Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko hare-haren Houthi a Saudiyya za su shafi ayyukan Umarah?
Hare-haren da mayaƙan Houthi na Yemen ke ci gaba da kai wa wasu wurare a Saudiyya da yankin Tekun Maliya sun sake tayar da hankali a tsakanin musulman duniya, musamman waɗanda ke shirin tafiya ƙasar Saudiyya domin gudanar da ibadar Umarah a watanni masu zuwa.
A ƴankwanakin nan mayaƙan sun kai hare-hare wasu filayen jiragen sama a ƙasar, ciki har da Riyadh, babban birnin ƙasar, inda harin da aka kai ranar Juma'a ya kashe mutum uku da raunata fiye da 10.
Kodayake mahukuntan Saudiyya sun sha bayyana cewa suna ɗaukar matakan tsaro domin kare wuraren ibada da mahajjata, yawan hare-haren da ake kai wa muhimman cibiyoyin ƙasar ya sa wasu masu niyyar Umarah ke tambayar ko rikicin zai iya barazana ga zirga-zirgar masu ibada da kuma ayyukan da suka shafi tafiyarsu.
A shekarun baya, rikicin Yemen ya kai ga kai hare-hare da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan wasu sassan Saudiyya, lamarin da ya sa hukumomi ke ƙarfafa matakan tsaro a filayen jiragen sama da sauran muhimman wurare.
Sai dai har yanzu biranen Makka da Madina na ci gaba da karɓar miliyoyin masu ibadar Umarah daga sassa daban-daban na duniya.
Wannan yanayi ya haifar da muhawara kan ko hare-haren Houthi za su iya shafar shirye-shiryen tafiyar mas Umarah.
Mene ne maƙasudin rikicin Houthi da Saudiyya?
Muhammad Qaddam Sadiq Isah mai sharhi kan al'amuran gabas ta Tsakiya kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ya ce rikicin tsaknin mayaƙan Houthi da Saudiyya ya samo asali ne daga 2014 sakamakon ƙawance da Saudiyya ta ƙulla da gwamnatin Yemen.
Ya ce ƙungiyar Houthi ta shafe lokaci mai tsawo dana yaƙi da gwamnatin Yemen, sakamakon gwagwarmayar neman iko da ƙasar.
''Gabanin shekarar 2014 Houthi ta samu ƙulla alaƙa da ƙasar Iran, lamarin da ya san manufarta ta sauya daga fafutikar neman mulkin Yeman, zuwa wani tushe na matsain lamaba kan Saudiyya da ma wasu ƙasashe maƙwabta'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa Iran ta riƙa amfani da ita kamar yadda take amfani da sauran ƙungiyoyi a wasu ƙasashe, kamar Hezbollah da Hamas da sauransu.
Mai sharhi kan ala'muran na Gabas ta Tsakiya ya ci gaba da cewa a shekarar 2014, Saudiyya ta shugabanci wani ƙawance na ƙasashen Larabawa domin kawo ƙarshen juyin mulkin da Houthi suka yi wa wasu sassan Yemen, ciki har d Sana'a, babban birnin ƙasar.
''A wannan lokaci ƙawancen ya ci nasarar kawo ƙarshen juyin mulkin a wasu sassan Yemen da dama, to daga nan ne rikici da gaba ya ƙullu tsakanin saudiyya da ƙungiyar Houthi'', in ji shi.
Ko hare-haren Houthi za su shafi Umarah?
A baya-bayan nan Saudiyya ta yi iƙirarin cewa kungiyar Houthi ta kai hare-hare kan biranen Makka da Madina, sanan kuma a makon da ya gabata ta kai hari kan filin jirgin saman Riyadh, babban birnin ƙasar.
Wani abu da ke ƙara jefa fargaba ga masu ziyarar ziyarar ibadar Umarah a ƙasar.
Qaddam Sadiq ya ce kusancin da ke tsakanin Saudiyya da Yemen da kuma inda cibiyar Houthi take a arewacin Yemen, wanda ke kusa da kudancin Saudiyya.
Masanin ya ce ba abin mamaki ba ne idan aka yi la'akari da irin ƙarfin ƙungiyar.
''Yadda ƙungiyar ke harba manya-manyan makamai na zamani masu cin nisan zango ba abin mamaki ba ne idan an samu hare-haren a biranen Makka da Madina'', in ji shi.
Ita dai Houthi ta sha musanta cewa tana kai hare-hare da gangan kan wurare masu alfarma a ƙasar Saudiyya.
Qaddam ya ce idan rikicin ya ci gaba yana iya zama cikas ga ayyukan ibadar umara da ma aikin hajjin da ke tafe.
''Idan yaƙin ya rincaɓe, ta yadda zai shafi ayyukan shirin Ibadun, da hana amfani da filayen jiragen sama, da hana shigar baƙi, to zai iya zama cikas ga ayyukan ibadar, ta yadda zai zama Umara da aikin Hajji sai waɗanda suke ƙasar, kamar yadda aka gani a lokacin annobar Corona'',
Mece ce alaƙar rikicin da yaƙin Iran da Amurka?
Qaddam Sadiq ya ce ko shakka babu wannan rikici yana da alaƙa da yaƙin Iran da Amurka.
''Kasancewar Ƙungiyar Houthi yanzu kusan a iya cewa ita ce kawai ta rage da ƙarfinta cikin ƙungiyoyin da Iran ke mara wa baya a yankin Gabas Ta Tsakiya, bayan koma-baya da ƙungiyoyin Hezbollah da Hamas suka samu'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan aka yi la'akari da inda Yemen ɗin take, akwai wata muhimmiyar mashigar ruwa da ake kira Bab-a-Mandab, wadda take so mayaƙan Houthin su ƙwace iko da ita.
''Don haka wannan yaki a iya cewa ci gaba ne na yaƙin Iran da Amurka da ake yi'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ta yaya za a warware rikicin?
Qaddam Sadiq ya ce dukkan wasu dabaru na kawo ƙarshen yaƙin a tsawon shekaru, babu wanda ba a bi ba.
Ya ce abin da ke kawo kicas ga rikicin shi ne su mayaƙan Houthi ba sa so ƙasar Yemen ta zauna lafiya ta yadda za a iya shirya zaɓe.
''Saboda su suna da son mulki, to amma kuma su tsiraru ne a ƙasar, idan aka koma zaɓe babu yadda za a yi, su yi mulki, saboda ba shu fi kashi biyar cikin ɗari na al'ummar ƙasar ba'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa su sun fi son su yi amfani da ƙarfi wajen ci gaba da riƙe mulki.
"Saboda haka ko ma wane mataki ne zai kawo ƙarshen wannan yaƙi ba zai zama cikin sauƙi ba'', in ji Muhammad Qaddam Sadiq Isah.