ya musanta aikata zarge-zargen.
Sai dai a lokacin shari'ar, EFCC ta gabatar da shaidu 17 tare da miƙa wasu bayanai gaban kotun.
Hukuncin da aka yanke a yanzu ya kawo ƙarshen wata babbar shari'ar cin hanci da rashawa da ta fara tun bayan kama tare da tsare Mamman da EFCC ta yi a ranar 10 ga Mayun 2021.




