An dakatar da ƙirga ƙuri'in zaɓen shugaban ƙasar Zambiya
Hukumar Zaɓen Zambiya ta dakatar da ƙirga ƙuri'un zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Alhamis, bayan rahotannin farmakar ma'aikatan zaɓe.
A wata sanarwa da shugaban hukumar, Mwangala Zaloumis, ya fitar, ya ce za a sake duba matakin cikin sa'o'i 24 masu zuwa.
Tun da farko, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar adawa, Brayen Mundubile, ya yi ikirarin lashe zaɓen.
Ya ce duk wani jinkirin sanar da sakamakon zaɓen na iya buɗe ƙofar maguɗi.
Shugaban ƙasar mai ci, Hakainde Hichilema, wanda ke neman wa'adi na biyu, ya yi kiran kwantar da hankali tare da kauce wa tashin hankali.