Ƙungiyar HRW ta zargi sojojin Rasha da kashe fararen hula 8 a Mali
Human Rights Watch ta zargi rundunar Africa Corps ta Rasha da kashe fararen hula a Mali
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch ta zargi rundunar sojin Rasha a Afirka ta Africa Corps da kai hare-hare ta sama sau biyu a yayin wani samamen soji da aka gudanar a tsakiyar ƙasar Mali a watan Yuni,
Ƙungiyar ta ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar fararen hula takwas, ciki har da yara uku.
Ƙungiyar mai hedikwata a birnin New York ta buƙaci gwamnatocin Mali da Rasha su gudanar da bincike kan lamarin.
Zarge-zargen na iya ƙara jawo damuwa game da faɗaɗar ayyukan rundunar sojin Rasha a yankin Sahel, inda ƙasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar suka juya baya ga ƙawayensu na Yamma tare da ƙara kusanci da Moscow domin neman taimako wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.
Sai dai jami'an gwamnatocin Bamako da Moscow na ci gaba da musanta zarge-zargen da ke cewa hare-haren nasu na haddasa mutuwar fararen hula.