OPEC ta amince da ƙara haƙar gangar mai 188,000 a kullum

Asalin hoton, Getty Images
Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar OPEC+, ciki har da Saudiyya da Rasha, sun amince da ƙara yawan haƙar mai da ganga 188,000 a kullum daga watan Satumba, sakamakon matsalolin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ya haifar a kasuwar mai.
Matakin dai bai zo da mamaki ba, domin masana da dama sun riga sun yi hasashen cewa ƙungiyar za ta ƙara yawan haƙar mai domin biyan buƙatun kasuwa da kuma daidaita farashin mai.
Sai dai takunkumin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz sakamakon yaƙin ya kawo cikas ga ƙoƙarin ƙasashen yankin Tekun Fasha na ƙara yawan fitar da man fetur zuwa kasuwannin duniya.
Har yanzu ba a san lokacin da ƙasashen OPEC+ za su iya aiwatar da wannan ƙarin haƙar mai ba.
Yayin da ƙasashe irin su Iraq ke son ƙara samar da mai sosai, Rasha na fuskantar matsaloli sakamakon hare-haren jirage marasa matuƙa na Ukraine kan cibiyoyinta na man fetur, lamarin da ke takaita yawan haƙarta.































