Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Nabeela Mukhtar Uba

  1. Iran na shirye-shiryen kai wa Amurka da ƙawayenta hari

    Wasu rahotanni na cewa ƙasar Iran na ƙarfafa ƙarfin tsaronta, da tattara masu mara mata baya, tare da yin barazanar mayar da kakkausan martani ga Amurka da ƙawayenta a yankin Tekun Fasha.

    Rahoton da Jaridar Wall Street Journal ta wallafa, na ya bayyana cewa Tehran na shirye-shiryen tunkarar yiwuwar kai hare-haren da Amurka za ta iya kaiwa bayan zaɓen tsakiyar wa’adi na ƙasar, kuma tana ɗaukar waɗannan matakai ne domin hana irin waɗannan hare-hare.

    Za a gudanar da zaɓukan tsakiyar wa’adin mulki na Amurka a makon farko na watan Nuwamba.

    Jami’an Iran sun yi gargaɗi, a cikin jawabai na fili da kuma tattaunawa ta sirri da hukumomin yankin, cewa idan Amurka ta ƙaddamar da sabbin hare-hare, Jamhuriyar Musulunci za ta ƙara rura wutar rikici a faɗin Gabas ta Tsakiya.

    Jaridar ta kuma ce hotunan tauraron ɗan adam sun nuna cewa Iran na ƙara tsaurara matakan kariya a wurare masu muhimmanci, ciki har da cibiyoyin nukiliya da yankunan kan iyaka.

    Rahoton ya ƙara da cewa wannan na iya zama yunƙurin karkatar da hankalin jama’a daga matsanancin halin tattalin arzikin da al’ummar ƙasar ke fuskanta, musamman bayan Amurka ta tsaurara takunkuminta kan Iran.

    Ko a ranar Lahadin ƙarshen mako, an jiyo sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa a Iran, Mohsen Rezaei, na cewa idan Amurka ta sake kai hari, sojojin Iran za su kai farmaki kan dukkan cibiyoyin adana bayanai ciki har da na ƙirkirarriyar basira ta AI da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

  2. Ma'aikatan jirgin ruwa 11 sun ɓata bayan harin da aka kai jirginsu a tekun Bulgaria

    Ma'aikatan jirgin ruwa 11 sun ɓata, bayan wani hari da aka kai da jirage marasa matuƙa kan jiragen dakon kaya a gaɓar tekun Bulgaria.

    Wakilin BBC ya ce bayan 11 da suka ɓata, akwai wasu da aka ceto.

    An kai hari kan jiragen ruwa biyu, wanda ɗaya daga ciki mallakar Ukraine ne.

    Wannan na daga cikin jerin hare-haren da ya zuwa yanzu suka shafi jiragen ruwa biyar a kusa da yankin ruwan Bulgaria.

    Ukraine na ƙara amfani da wannan ɓangare na Tekun Baharul aswad wajen jigilar kayayyaki ta ruwa.

    Firaministan Bulgaria, Rumen Radev, ya ce hare-haren za su amfani Rasha, kuma ya gayyaci jakadan Rasha domin neman bayani.

  3. Ƙawancen da Saudiyya ke jagoranta ta ce tana shirya wani 'aiki na musamman' a Yemen

    Mai magana da yawun kawancen da Saudiyya ke jagoranta ya ce an kakkaɓo tare da lalata makamai masu linzami guda uku a arewacin Riyadh.

    Ya kuma ce nan ba da jimawa ba za a fitar da gargaɗi ga mazauna wani yanki a babban birnin Yemen, Sana'a, domin su fice daga wurin kafin abin da ya kira "aiki na musamman", a yankin da mayakan Houthi ke iko da shi.

    Tun da farko, rahotanni sun ce Saudiyya ta fara bincike kan yadda na'urorin kare sararin samaniyarta ya gaza dakile hare-hare uku masu muni da mayaƙan Houthi masu goyon bayan Iran suka kai kan filin jirgin saman Riyadh.

  4. Gwamnatin Taliban ta dakatar da yaɗa shirye shiryen BBC a gidajen rediyon Afghanistan

    BBC ta ce gwamnatin Taliban a Afghanistan ta dakatar da watsa shirye-shiryen kafar yada labaran a gidajen rediyo a faɗin ƙasar.

    A wata sanarwa, BBC ta ce tana aiki tare da hukumomin Afghanistan domin warware matsalar.

    Ta ƙara da cewa mutane kusan miliyan 5.5 ne ke sauraron shirye-shiryenta a Afghanistan, adadin da ya kai fiye da kashi ɗaya cikin biyar na al'ummar ƙasar.

    BBC na gudanar da shirye-shiryenta ne a harsunan Turanci da Pashto da kuma Dari.

    Tun bayan da Taliban ta sake ƙarbar mulki a Afghanistan shekaru biyar da suka gabata, ƙungiyar ta taƙaita ayyukan kafafen yada labarai masu zaman kansu a ƙasar.

  5. Tinubu ya sanya gwamnonin hamayya biyu cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya saka gwamnonin hamayya biyu cikin kwamitin yaƙin neman zaɓensa na 2027.

    A ranar Laraba ne za a ƙaddamar da kwamitin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

    Gwamnonin hamayyar da suka samu shiga kwamitin yaƙin neman zaɓen su ne Ademola Adeleke na jam'iyyar Accord, sai kuma Charles Soludo na jam'iyyar APGA.

    Baya ga gwamnonin biyu, kwmaitin ya kuma saka Ministan Abuja Nyesom Wike na PDP cikin kwamitin, inda aka naɗa shi kodinetan Abuja da Rivers.

    Haka ma akwai tsohon gwamnan jihar Gombe kuma sanata a jami'yyar PDP, Ibrahim Danƙwambo, wanda aka bai wa muƙamin mai bayar da shawar a kwamitin.

    Wannan ba abu ne da aka saba gani ba a siyasar ƙasar.

    Da yake jawabi game da batun, Ministan Abuja Nyesom Wike ya ce matakin ya nuna wayewar Shugaban Tinubu na APC a siyasance.

    ''Hakan na nuna burin shugaban ƙasar na haɗa kan mutane, har daga wajen jam'iyyarsa ta APC'', in ji tsohon gwamnan na jihar Rivers.

  6. Hezbollah za ta bai wa iyalan da yaƙi ya lalata wa gidaje tallafin kuɗi

    Kungiyar Hezbollah ta sanar da cewa za ta bai wa iyalai a Lebanon da gidajensu na asali suka lalace ko kuma suka zama ba za a iya zama a cikinsu ba sakamakon yaƙin da ake yi da Isra'ila a halin yanzu, tallafin da ya kai dala dubu 14.

    Wannan ne karo na farko da ƙungiyar da Iran ke mara wa baya ta bayar da irin wannan tallafin kudi tun bayan da ta harba makamai masu linzami zuwa Isra'ila a watan Maris, lamarin da ya sa gwamnatin Isra'ila ta ƙaddamar da wani sabon farmaki mai girma a Lebanon.

    Matakin na zuwa ne duk da ƙarin matsin lamba da Amurka da kawayenta ke yi na ganin sun katse hanyoyin samun kudaɗen tallafi na Hezbollah, musamman daga Tehran.

  7. Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ta zarga da tilasta wa yara shiga ƙungiyoyin ƴanbindiga

    Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da take zargi da amfani da yara wajen yin yaƙi ƙarƙashin dokar hana ɗaukar yara aikin soji wato Child Soldiers Prevention Act.

    Ta yi gargaɗin cewa wannan mataki na iya kai ga Amurkar ta rage bai wa sojojin ƙasar horo, ko sayar mata da makamai, ko bayar da tallafin soji, ko kuma hadin gwiwar tsaro daga ranar 1 ga Oktoba, 2026, sai dai idan Shugaba Donald Trump ya bayar da sassauci.

    Wannan mataki ya biyo bayan rahoto kan safarar mutane na 2026 da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar, wanda ya zargi kungiyoyin Boko Haram da ISIS reshen Yammacin Afirka da ci gaba da ɗaukar yara aiki tare da amfani da su a rikice-rikice a Najeriya.

    Rahoton ya sanya Najeriya cikin jerin kasashe 14 da ake zargi da ɗauka ko amfani da yara sojoji, ciki har da Rasha da Iran da Sudan ta Kudu da Somaliya.

  8. Tsofaffin sojojin Najeriya na zanga zangar lumana na neman ƙarin kuɗin fansho

    Tsofaffin sojojin Najeriya sun toshe kofar shiga ofishin Hukumar Kula da Fanshon Sojoji da ke babban birnin ƙasar Abuja a ranar Talata, domin neman a biya musu buƙatunsu na sauya tsarin da aka amince da shi wajen biyansu kuɗaden fanshonsu.

    Tsofaffin sojojin sun yi zaman dirshen a kofar shiga ofishin, yayin da sojoji masu ɗauke da makamai suka tare kofar shiga harabar ofishin, kamar yadda jaridar PUNCH ta ruwaito.

    Wannan alamari na zuwa ne makonni bayan zanga zangar da wasu tsofaffin sojojin suka gudanar a Ma'aikatar Tsaro a watan Satumba, inda suka buƙaci a ƙara musu kuɗaden fansho bayan ƙarin albashin da aka yi wa sojojin da ke aiki.

    Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya yi alƙawarin cewa wadanda suka yi ritayar za su samu karin kudin fansho a watan Oktoba.

    Shugaban Kungiyar Tsofaffin Sojojin Najeriya, Laftanar Kanal Innocent Azubike, ya zargi hukumar da amfani da tsarin lissafa fansho wanda a cewarsa, bai yi dai dai da abin da ya kamata a rika biyansu ba.

  9. Jihohi 10 da suka fi fama da talauci a Najeriya

    Kimanin mutane miliyan 123 ne ke barazanar faɗawa cikin matsanancin talauci a Najeriya, kamar yadda wani rahoto na Bankin Duniya ya nuna a 2026.

    Rahotanni na baya-bayan nan da hukumar ƙididdiga ta ƙasar (NBS) ta fitar sun nuna cewa jihar Sokoto ce ta fi fama da talauci a Najeriya, inda aka ƙiyasta kusan kashi 90.5% na al'ummarta suna rayuwa cikin matsanancin talauci.

    Sai dai wani rahoton hukumar raya ƙasashe na Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ya wallafa, ya nuna cewa yawan mutanen da ke fama da talauci a yankuna daban-daban na Najeriya ya bambanta sosai kuma ba jihar Sokoto ke kan gaba ba.

  10. Nan da 2050 masu ciwon mantuwa za su ninka sau biyu - Bincike

    Wani sabon bincike da aka gudanar kan ciwon mantuwa (dementia) ya yi hasashen cewa, nan da shekarar 2050, adadin sabbin mutanen da za a gano suna ɗauke da cutar zai ninka har sau biyu, kuma buƙatar samar da kulawa za ta yi matukar ƙaruwa.

    Wannan bincike—wanda Cibiyar Kula da Lafiyar Kwakwalwa a Lokacin Tsufa ta Jami'ar New South Wales ta gudanar—ya yi nazari kan al'ummomin ƙasashe da yankuna 18.

    Binciken ya nuna cewa a duk faɗin duniya, an samu sabbin mutane kimanin miliyan 11 da rabi da suka kamu da cutar mantuwa a shekarar 2023 kuma nan da tsakiyar wannnan ƙarnin adadin zai haura sama da miliyan 24 da rabi.

    Marubutan binciken sun bayyana cewa ya kamata a ba da fifiko ga lafiyar ƙwaƙwalwar mata.

  11. Saudiyya ta ƙaddamar da bincike kan yadda ƴan Houthi suka samu nasarar kai mata hari

    Rahotanni sun bayyana cewa Saudiyya ta ƙaddamar da bincike domin gano yadda na'urorin kariyar sararin samaniyarta suka gaza daƙile makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da ƙungiyar Houthi ta harba daga Yemen, lamarin da ya yi sanadin munanan hare-hare uku a filin jirgin saman Riyadh.

    Kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) ya ce wasu jami'ai biyu daga yankin sun bayyana cewa binciken farko ya nuna mayaƙan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun fara harba jirage marasa matuƙa masu yawa ne domin kaucewa na'urorin kariyar sannan su kai hari filin jirgin saman.

    AP ya kara da cewa daya daga cikin jami'an ya bayyana cewa binciken yana kuma ƙokarin gano dalilin da ya sa na'urorin kariyar sararin samaniyar kasar basu bayar da gargaɗin tun da wuri kan harin ba.

  12. Jami'an shige da fice na Amurka sun kai samame gidan 'yar majalisa Ilhan Omar

    Jami'an shige da fice na Amurka sun gudanar da bincike a gidan 'yar majalisar dokokin Amurka daga jihar Minnesota, Ilhan Omar, a wani ɓangare na binciken aikta laifi da ake yi.

    Mai magana da yawun Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ya ce jami'an Hukumar Binciken Tsaron Cikin Gida (HSI) sun aiwatar da umurnin yin bincike ne da wata kotu ta amince da shi a wani gida da ke yankin Washington DC.

    Sai dai bai yi ƙarin bayani kan binciken ba.

    Haka kuma babu tabbacin ko Omar tana gida a lokacin da aka gudanar da binciken, saboda majalisar dokokin Amurka na hutu a halin yanzu.

    Omar, wadda 'yar jam'iyyar Democrat ce kuma mai yawan sukar Shugaba Donald Trump, ta wallafa a shafukanta na sada zumunta cewa matakin wani yunƙuri ne na "musgunawa abokan hamayya na siyasa da kuma amfani da jami'ian gwamnati a matsayin makamin siyasa."

    Da yake magana da manema labarai, Shugaba Trump ya ce ba shi da wata alaƙa da binciken da ma'aikatar shari'a ke yi wa Omar.''

  13. Jarumin shirin Breaking Bad, RJ Mitte ya rasu

    Fitaccen jarumin fina-finan Amurka RJ Mitte, wanda ya shahara saboda rawar da ya taka a shahararren shirin talabijin na Breaking Bad, ya rasu yana da shekara 34 a duniya.

    Wakilinsa ya shaidawa BBC "Cikin alhini da baƙin ciki ne muke sanar da rasuwar jarumi mai tarin masoya, mai ayyukan jin ƙai, kuma jajirtaccen mai fafutukar kare haƙƙin masu nakasa, RJ Mitte."

    Mitte ya rasu ne a Brownsville da ke jihar Texas ranar Litinin.

    Mai magana da yawunsa ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya kashe kansa ne.

    Jarumin, wanda ke fama da lalurar ƙwaƙwalwa da ke shafar gaɓoɓi wato cerebral palsy, ya yi amfani da abubuwan da ke faruwa a rayuwarsa wajen taka rawar Walter "Flynn" White Jr. a cikin shirin Breaking Bad wanda ya lashe lambobin yabo na Emmy.

    Jarumi Bryan Cranston, wanda ya taka rawar mahaifinsa a shirin, ya yi masa ta'aziyya a shafinsa na Instagram, yana cewa yana cikin matsanancin alhini bayan samun labarin rasuwar.

    Baya ga aikinsa na fim, Mitte ya kasance jakada na ƙungiyoyin United Cerebral Palsy da Shriners Children's, sannan ya kafa gidauniyar The Mitte domin tallafa wa ayyukan jin ƙai da shirye-shiryen ci gaban al'umma.

    A cewar wakilinsa, ya yi amfani da sunansa da tasirinsa wajen ƙalubalantar wariya da ƙasantarwa da ake yi wa masu nakasa.

  14. Gwamnatin Kaduna ta ce tana iya ƙoƙarinta na ceto magidanci da iyalinsa da aka sace

    Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana ƙoƙarin ganin an ceto wani magidanci da matarsa da jaririyarsu da ’yan bindiga suka sace a unguwar Millennium City.

    Bidiyon mutanen da aka sace, wanda ya nuna su cikin mawuyacin hali a hannun masu garkuwa da mutanen, ya jawo kakkausar suka daga ƴan Najeriya, ciki har da jagoran ’yan adawa, Atiku Abubakar, wanda ya yi kira da a gaggauta ceto su.

    Gwamnatin jihar Kaduna ta ce tana sane da halin da mutanen ke ciki, kuma tana yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da kuɓutar da su.

    Kwamishinan watsa labarai na jihar Ahmed Maiyaki, ya ce bisa umurnin gwamnan jihar suna ci gaba da tattaunawa da jami'an tsaro domin ceto iyalan da ma kara tabbatar da tsaron rayukan alummar yankin.

    Ya ce tun kafin ɓullan bidiyon suna sane da alamarin, kuma tuna a wannan lokaci suka soma ɗaukar matakai.

    Tun da farko rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta kama wasu da ake zargin suna da alaƙa da garkuwa da iyalin.

  15. Tattalin arziƙin duniya ya nuna juriya na ban mamaki - IMF

    Yayin da yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da kawo cikas ga samar da makamashi da sauran kayayyaki a duniya, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa tattalin arziƙin duniyar ya nuna juriya mai ban mamaki.

    A cikin sabon hasashensa, ya sauya matakin matsin da ya ce za a samu ta fuskar tattalin arziƙin manyan ƙasashe da dama—ciki har da Birtaniya—a farkon yaƙin Iran.

    Wakilin BBC ya ce yanzu ana hasashen cewa matakin ci gaban tattalin arziƙin Birtaniya zai kasance na biyu a bayan Amurka cikin manyan ƙasashe bakwai masu ƙarfin tattalin arziƙi a duniya a wannan shekarar.

    Hukumar da ke sa ido kan tattalin arziƙi ta ce akwai yiwuwar ƙasahsen duniya sun koyi yadda za su fuskanci manyan matsalolin da suka shafi tattalin arziƙin ƙasashensu.

  16. Za a ci gaba da rufe filin jirgin saman Riyadh saboda hare haren Houthi - Saudiyya

    Hukumomin ƙasar Saudiyya sun ce filin jirgin saman ƙasa da ƙasa da ke birnin Riyadh zai ci gaba da kasancewa a rufe har zuwa aƙalla ranar Asabar, sakamakon hare-haren da ƴan tawayen Houthi na Yemen ke ci gaba da kai wa kan birnin.

    Da yammacin jiya Litinin, ƙungiyar ta bayyana cewa ta kai hari kan filin jirgin saman, yayin da rundunar sojin Saudiyya ta ce ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harba zuwa birnin na Riyadh.

    Wakiliyar BBC ta ce A Yemen, mayakan Houthi sun tsaurara ƙawanyar da suka yi wa birnin Taiz – wanda ke ƙarkashin ikon gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da ita.

    Yaƙin da ke gudana a yankin yana haifar da damuwa game da tasirin da zai yi ga tattalin arzikin duniya.

  17. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da safiyar ranar Talata.

    Yau ma mun dawo kamar kullum da labarai da rahotanni da sharhi kan muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya.

    Da fatan za ku ci gaba da kasance da wannan shafi na kai tsaye na sashen Hausa na BBC. Ka da ku manta za ku iya leƙawa sauran shafukan namu na sada zumunta domin samun ƙarin labarai da rahotanni da ma bidiyo.

    Mun gode.